Kano: Sunayen mutane 8 da ke takarar neman kujerar shugaban jami'ar YUMSU

Kano: Sunayen mutane 8 da ke takarar neman kujerar shugaban jami'ar YUMSU

- An zabi sunayen mutane takwas daga cikin ma su neman kujerar shugaban jami'ar Yusuf Maitama Sule (YUMSU) da ke Kano

- Kwamitin tantance 'yan takara ya sanar da cewa za a tantance mutanen takwas a ranakun 29 da 30 ga watan Satumba

- Manyan Malaman Jami'a da ke kan matakin Farfesa daga jami'o'i daban-daban za su fuskanci kwamitin da zai zabi mutum daya daga cikinsu

Hukumar jami'ar Yusuf Maitama Sule (YUMSU) da ke jihar Kano ta sanar da cewa ta fitar da sunayen mutane 8 na karshe da za a tantance domin zaben sabon shugabar jami'ar daga cikinsu.

Kwamitin tantance 'yan takara ya sanar da cewa za a gana da mutanen daya bayan daya a ranakun 29 da 30 ga watan Satumba na shekarar 2020 a dakin taro na 'Council Chambers' da ke harabar jami'ar.

KARANTA WANNAN: Labarin ƙarya ne: Elrufai ya magantu kan karɓar sunaye daga masu zaɓen sarkin Zazzau

Kano: Sunayen mutane 8 da ke takarar neman kujerar shugaban jami'ar YUMSU
Kano: Sunayen mutane 8 da ke takarar neman kujerar shugaban jami'ar YUMSU - Freedom Radio
Asali: Twitter

MSU ta tabbatar da hakan a cikin wani jawabi da ta aikawa manema labarai inda da bayyana cewa an zabi mutanen takwas daga cikin sauran wadanda suka nuna sha'awar neman kujerar bayan tallata cewa kujerar ta zama ta mai rabo.

Mutanen takwas da aka fitar da sunayensu sun hada da; farfesa Abdullahi Shehu Ma'aji daga jami'ar kimiyya da fasaha (KUST) da ke Wudil, Farfesa Bako El-Yakub Jibril da Farfesa Sadiq Z. Abubakar daga jami'ar ABU Zaria.

KARANTA WANNAN: Gwamnatin Nigeria ta samu umurnin dakatar da yajin aikin NLC daga kotu

Sauran sun hada da Farfesa Lawan Alhassan Bichi daga BUK, Farfesa Mukhtar A. Kurawa; shugaban kwalejin kimiyya ta Kano, Farfesa Balarabe Jakada; shugaban makarantar 'Legal' ta Kano, da Farfesa Aliyu Musa na YUMSU.

"An samu jinkiri a harkar zaben sabon shugaba saboda annobar korona saboda wa'adin tsohon shugaban jami'ar ya kare tun ranar 17 ga watan Mayu," kamar yadda YUMSU ta sanar a cikin jawabin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel