Matashi Ya Mutu, 1 kuma Rai a Hannun Allah bayan Artabu kan Budurwa a Bikin Sallah
- Wani matashi ya rasa ransa yayin da daya ke kwance rai a hannun Allah bayan rikici kan wata budurwa yayin bikin sallah a Adamawa
- Rikicin ya barke ne tsakanin matasa biyu, Idrisu Nuhu mai shekara 18 da Ahmadu Lawali mai shekara 16, inda suka kai wa juna farmaki da adda
- Idrisu ya samu mummunan rauni a kansa, yayin da Ahmadu ya gamu da rauni a wuyansa, likita ya tabbatar da mutuwar Idrisu a asibiti
- 'Yan sanda sun kwace adduna biyu a wurin da rikicin ya faru, kuma sashen CID na bincike don gano cikakken abin da ya faru a rigimar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Yola, Adamawa - Abun al'ajabi ya faru a jihar Adamawa bayan artabu tsakanin matasa kan wata budurwa.
Yayin artabun, wani matashi ya mutu yayin da dayan ke kwance rai a hannun Allah bayan mummunan arangama.

Asali: Facebook
Gombe: Yara 2 sun mutu a cunkoson idi
Rahoton Zagazola Makama ya ce an yi fadan ne kan wata budurwa a bikin sallah a kauyen Tasha Dinya da ke karamar hukumar Fufore, Jihar Adamawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na zuwa ne bayan rahoton Legit Hausa cewa rundunar ‘yan sandan Gombe ta tabbatar da mutuwar yara biyu sakamakon turmutsutsu da ya auku a babban filin Sallar idi.
Lamarin ya faru ne da misalin karfe 10:45 na safe a ranar sallah yayin da jama’a suka yi kokarin fita cikin gaggawa, lamarin da ya janyo jikkatar mutum 22.
An garzaya da wadanda suka jikkata asibitoci daban-daban, yayin da Gwamna Inuwa Yahaya ya dauki nauyin jinyar dukkan wadanda suka samu raunuka.
Rundunar ‘yan sanda ta jajanta wa iyalan wadanda suka rasu tare da fatan samun sauki ga wadanda suka jikkata.

Asali: Facebook
Matashi ya mutu a fada kan budurwa
Wani majiyar sirri ya shaida cewa lamarin ya faru da misalin karfe 4:30 na asuba a ranar Laraba 2 ga Afrilun 2025.
An yi fadan ne tsakanin Idrisu Nuhu mai shekara 18 da Ahmadu Lawali mai shekara 16 a duniya.
Rundunar 'yan sanda ta ce matasan biyu masu kananan shekaru sun fafata da juna da adda.
Idrisu ya samu mummunan rauni a kansa, yayin da Ahmadu ya samu rauni mai tsanani a wuyansa.
Dan uwansu, Nuhu Alhaji Muazu, ya garzaya da su zuwa Asibitin Malabu, inda likita ya tabbatar da mutuwar Idrisu.
An tabbatar da cewa Ahmadu kuma na cikin mawuyacin hali inda yake karbar magani.
Majiyar ‘yan sanda ta ce ta kwace adduna biyu daga wurin da abin ya faru, sannan an mika lamarin ga sashen CID domin gudanar da cikakken bincike.
Adamawa: Ƴan bindiga sun sace fastoci 2
Mun ba ku labarin cewa wasu majiyoyi sun tabbatar da cewa mahara sun sace fastoci biyu, Rabaran Mathew David Dusami da Rabaran Abraham Samman.
Maharan sun sace Fasto Samman na Jalingo da Fasto Dusami na Yola a Gwaida Malam a Numan da ke jihar Adamawa.
'Yan bindigar sun kutsa gidan fastocin da safiyar Asabar 22 ga watan Fabrairun 2025 dauke da makamai, suka kwashe su.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng