'Haka Suka Yi wa Albany': Dutsen Tanshi Ya Fadi Abin da Yake Tsammani bayan Ya Mutu

'Haka Suka Yi wa Albany': Dutsen Tanshi Ya Fadi Abin da Yake Tsammani bayan Ya Mutu

  • A wani tsohon bidiyo, marigayi Sheikh Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi ya koka kan halin da al'umma ke nunawa ga malamai tun suna raye
  • Malamin ya ce wasu malamai sun rika sukar Sheikh Muhammad Adam Albany Zaria lokacin yana raye, amma suka zo jikinsa bayan ya mutu
  • Ya bayyana cewa malaman sun ce Albany bai bar kowa ba har da Ahlus Sunnah, amma daga baya suka fara yaba shi bayan rasuwarsa
  • A bidiyon, marigayin ya ce shi ba ya tsammanin za su zo jikinsa ko bayan ya mutu, yana nuna takaicinsa kan irin halin mutane

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Bauchi - Marigayi Sheikh Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi ya yi magana kan halin al'umma tun yana raye a wani tsohon bidiyo da aka yaɗa.

Malamin ya koka kan yadda wasu daga cikin malamai da al'umma suka nuna ga Sheikh Adam Muhammad Albany Zaria lokacin da yake raye.

Kara karanta wannan

Bayan jana'izar Dr Idris, wani limami ya ja sallar Juma'a a masallacin Dutsen Tanshi

Dutsen Tanshi ya soki yadda aka mu'amalanci Albany a tsohon bidiyo
Marigayi Sheikh Idris Dutsen Tanshi ya koka kan halin mutane, malamai a wani bidiyo. Hoto: Dutsen Tanshi Majlis Bauchi, Karatuttukan Malaman Musulunci.
Asali: Facebook

Dutsen Tanshi ya magantu kan halin al'umma

Hakan na cikin wani faifan bidiyo da Abubakar Sadiq Kurbe ya wallafa a shafinsa na Facebook a yau Juma'a 4 ga watan Afrilun 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin faifan bidiyon, malamin na kokawa kan halin wasu malamai game da yadda suka mu'amalanci Sheikh Muhammad Adam Albany Zaria.

Marigayi Idris Dutsen Tanshi ya ce a lokacin da Albany ke raye sukarsa suka rika yi sai da ya mutu suka shiga jikinsa.

Ya ce ba irin sukar da ba su yi wa Albany ba da cewa tsarin koyarwarsa ba shi da kyau da cewa babu wanda ya bari ciki har da ahlus Sunnah gaba daya.

An gano tsohon bidiyo da marigayi Dutsen Tanshi ke koka yadda aka yi wa Albany
Marigayi Sheikh Idris Dutsen Tanshi ya koka yadda aka mu'amalanci Albany kafin rayuwarsa. Hoto: Dutsen Tanshi Majlis Bauchi.
Asali: Twitter

Tsammanin Dutsen Tanshi kan mutane da malamai

Marigayi Sheikh Dutsen Tanshi ya kara da cewa malaman sun koka kan halin Albany lokacin yana raye cewa har su ahlus Sunnah bai bari ba bare kuma sauran mutane.

A cikin tsohon bidiyon, marigayin ya ce:

Kara karanta wannan

"Mutane sun manta": Tinubu ya faɗi aikin da Sheikh Dutsen Tanshi ya yi wa Najeriya

"Ka ga abin suke yi mani dinnan? Wallahi haka suka yi wa Albany.
"Lokacin Albany yana raye cewa suke yi ai usulubinsa bai da kyau, shi bai bar kowa ba, muma ahlus Sunnah bai bar mu ba.
"Haka suka rika yi, ba su zo jikinsa ba sai da ya mutu, sai da ya mutu.

Sai dai a tsohon bidiyon, marigayin ya ce kwata-kwata bai yi tsammanin za su zo jikinsa ba ko da ya bar duniya.

A cewarsa:

"To ni kam ma ba na tsammani idan na mutu ma za su zo jiki na."

Atiku ya kaɗu da rasuwar Dutsen Tanshi

Kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya bayyana alhini bisa rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Idris AbdulAziz Dutsen Tanshi.

Atiku, wanda tsohon dan takarar shugaban kasa ne a PDP ya nanata muhimmancin Sheikh Dutsen Tanshi wajen da'awa da kokarin yada zaman lafiya a Najeriya.

Jigon PDP ya bayyana rasuwar malamin a matsayin babbar asara ba ga iyalansa kawai ba, har ma da sauran al'ummar Musulmi a Bauchi da ke Arewacin Najeriya da kuma kasa baki daya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng