Tirkashi: Matasa Sun Bijirewa Ƴan Sanda, Sun Mamaye Titunan Abuja da Wasu Jihohi

Tirkashi: Matasa Sun Bijirewa Ƴan Sanda, Sun Mamaye Titunan Abuja da Wasu Jihohi

  • Rahotanni sun nuna cewa masu zanga zanga sun mamaye titunan babban birnin tarayya Abuja da Legas duk da gargaɗin 'yan sanda
  • A birnin Fatakwal na Rivers, an ce 'yan sanda sun harba barkonon tsohuwa domin tarwatsa masu zanga-zanga a filin Isaac Boro Park
  • Kungiyar Take It Back na zanga-zanga ne domin nuna adawa da mulkin danniya, take hakki da amfani da dokar yanar gizo ba daidai ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Masu zanga-zanga sun fito kan tituna a Abuja, babban birnin Najeriya, da kuma birnin Legas, babbar cibiyar kasuwanci ta kasar.

Zanga-zangar da ƙungiyar 'Take It Back' ta shirya na ci gaba da gudana duk da gargaɗin da rundunar ‘yan sanda suka yi a kan gangamin.

Masu zanga-zanga sun mamaye titunan Abuja, Legas, da Rivers
Duk da umarnin 'yan sanda, masu zanga zanga sun mamaye titunan Abuja, Legas da Rivers.
Asali: Twitter

Masu zanga zanga sun mamaye Abuja, Legas

Kara karanta wannan

Matasa sun rikita Abuja da zanga zanga, an fara harba barkonon tsohuwa

A Abuja, an hango Omoyele Sowore da Deji Adeyanju suna jagorantar zanga-zangar, inda suka ki sauka daga titi duk da ƙoƙarin ‘yan sanda na tarwatsa su, inji rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A Legas kuwa, rahoto ya nuna cewa an ga wasu gungun masu zanga-zanga da kwalaye masu dauke da rubuce-rubuce daban daban a Ikeja, babban birnin jihar.

A jihar Rivers kuwa, masu zanga-zangar sun taru a Filin Isaac Boro da ke Fatakwal, amma ‘yan sanda sun harba musu barkonon tsohuwa, kamar yadda muka ruwaito.

Rundunar ‘yan sanda ta ce ba ta yarda da zanga-zangar ba, kasancewar an shirya ta a ranar da gwamnati ta ware don bikin 'Ranar ‘Yan Sanda ta Ƙasa'.

'Yan sanda sun gargadi masu zanga-zanga

A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi, ya fitar, ya ce zanga-zangar na da nufin bata sunan ‘yan sanda da kuma ƙasar baki ɗaya.

Kara karanta wannan

"Abin tausayi": Mutane sun yi magana, an ji yadda aka kashe bayin Allah sama da 50

Sanarwar ta ce:

“Rundunar ‘yan sanda ta karanta a cikin labarai cewa wata ƙungiya mai suna 'Take It Back' na shirin gudanar da zanga-zanga a jihohin ƙasar, musamman a Abuja, a ranar Litinin, 7 ga Afrilu, 2025 – ranar da gwamnati ta ware don bikin ranar ‘yan sanda ta kasa.”
“Ko da yake ‘yan sanda ba su da matsala da ‘yancin gangami kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada, amma akwai damuwa kan dalilin da ya sa aka zaɓi ranar da ake girmama gudunmawar ‘yan sanda ga tsaron ƙasa don gudanar da irin wannan zanga-zanga."

Dalilin matasa na gudanar da zanga-zanga

Sanarwar da rundunar ta wallafa a shafinta na X, ta bukaci masu niyyar shiga zanga-zangar da su nemi hanyar tattaunawa da hukumomi maimakon fitowa kan tituna.

Kungiyar 'Take It Back Movement' ta bayyana cewa ta kira zanga-zangar don nuna adawa da mulkin danniya na shugaban ƙasa Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

'A dawo mana da Fubara': Zanga zangar adawa da Tinubu ta barke a Rivers

Kungiyar ta kuma yi ikirarin cewa mulkin Tinubu na cike da take haƙƙin ɗan Adam da kuma amfani da dokar laifuffukan yanar gizo ta 'Cybercrime' ba bisa ka'ida ba.

Abuja: 'Yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zanga

A wani labarin, mun ruwaito cewa, jami'an rundunar 'yan sanda sun tarwatsa masu zanga zanga a babban birnin tarayya Abuja ta hanyar watsa masu barkonon tsohuwa.

An rahoto cewa ‘yan sanda sun yi kokarin tarwatsa masu zanga-zangar da borkonon tsohuwa, amma hakan bai hana matasan ci gaba da bayyana korafinsu ba.

Masu zanga zangar dai na korafi ne kan yadda Shugaba Bola Tinubu ke gudanar da mulkinsa da kuma yadda ake take dokar amfani da yanar gizo a kasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.