An Fara Gargadin Gwamnatin Tinubu kan Hana Shigo da Kayan Sola Najeriya
- Cibiyar Bunkasa Harkokin Masana’antu masu zaman kansu (CPPE) ta gargadi gwamnati kan shirin hana shigo da kayan sola
- Ta ce Najeriya ba ta da isasshiyar masana’antar kera na'urorin sola da za ta iya cike gibin bukatar da ke da ita a halin a yanzu
- CPPE ta bukaci gwamnati ta saukaka haraji da samar da tallafi maimakon takaita shigo da kayayyakin makamashi a Najeriya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Cibiyar Bunkasa Harkokin Masana’antu Masu Zaman Kansu (CPPE) ta bayyana damuwa kan shirin gwamnatin tarayya na dakatar da shigo da na’urorin sola zuwa Najeriya.
Cibiyar CPPE ta ce hakan na iya kara tsananta matsalar rashin wutar lantarki da kasar ke fama da ita.

Asali: Getty Images
Rahoton Arise News ya nuna cewa shugaban CPPE, Dr Muda Yusuf, ne ya bayyana hakan a cikin wata tattaunawa.

Kara karanta wannan
Wike ya fadi halin da yake ciki bayan cewa ya yanki jiki ya fadi, an tafi da shi Faransa
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dr Muda Yusuf ya ce Najeriya na fama da rashin wuta, kuma hana shigo da kayan sola a yanzu zai jefa miliyoyin ‘yan kasa cikin matsanancin hali.
Sanarwar martani ne ga jawabin Ministan Kimiyya da Fasaha, Uche Nnaji, wanda ya bayyana shirin hana shigo da sola don karfafa masana’antun cikin gida.
Najeriya ba ta shirya ba – CPPE
A cewar Dr Yusuf, Najeriya ba ta da isassun masana’antun da za su iya samar da sola da zai biya bukatar kasar.
Ya ce a halin yanzu Najeriya na fama da matsanancin karancin lantarki inda kowanne dan kasa ke amfani da kimanin 160 kWh kacal a shekara.
Ya ce:
“Takaita shigo da kayan sola zai kara tabarbarewar wutar lantarki a kasar nan, musamman ganin yadda ake da karancin hanyoyin samar da wuta."
Yusuf ya kara da cewa amfani da na’urorin sola yana kara karbuwa a tsakanin al’umma da kanana da matsakaitan masana’antu saboda hauhawar farashin man fetur da wutar lantarki.
Gargadi kan tashin farashin kayan sola
Yusuf ya bayyana cewa hana shigo da kayan sola zai kara tsadar kayayyakin da rage hanyar samun wuta, lamarin da zai maida damar mallakar sola ga masu hannu da shuni kacal.
Ya ce:
“Farashin kayan sola zai tashi sama, wanda hakan zai hana talakawa da masu kananan sana’o’i amfani da shi.”
A maimakon haka, Yusuf ya shawarci gwamnati da ta saukaka haraji da tallafi ga masu shigo da kayan sola da kuma masu masana’antu a fannin.

Asali: Getty Images
Dr Yusuf ya ce shirin hana shigo da kayan sola zai tayar da hankali a tsakanin masu saka jari, kungiyoyin farar hula, gidaje da hukumomin duniya da ke saka hannun jari a fannin makamashi.
NNPCL ya kara kudin litar fetur
A wani rahoton, kun ji cewa kamfanin man Najeriya na NNPCL ya kara kudin litar man fetur a wasu yankuna.
An samu karin kudin man fetur ne jim kadan bayan shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanar da sauke Mele Kyari daga NNPCL.
Rahotanni sun tabbatar da cewa farashin litar man fetur ya haura zuwa N950 a Abuja yayin da ya haura zuwa N930 a jihar Legas.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng