Ana Zaman Makokin Galadiman Kano, Mummunar Gobara Ta Tashi a 'Gidan Ado Bayero'
- Wata gobara ta tashi a 'Gidan Ado Bayero' da ke Kofar Nasarawa, a Kano, yayin da ake cikin zaman makoki na rasuwar Galadiman Kano
- Gobarar ta tashi ne wajajen Sallar Azahar, inda ta fara cin ginin daga hawa na ƙarshe, lamarin da ya jefa jama’ar yankin cikin firgici
- Rahoto ya ce gobarar ta shafi wani sashen kimiyya a jami’ar NYU da ke kan ginin, yayin da 'yan kwana kwana suka kai dauki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - A yayin da ake zaman makoki na rasuwar Galadiman Kano, Abbas Sanusi Bayero, wata mummunar gobara ta tashi a 'Gidan Ado Bayero' na Kofar Nasarawa.
Mummunar gobarar ta tashi ne wajajen Sallahar Azahar, na ranar Alhamis, 3 ga watan Afrilu, lamarin da ya jefa mazauna yankin cikin tashin hankali.

Kara karanta wannan
Galadima: Aminu Ado na karbar ta'aziyya a fadarsa, sarakuna, 'yan siyasa na tururuwa

Asali: Twitter
Gobara ta tashi a 'Gidan Ado Bayero' Kano
Wani bidiyo da Isa Sadi ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya nuna yadda gobarar ke ci gadan-gadan a hawa na na karshe na dogon ginin gidan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Gidan Ado Bayero' a halin yanzu ana amfani da shi a matsayin matsugunnin daliban jami'ar North University (wanda aka santa da Jami'ar Yusuf Maitama Sule a baya.)
A hade da wannan bidiyo, Isa Sadi ya wallafa cewa:
"Gobara a Gidan Ado Bayero na Kofar Nassarawa yanzu haka.
"Don Allah a rarraba wannan sakon har masu kashe gobara su zo. Don yanzu haka muna wajen babu kowa a wajen."
Kalli bidiyon gobarar a nan kasa:
Kano: An ji barnar da gobarar ta yi
A wani ci gaba da aka samu, wani mazaunin Kano, Anas Saminu Ja'en, ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa 'yan kwana kwana sun yi wa Gidan Ado Bayero Tsinke.

Kara karanta wannan
'Ba zan yi sata ba': Ɗan majalisa ya cire tsoro a gaban ƴan mazabarsa bayan shan suka
Anas Ja'en, ya rubuta cewa:
"Al'ummar da ke kusa don Allah a kawo ɗauki, duk da cewa an sanar da ni, tuni jami'an hukumar kashe goba suka yi wa wurin tsinke domin shawo kan wutar, Allah ya kiyaye, Amin."
Gidan Rediyon Arewa da ke Kano, a rahoto cewa gobarar ta shafi sashin kimiyyar na'ura mai kwakwalwa wato ICT na jami'ar.
Hotunan da gidan rediyon ya wallafa sun nuna irin barnar da wutar ta yi, da kuma kokarin da hukumar kwana kwana ke yi na takaita lamarin.
Duba hotunan a kasa:
Martanin mutane kan gobarar Gidan Ado Bayero
Legit Hausa ta tattaro ra'ayoyin mutane game da wannan gobara da ta tashi a Gidan Ado Bayero:
Real Abdullahi Yau Zawaciki:
"Watau wannan wajen ya shahara wajan ci da wuta. Allah ya kiyaye na gaba."
Adamu Aliyu Shu'aibu: ·
"SubhanalLah! Allah ta'aLah ya kiyaye aukuwar haka a gaba, ya maida alheran da aka rasa na ilimi, takardu, da sauran abubuwa."

Kara karanta wannan
"An yi rashi," Shugaba Tinubu ya yi magana da Allah ya karɓi rayuwar Galadiman Kano
Nuraddeen Sa'eed Muhammad
"Allah ya mayar da alkhairi, Allah kuma ya kiyaye gaba."
Ali A Isah:
"Allah ya tsayar haka. To! Me ye musabbabin faruwan tashin watar?"
Aminu Danlami Muhammad:
"Ana yawan yin gobara anan gurin, ya kamata mahukunta su dauki matakin gyara wajan, Allah ya kiyaye gaba, amin."
Mutuwar Galadima: Abba ya soke gaisuwar Sallah
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Gwamnan Kano, Abba Yusuf ya soke gaisuwar Sallah a masarautar Rano da Karaye saboda rasuwar Galadiman Kano, Abbas Sanusi Bayero.
Gwamnatin Kano ta ce ta dauki wannan matakin ne domin ba al'umma damar halartar jana'izar marigayin da kuma fara zaman karbar gaisuwarsa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng