An Yi Rashi a 2025: Manyan Malaman Addinin Musulunci da Suka Rasu a Bana
FCT, Abuja - A watanni huɗun farko na shekarar 2025, an yi rashin manyan malaman addinin musulunci a Najeriya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Da yawa daga cikin malaman addinin musuluncin da suka rasu, sun koma ga Mahaliccinsu ne sakamakon rashin lafiya.

Asali: Facebook
Malamai suna taka muhimmiyar rawa wajen koyarwa da sanar da jama'a abubuwan da addinin musulunci ya ƙunsa.
Rashinsu babbar asara ce a duniyar addinin musulunci domin suna barin babban gibi lokacin da suka rasu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Manyan malaman addinin musulunci da suka rasu
Ga jerin wasu daga cikin manyan malaman musuluncin da suka rasu a farkon shekarar 2025:
1. Sheikh Ishaq Yunus Almadany

Asali: Facebook
Allah ya yi wa Sheikh Ishaq Yunus Almadany rasuwa a ranar Alhamis, 6 ga watan Fabrairun 2025.
Shahararren malamin addinin musuluncin wanda ya ke a jihar Kaduna, ya rasu ne bayan ya ɗauki dogon lokaci yana fama da jinya.
Masallacin Sultan Bello da ke Kaduna ya tabbatar da rasuwar malamin addinin musuluncin a shafinsa na Facebook.
2. Sheikh Sa'idu Hassan Jingir

Asali: Facebook
A ranar Alhamis 6 ga watan Maris na shekarar 2025 aka tashi da labarin rasuwar Sheikh Sa'idu Hassan Jingir.
Wani ɗan agajin ƙungiyar Izala, Hamza Muhammad Sani ya sanar da labarin rasuwar babban malamin addinin musuluncin a shafinsa na Facebook.
Sheikh Sa'idu Hassan Jingir shi ne mataimakin shugaban ƙungiyar Izala na ƙasa na biyu kafin rasuwarsa.
Marigayin ya rasu ne bayan ya daɗe yana fama da jinya ta rashin lafiya wacce daga ƙarshe ta zama sanadiyyar komawarsa ga mahalaccinsa.
Sheikh Sa'idu Hassan Jingir ya kwashe shekaru ya na karantarwa da wa'azin addinin musulunci a sassa daban-daban na Najeriya.
3. Sheikh Abu Ishaq Al-Huwainy

Asali: Facebook
A ranar 17 ga watan Ramadan 1446AH aka samu labarin rasuwar babban malamin Hadisi a duniya, Sheikh Abu Ishaq Al-Huwainy.

Kara karanta wannan
Pascal Dozie: Abubuwa 11 da ya kamata ku sani game da attajirin da ya rasu a Najeriya
Ɗaya ɗaga cikin ƴaƴansa Haitham Al-Huwainy ya sanar da rasuwar mahaifinsa a shafinsa na Facebook.
Sheikh Abu Ishaq Al-Huwainy ya rasu ne bayan lafiyarsa ta ƙara taɓarɓarewa sakamakon jinyar da ya daɗe yana fama da ita.
Marigayin ya yi fice a fannin karantar da Hadisi da koyar da sunnonin Manzon Allah (S.A.W), kuma yana daga cikin manyan malaman Salafiyya a ƙasar Masar.
4. Sheikh Abdul'aziz Idris Dutsen Tanshi

Asali: Facebook
An yi rashi na ɗaya cikin manyan malaman Sunnah, Sheikh Abdul'aziz Idris Dutsen Tanshi.
Babban malamin addinin musuluncin ya rasu ne a daren ranar Alhamis, 3 ga watan Afirilun 2025 a jihar Bauchi.
Tun cikin dare shahararren malamin addinin musulunci, Umar Shehu Zaria, ya sanar da rasuwar Sheikh Abdul'aziz Idris Dutsen Tanshi a shafinsa na Facebook.
5. Malam Adamu Bajoga

Asali: Facebook
Fitaccen malamin addinin musulunci a jihar Gombe, Malam Adamu Bajoga ya rasu a ranar Lahadi, 5 ga watan Janairun 2025.
Tsohon ministan sadarwa na Najeriya, Farfesa Ali Isa Ibrahim Pantami ya tabbatar da rasuwarsa a wani saƙon ta'aziyya da ya sanya a shafinsa na Facebook.
An yi jana'izar Marigayin a garin Bajoga d ake jihar Gombe da safiyar ranar Litinin, 6 ga watan Janairun 2025.
6. Sheikh Yahya Harun Gombe
Allah ya yi wa fitaccen malamin addinin musulunci a jihar Gombe, Sheikh Yahya Harun Gombe rasuwa.
Marigayin ya rasu ne a safiyar ranar Litinin, 7 ga watan Afirilun 2025 sannan an yi jana'izarsa a kusa barikin ƴan sanda da ke birnin Gombe.
Farfesa Ali Isa Ibrahim Pantami wanda ya taɓa riƙe muƙamin ministan sadarwa ne ya sanya labarin rasuwar malamin a shafinsa na Facebook.
7. Sheikh Ibrahim Modibbo Daware
Babban malamin addinin musulunci a jihar Adamawa, Sheikh Ibrahim Modibbo Daware ya yi bankwana da duniya.
Marigayin wanda babban jagora ne a ɗarikat Tijjaniyya ya rasu ne a ranar Juma'a, 7 ga watan Fabrairun 2025.

Kara karanta wannan
'A tsaye aka karɓi ta'aziyya ta': Sheikh ya fadi dattakun ɗaliban Malam Dutsen Tanshi
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu na daga cikin waɗanda suka yi alhinin rasuwar fitaccen malamin wanda ya kwashe shekaru yana koyarwa.
Mahaifiyar malamin musulunci ta rasu
A wani labarin kuma, kun ji cewa Allah ya yi wa mahaifiyar fitaccen malamin addinin musulunci a Borno, Farfesa Muhammad Alhaji Abubakar rasuwa.
Marigayiyar ta yi bankwana da duniya ne a daren ranar Juma'a, 21 ga watan Maris na shekarar 2025.
A cikin wata sanarwa da babban malamin ya fitar, ya bayyana cewa mahaifiyarsa ta rasu ne bayan ta kwashe tsawon lokaci tana jinya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng