Bayan Kai Hari Gidan Sheikh Murtala Asada, Malamin Musulunci Ya Shawarci Al'umma

Bayan Kai Hari Gidan Sheikh Murtala Asada, Malamin Musulunci Ya Shawarci Al'umma

  • Babban malamin Musulunci a Najeriya, Sheikh Musa Ayyuba Lukuwa ya yi martani bayan harin yan bindiga gidan Sheikh Murtala Bello Asada
  • Sheikh Lukuwa ya jaddada bukatar al'umma su bi duk hanyar da ta dace ta doka domin mallakar bindiga saboda yanayin tsaro a yankin
  • Shahararren malamin ya ce idan da ba don Sheikh Asada ya yi harbi da bindiga ba da yanzu wata maganar ake yi ba wannan ba
  • Wannan na zuwa ne bayan wasu miyagu sun kai hari gidan malamin addinin a daren ranar Talata 14 ga watan Janairun 2025

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Sokoto - Sheikh Musa Ayyuba Lukuwa ya yi magana bayan harin da wasu miyagu suka kai gidan Sheikh Murtala Bello Asada.

Sheikh Musa Ayuba Lukuwa ya nuna damuwa kan yadda maharan suka yi kokarin kai hari gidan malamin inda suka yi rashin nasara.

Kara karanta wannan

Izala ta yi martani kan zargin raba Sheikh bin Usman da masallacinsa a Kano

Sheikh Lukuwa ya magantu bayan hari gidan Murtala Asada
Sheikh Musa Lukuwa ya shawarci al'umma bayan harin yan bindiga gidan Malam Murtala Bello Asada. Hoto: Sheikh Murtala Bello Asada.
Asali: Facebook

Martanin Sheikh Lukuwa bayan hari kan Murtala Bello

Wannan na kunshe ne a cikin wani faifan bidiyo da shafin Abdullahin Gwandu TV ya wallafa a shafin Facebook a jiya Juma'a 17 ga watan Janairun 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin bidiyon, Sheikh Lukuwa ya yaba wa malamin kan jaruntar da ya nuna yayin da ya yi harbi maharan suka watse bayan kawo masa hari.

Sai dai ya sake jaddada maganar da ya yi a bayan kan ba al'umma musamman yan yankin shawara da su mallaki makami saboda kare kansu daga yan bindiga.

Yadda Murtala Bello ya fatattaki miyagu a gidansa

"Yanzu ka ji Malam Murtala ranar Talata da dare aka kai masa hari, aka ɗauki mutum guda aka tsallaka da shi saboda ya bude kofa wadanda ke da mota a waje su shigo."
"Kuma wadanda ke wajen suna dauke da bindigogi, Allah ya sa Malam yana da na'urar nadan bidiyo sai ya ji su."

Kara karanta wannan

Shugaba a Izala ya sha rubdugu yayin bayani kan bikin 'Qur'anic Festival'

"Da ya yi harbi daya, biyu sai daya ya tsallaka ya koma, su kuma wadanda ke cikin mota suka fisge ta suka koma."

- Sheikh Musa Lukuwa

Ta'addanci: Sheikh Lukuwa ya ba al'umma shawara

Malamin ya jaddada maganar da ya fada a baya cewa kowa ya nemi bindiga saboda kare kansa.

Ya ce babu wata dabara da ta rage dan Najeriya musamman da ke yankunan da babu tsaro ya mallaki makami.

"Shi ya sa tun farko akwai hudubar da na ce ku mallaki makamai ko? Akwai hanyoyin doka na rike bindiga."
"Yadda ku ka sani ku na bin hanyoyin doka na siyan gida ku gina to ku bi hanyoyin nan na doka domin mallakar bindiga."

- Sheikh Musa Lukuwa

Sheikh Asada ya kalubalanci Bello Turji, Matawalle

Kun ji cewa Sheikh Murtala Bello Asada ya sake kalubalantar Bello Turji a wani bidiyo inda ya tabbatar da zargin ana daukar nauyin ta'addanci.

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi ya jajanta da Malamin Musulunci, yayan gwamna suka kwanta dama

Malamin ya ce Turji a faifan bidiyo, ya tabbatar da hannun karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle wajen harkar ta'addanci.

Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan kisan rikakken dan ta'adda, Halilu Sabubu a Zamfara bayan addabar al'umma da ya yi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.