'Tinubu ba Jonathan ba ne,' APC na Ganin za Ta Dawo Mulkin Najeriya a 2027
- Jam'iyyar APC ta ce Shugaba Bola Tinubu ba zai bari ya faɗi a zaben 2027 ba, kamar yadda ya faru da Goodluck Jonathan a 2015
- Daraktan yada labarai na APC, Bala Ibrahim ne ya bayyana haka a matsayin martani ga ƙaruwar rashin tsaro a sassan Najeriya
- Ya bayyana cewa jam'iyyarsa ta APC ta kayar da Jonathan zaɓe, saboda haka babu dalilin da zai sa ta kayar da kanta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Jam’iyya mai mulki ta APC ta bayyana cewa Shugaban kasa, Bola Tinubu ba zai bari ya sha kaye a zaben shekarar 2027 ba.
Jam’iyyar ta ce Tinubu zai fi tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, wanda aka kayar da shi a 2015 sakamakon tabarbarewar tsaro a kasar.

Asali: Twitter
Arise News ta ruwaito cewa APC ta bayyana haka a martaninta kan ƙaruwar matsalar tsaro da ke ci gaba da ta’azzara a fadin ƙasar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanatoci daga jihohin Arewacin Najeriya 19 sun yi tir da karuwar matsalar tsaro a jihohin Filato da Binuwai dake salwantar da rayukan jama'a.
Jam'iyyar APC ta yi martani kan rashin tsaro
This Day ta ruwaito cewa Daraktan yada labarai na APC, Bala Ibrahim, ya yi bayani kan jita-jitar cewa karuwar rashin tsaro a ƙasar na da nasaba da siyasa.
Akwai zarge-zarge da ke cewa ƙaruwar matsalar tsaron na da nasaba da yunƙurin ganin an kayar da Bola Tinubu a zaben 2027.
Sai dai Bala ya musanta hakan, inda ya ce:
“Idan wannan ne ra'ayin wasu masu sukar gwamnati, gwamnati ba za ta zauna tana kallo har a kama ta a farkon barci.
“Idan hakan ne ya jawo faduwar Jonathan, zan iya cewa Jonathan APC ce ta kayar da shi, kuma APC ba za ta rufe idonta har ta bai wa kanta kunya ba.”
APC: ‘Jami’an tsaro suna aikinsu’
Bala Ibrahim ya ce a baya, shugaban kasa ya umarci karamin ministan tsaro, Bello Matawalle, da ya koma yankin da matsalar 'yan bindiga ta fi tsanani, wato Arewa maso Yamma.

Asali: Facebook
Ya ce:
“Shi ya sa ya zabi mutum mai kwarewa a matsayin mai ba da shawara kan harkokin tsaro na kasa, Malam Nuhu Ribadu, wanda a halin yanzu yana zagaye wuraren da rikice-rikice ke yawaita, domin karfafa tsarin yaki da ta’addanci da kuma daga karfin gwiwar jami’an tsaro.”
Gwamnonin APC sun ziyarci Muhammadu Buhari
A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, tare wasu gwamnonin jam’iyyar APC sun ziyarci tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
Rahotanni sun tabbatar da cewa ziyarar ta gudana ne a gidan Buhari da ke jihar Kaduna, inda ya koma da zama bayan barin mahaifarsa Daura a Katsina.
Shugaban kungiyar gwamnonin APC, Sanata Hope Uzodinma na jihar Imo, shi ne ya jagoranci tawagar, suka gaishe da Buhari tare da mika masa sakon gaisuwa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng