Harkar noma: Najeriya za ta fitar da kayan abinci kasar waje

Harkar noma: Najeriya za ta fitar da kayan abinci kasar waje

– Yau Najeriya ta fara fitar da doya zuwa Kasar China

– Duk Duniya babu inda ya kai Najeriya noman rogo da doya

– Gwamnatin Shugaba Buhari ta dage wajen harkar noma

Hakika Shugaba Muhammadu Buhari ya dage wajen ganin an koma noma a kasar nan. Yanzu haka Kasar Najeriya za ta fara fitar da doya a yau dinnan da mu ke magana. Tuni kasashen China da sauran su suka nemi a kawo masu doya daga kasar nan.

Harkar noma: Najeriya za ta fitar da kayan abinci kasar waje
Najeriya za ta fitar da doya kasar waje

Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta dage wajen harkar a kasar nan wanda yanzu har ta kai yau za a fara fita da doya zuwa kasar waje. Ministan gona na kasar Cif Audu Ogbeh ya tabbatar da wannan kamar yadda mu ka samu labari.

KU KARANTA: Tsohon Gwaman Danbaba Suntai ya cika

Harkar noma: Najeriya za ta fitar da kayan abinci kasar waje
Najeriya ta fara fitar da abinci zuwa Kasar China

Kasar China watau Sin dai tayi odar wannan kaya wanda zai ba Najeriya damar samun kudin kasar waje. Duk Duniya babu inda ta kai Najeriya noman rogo da doya musamman ta bangaren Arewa maso tsakiya na kasar.

A bara an noma sama da ton miliyan biyu na shinkafa a Najeriya. Yanzu dai abin da Najeriya ta ke fitarwa ya fi karfin abin da ake shigo da shi wanda shi ne manufar Gwamnatin Shugaba Buhari.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Dabarar cefana cikin sauki [Bidiyo]

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng