Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Maganar Batun Tsige Shugaban INEC, Mahmud Yakubu

Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Maganar Batun Tsige Shugaban INEC, Mahmud Yakubu

  • Fadar shugaban ƙasa ta musanta raɗe-raɗin da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa Bola Tinubu ya sauke Farfesa Mahmud Yakubu
  • A wata sanarwa da hadimin shugaban ƙasa, Daniel Bwala ya fitar yau Litinin, ya ce labarin ba gaskiya ba ne
  • Bwala ya bayyana cewa duk wani mataki da Shugaba Tinubu ya ɗauka zai fito ne daga hanyoyin da ya dace, ba ta hanyar jita-jita ba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

State House, Abuja - Hadimin shugaban ƙasa kan harkokin sadarwa, Daniel Bwala, ya karyata jita-jitar da ke yawo cewa Bola Tinubu ya sauke shugaban hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC).

Daniel Bwala ya tabbatar da cewa Shugaba Tinubu bai tsige Farfesa Mahmood Yakubu daga muƙaminsa na shugaban hukumar INEC ba.

Shugaban INEC, Mahmud Yakubu.
Fadar shugaban kasa ta musanta jita-jitar tsige shugaban INEC, Mahmud Yakubu Hoto: @INECNigeria
Asali: Twitter

Bwala ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ta shafinsa na dandalin X wanda aka fi sami da Twitter a yau Litinin, 7 ga watan Afrilu, 2025.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya tsige shugaban INEC kuma ya naɗa sabo? Gaskiya ta bayyana

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin sanarwar, Bwala ya bayyana cewa irin waɗannan rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta da wasu shafukan yanar gizo ba su da tushe, kuma ƙarya ce tsagwaronta.

Yadda aka fara jita-jitar tsige shugaban INEC

Tun farko dai wani saƙo da ya bazu cikin sauri a kafafen sada zumunta ya yi iƙirarin cewa shugaban ƙasa ya ya canza shugaban hukumar INEC na ƙasa.

Saƙon wanda mutane duka yaɗa a Facebook da shafin X, ya ce Tinubu ya maye gurbin Farfesa Mahmood Yakubu da wani Farfesa Bashiru Olamilekan.

Wannan lamari dai ya ja hankalin ƴan Najeriya musamman masu amfani da kafafen sada zumunta.

Me hukumar INEC ta ce kan tsige Yakubu?

Jim kaɗan bayan haka, mai magana da yawun shugaban INEC, Mista Rotimi Oyekanmi, ya shaida wa jaridar Vanguard cewa wannan jita-jita ƙarya ce.

Rotimi ya buƙaci ƴan Najeriya su yi watsi da wannan jita-jita, yana mai cewa: “Don Allah a yi watsi da ita. Ba gaskiya ba ce.”

Kara karanta wannan

An samu matsala a Gwamnatin Tinubu, Hakeem Baba Ahmed ya yi murabus daga muƙaminsa

A na ta ɓangaren, fadar shugaban kasa ta hannun Daniel Bwala ta ce labarin ba gaskiya ba ne.

Shugaban INEC.
Shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu na nan a kan muƙaminsa Hoto: INEC Nigeria
Asali: Twitter

Fadar shugaban ƙasa ta musanta rahoton

Bwala ya ce:

“Labarin da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya kori shugaban INEC ko kuma ya maye gurbinsa da wani, ba gaskiya ba ne, ya kamata a yi watsi da shi.
“Duk wani hukunci ko mataki daga shugaban ƙasa ana sanar da shi ne ta hanyoyin da suka dace, ba ta hanyar jita-jita da ƙage a kafafen sada zumunta ba.”

INEC ta jingine batun tsige Natasha

A wani rahoton, kun ji cewa hukumar INEC ta yi watsi da bukatar tsige sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan saboda rashin cika ƙa'ida.

Hukumar INEC ta bayyana cewa ƙorafin da wasu mazaɓar mutanen Kogi ta Tsakiya suka shigar na yi wa Sanata Natasha kiranye bai cika tanadin doka ba.

Wata sanarwa da INEC ta fitar, ta ce ta ɗauki wannan mataki ne bayan kammala tantance sa hannun dukkan waɗanda suka amince a yi wa sanatar kiranye.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng