‘Yadda Aka Yi Jinyar Ɗan Bindiga, Aka ba Shi Kyautar N3m Kafin Sakinsa a Sokoto’
- Murtala Bello Asada ya sake tasowa da bayani kan yadda matsalar tsaro ke ƙara kamari a Arewa maso Yamma, yana kalubalantar jami'an tsaro
- Malamin ya ce yana da hujjoji da ke nuna yadda manyan 'yan bindiga ke yawo babu tsoro, inda ya bayyana sunayensu da maboyarsu
- Ya zargi wasu jami'an tsaro da bayanai kan 'yan ta'adda, yana neman a fitar da gaskiya kan inda makamansu da motocinsu suka fito
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Sokoto - Sheikh Murtala Bello Asada ya sake buɗe aiki kan yanayin matsalolin tsaro musamman a Arewa maso Yamma.
Shehin malamin ya kalubalanci hukumomi da jami'an tsaro su fito su ƙaryata zarge-zargen da yake yi kan wasu rikakkun yan bindiga.

Asali: Facebook
Malam ya tona asirin ta'addanci a Sokoto
Malamin ya fadi haka ne a cikin wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Juma'a 4 ga watan Afrilun 2025.

Kara karanta wannan
'Haka suka yi wa Albany': Dutsen Tanshi ya fadi abin da yake tsammani bayan ya mutu
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shehin malamin ya fadi inda wani shahararren dan ta'adda yake a Gabashin Sokoto da ke dauke da muggan makamai.
"Murtala Bello ya fadi abubuwa da yawa daga ciki akwai Kachallah Haru, Haru Dole yanzu haka yana Gabashin Sokoto da muggan makami da sama da mutum 200 a hannunsa.
"Murtala Bello ya kalubalanci jami'an tsaro cewa an kama Haru Dole na fadi inda aka kai shi FIB aka bincike shi na fadi an tura wani Bashar ya zo ya yi belinsa.
"Akwai shaidu fa, na kuma ce an kai shi asibiti mai zaman kansa aka yi jinyarsa sannan aka ba shi N3m ya yi tafiyarsa."
Sheikh Murtala Bello ya kalubalanci hukumomi da su tuhume shi kan zarge-zargen da yake yi inda ya ce babu wanda bai san yawan wadannan maganganu ba.
"Wannan ya kamata a kalubalanci Murtala Bello, akwai wani jami'in tsaro da bai jin maganganun da Murtala Bello ke fadi?

Kara karanta wannan
Hotuna: Yadda musulmi suka yi cikar ƙwari a wurin janazar Sheikh Idris Dutsen Tanshi
"Duk wanda za ka kai wa tsegumi ka ce kaza ya riga ka sani waye Murtala Bello, kuma dukan maganganun ko guda ban janye ba.
"Na ce akwai Cedi an siya masa gida a Gusau har mutanen gari suka kashe shi cewa ba za su yarda a siyawa ɗan ta'adda gida ba."

Asali: Original
Sheikh Murtala Asada ya kalubalanci jami'an tsaro
Sheikh Murtala Bello Asada ya kalubalanci jami'an tsaro da hukumomi kan zargin da ya yi game da siyawa ƴan ta'adda motoci da gidaje
Ya kalubalanci masu cewa an yi sulhu da su nuna inda aka yi kuma ina makaman ƴan ta'addan suke.
"Na ce an siyawa Bello Turji mota da Ado Aliero, abin da ya kamata ku kalubalanci Murtala Bello kenan a kai idan ba haka ba zan fitar da abubuwa.
"Na kuma ce an siyawa Halilu Sububu mota sabuwa, masallacin za shi na zuwa da ita? Sai a fada mana ina aka yi sulhu da su."

Kara karanta wannan
'Ka saurare mu': Malamin Musulunci ya gargadi Ɗan Bello, ya shawarci ƴan Najeriya
Yadda aka kai wa Sheikh Asada hari
Mun ba ku labarin cewa babban malamin Musulunci a Najeriya, Sheikh Musa Ayyuba Lukuwa ya yi martani bayan harin yan bindiga gidan Sheikh Murtala Bello Asada.
Sheikh Lukuwa ya jaddada bukatar al'umma su bi duk hanyar da ta dace ta doka domin mallakar bindiga saboda yanayin tsaro a yankin.
Shahararren malamin ya ce idan da ba don Sheikh Asada ya yi harbi da bindiga ba da yanzu wata maganar ake yi ba wannan ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng