'Ka Saurare Mu': Malamin Musulunci Ya Gargadi Ɗan Bello, Ya Shawarci Ƴan Najeriya
- Malam Alkali Abubakar Salihu Zaria ya gargadi matashi Ɗan Bello kan zargin da ya yi wa Sheikh Bala Lau inda ce dole za su dauki mataki
- Malamin ya bayyana haka a cikin bidiyo cewa lokaci ya yi da za a dakatar da masu cin mutuncin malamai a Najeriya, darika ko Izalah
- Ya kara da cewa suna ci gaba da bincike kan Ɗan Bello, bayan kammalawa, za su dauki mataki kan cin mutuncin da aka yi
- Malamin addinin ya shawarci jama'a su rika bincike kafin su yarda da kowanne labari, kamar yadda Alkur’ani ya umarta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kaduna - Malam Alkali Abubakar Zaria ya yi magana kan zargin Sheikh Bala Lau da Ɗan Bello ya yi.
Shehin malamin ya gargadi matashin kan zarge-zargen da ya yi, ya ce dole za su dauki mataki kan lamarin.

Asali: Facebook
Ɗan Bello: Matakin da malamai ke shirin dauka
Sheikh Abubakar Salihu ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo da shafin Karatuttukan Malaman Musulunci ya wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sheikh Abubakar Salihu Zaria ya lokaci ya yi da za su dauki mummunan mataki kan masu ci wa malamai mutunci a Najeriya.
A cikin bidiyon, malamin ya ce:
"Budaddiyar wasika zuwa ga masu cin mutuncin malamai a Najeriya.
"Lokacin dakatar wadannan mutane ya yi, babu shakka daga yanzu duk wanda ya kara cin mutuncin malamai ko a darika ko Izalah zai mun ci mutuncinsa.
"Babu wanda ya fi mu bakin magana, babu wanda ya fi mu iya tsara magana kuma babu wanda yake ganin ba zamu iya fadin abin da ya fada ba."

Asali: Facebook
Alkali ya gargadi Ɗan Bello kan kalamansa
Shahararren malamin ya ce suna ci gaba da bincike kan Ɗan Bello game da karairayi da ya yi wa Sheikh Bala Lau.
Malamin ya ce da za ran sun kammala bincike ya saurari matakin da za su dauka na gaba.
"Musamman wannan yaro Ɗan Bello muna nan mu na bincike a kanka, kan cin mutuncin da ka yi wa shugaba Sheikh Abdullahi Bala Lau.
"Idan mun gama ka saurari matakin da za mu dauka, masu cewa Ɗan Bello ya fi gaskiya su je su yi ta magana, za su yi bayani a gaban hukuma.
"Kur'ani ya ce ya ku wandada kuka yi imani idan fasiki da ya zo muku da labari ku yi bincike."
Har ila yau, malamin ya shawarci al'umma kan binciken duk wani labari da aka kawo domin kawar da kokwanto.
Sheikh Alkali Zaria ya magantu kan Muslim/Muslim
A baya, mun ba ku labarin cewa Malam Salihu Abubakar Zaria ya bayyana cewa ko kadan bai yi nadamar zaben Bola Tinubu a tsarin Musulmi da Musulmi ba.
Sheikh Salihu ya ce ko kadan ba tsarin Musulmi da Musulmi ba ne ya kawo damuwar da ake ciki inda ya ce daga Allah ne.
Hakan na zuwa ne yayin da yan Najeriya da dama ke kokawa kan mulkin Bola Tinubu da suke zargin malamai da jawo musu duba da halin da ake ciki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng