An Hukunta Tsohon Kwamishinan Ƴan Sandan Kano kan Sukar Matakin Tinubu a Rivers

An Hukunta Tsohon Kwamishinan Ƴan Sandan Kano kan Sukar Matakin Tinubu a Rivers

  • Sufeto Janar na ‘yan sanda, Kayode Egbetokun, ya sauya AIG Usaini Gumel daga Zone 7 Abuja zuwa sashen kula da lamuran al'umma
  • Ana zargin an yi hakan ne domin hukunta Gumel kan furucin da ya yi game da dokar ta-baci da shugaban kasa ya maka a jihar Rivers
  • Rahotanni sun ce AIG Gumel ya bayyana ra’ayinsa ne a tattaunawa ta sirri, amma wani daga cikin abokan aikinsa ya tona masa asiri
  • Hakan ya biyo bayan sanya dokar da Bola Tinubu ya yi Jihar Rivers a ranar 18 ga Maris 2025 inda ya dakatar da Gwamna Sim Fubara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Kayode Egbetokun, ya sauya wa tsohon kwamishinan yan sansa a Kano, AIG Usaini Gumel wurin aiki.

Kara karanta wannan

An bar kasa ba kowa: Shettima ya shilla kasar waje bayan Tinubu ya kwana a Faransa

Sufetan ƴan sandan ya dage AIG Gumel daga Zone 7 a Abuja zuwa bangaren kula da lamuran al'umma da bincike.

Sufetan ƴan sanda ya hukunta Gumel kan sukar Tinubu
Yadda aka ragewa tsohon kwamishinan yan sanda a Kano armashi kan sukar dokar ta-ɓaci a Rivers. Hoto: Nigeria Police Force.
Asali: Facebook

An canzawa AIG Gumel ofis a Abuja

Daily Nigerian ta ce an dauki matakin ne saboda furucin da ake zarginsa da yi kan dokar ta-baci a Jihar Rivers.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Legit Hausa ta ruwaito cewa a ranar 18 ga Maris, 2025 Shugaba Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-baci a Jihar Rivers da kuma dakatar da gwamna Sim Fubara.

Daga cikin wadanda abin ya shafa har da mataimakiyarsa da ‘yan majalisar dokoki na jihar na tsawon watanni shida.

Majiyoyi sun bayyana cewa tsohon kwamishinan yan sanda a Kano, Gumel ya fadi ra’ayinsa game da dokar ta-baci a cikin tattaunawa da wasu abokan aikinsa, amma daya daga cikinsu ya tona asirinsa ga IGP.

AIG Gumel, wanda ya kama aiki a Zone 7 Abuja a ranar 19 ga Fabrairun 2025 bai samu wata takardar bincike ko damar kare kansa kafin sauya shi ba.

Kara karanta wannan

A karon farko, gwamna Fubara ya fadi halin da ya shiga bayan dokar ta baci a Ribas

Majiyar ta ce:

“IGP ya dauki mataki cikin gaggawa, ana zargin AIG Gumel ya fadi hakan a ranar 29 ga Maris, 2025 kuma nan take Egbetokun ya umarci a sauya shi.”
An ragewa AIG Gumel matsayi kan sukar matakin Tinubu
IGP Kayode Egbetokun ya sauyawa tsohon kwamishinan yan sanda a Kano wurin aiki bayan sukar matakin dokar ta-ɓaci a Rivers. Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa.
Asali: Facebook

Zargin dalilin hukunta AIG Gumel a Abuja

Majiyoyi sun tabbatar cewa an sauya AIG Gumel da AIG Mobolaji Victor Olaiya a ranar 30 ga Maris 2025 bisa wata takarda mai lamba: TH.5361/FS/FHQ/ABJ/SUB.5/314.

Ana kallon wannan canjin a matsayin hukunci mai tsanani ga manyan jami’an da ba su cikin sahun IGP.

Ɓangaren Zone 7 na da alhakin kula da Babban Birnin Tarayya da Jihar Niger, kuma ana daukarsa wurin aiki mai alfanu, yayin da sashen 'Community Policing' ake ganin wuri ne na ukuba.

IGP ya yi watsi da ƴan sandan jihohi

Kun ji cewa Sufeto-Janar na ƴan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun ya yi fatali da shirin kirkirar yan sandan jihohi, ya ce har yanzu kasar ba ta shirya ba.

Kara karanta wannan

Hawan sallah: An taso Sanusi II da Abba Kabir a gaba kan bijirewa umarnin ƴan sanda

Egbetokun ya ce gwamnatocin jihohi ba su da kudin da za su samar da ‘yan sandan jihohinsu da za su dace da tsarin kasa.

IGP Egbetokun ya kuma yi ikirarin cewa wasu gwamnonin za su yi amfani da ‘yan sandan domin biyan bukatun siyasa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel