'Maza Sun Ƙare a Kano': An Shiga Jimami da Galadiman Kano, Abbas Sanusi Ya Rasu

'Maza Sun Ƙare a Kano': An Shiga Jimami da Galadiman Kano, Abbas Sanusi Ya Rasu

  • An shiga jimami a jihar Kano bayan rasuwar Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi, wanda ya cika yana da shekaru 92 a ranar Laraba
  • An shirya jana’izarsa a gidan Sarkin Kano a Kofar Kudu, da misalin karfe 10:00 na safiya, kamar yadda dan marigayin, Mahmoud Abbas, ya sanar
  • Al’ummar Kano sun bayyana alhinin su, inda suka ce rasuwarsa babban rashi ne, kasancewarsa jigo a masarautar Kano tun zamanin baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - An shiga tsananin jimami gami da alhini a jihar Kano yayin da aka sanar da rasuwar Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi.

A safiyar Laraba, 2 ga watan Afrilu, Legit Hausa ta rahoto cewa Allah ya karbi rayuwar Galadiman Kano, Abbas Sanusi, yana da shekaru 92 a duniya.

Allah ya yi wa Galadiman Kano, Abbas Sanusi rasuwa
An shiga tsananin jimami a Kano yayin da Galadiman Kano, Abbas Sanusi ya rasu. Hoto: Masarautar Kano
Asali: Facebook

An sanar da rasuwar Galadiman Kano

Kara karanta wannan

Mutuwar Galadiman Kano: Abba ya soke gaisuwar Sallah a masarautun Rano da Karaye

A sanarwar da Mahmoud Abbas (Sanusi), dan marigayin ya fitar a shafinsa na X, ya ce za a yi jana'izar Galadiman Kano da misalin karfe 10:00 na safiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mahmoud Abbas, wanda shi ne mataimaki na musamman ga gwamnan Kano kan harkokin masarautu, ya sanar da cewa:

"InnalilLahi wa'inna iLaihi raji'un.
"Allah (SWA) ya yi wa mahaifinmu Alhaji Abbas Sanusi (Galadiman Kano) rasuwa.
"Jana'iza karfe 10:00 na safiya, a gidan Sarkin Kano, Kofar Kudu. Allah Ubangiji ya gafarta masa Amin."

Kanawa sun yi alhinin rasuwar Galadiman Kano

Tun bayan fitar sanarwar rasuwar Alhaji Abbas Sanusi, al'ummar Kano da kewaye suka shiga alhinin rasuwar Galadiman Kano.

An ce, mutane sun girgiza da wannan mutuwa kasancewar Alhaji Abbas Sanusi ya dade a kan kujerar Galadiman Kano, tun lokacin mulkin dan uwansa, Sarki Muhammadu Sanusi I.

Ko kafin zamansa Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi ya taba rike mukamin sarkin dawakin tsakar gida, hakimin Ungogo a 1959, da Dan Iyan Kano a 1962.

Kara karanta wannan

Abubuwa 3 da ba ku sani ba game da marigayi Galadiman Kano

Hakazalika, mutuwar Alhaji Abbas Sanusi ta girgiza Kanawa, saboda shi ne mahaifin Abdullahi Abbas, shugaban jam'iyyar APC na jihar Kano.

Abin da Kanawa ke cewa da Galadima ya rasu

Kanawa sun yi alhinin rasuwar Galadiman Kano, Abbas Sanusi
Abin da Kanawa suka ce da Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi ya rasu. Hoto: Masarautar Kano
Asali: Facebook

Legit Hausa ta tattaro wasu daga cikin ra'ayoyin mutane da Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi ya rasu:

Abban Fati Mosquitor:

"Allah ya jikan shi, Allah ya shiryi Abdullahi Abbas alfarmar Annabi Muhammad (S.A.W)."

Mohammed Hafizu:

"Allahu Akbar, ubangiji Allah ya jikan Galadiman Kano, gaskiya mun yi babban rashi, don haka ina mika ta'aziya ta ga mutanen Kano bisa wannan rashi da muka yi. Ubangiji Allah ya jikansa da rahama, ya sa Aljannah ta zama makoma a gare shi."

Aliyu S K Yareema:

"Maza sun kare a Kano."

Najib Abdullahi Shamsu:

"Allah ya kyauta makwancin mai girma Galadiman Kano."

Musaddeeq M Abdullahi:

"Allah ya jikansa da rahama. Hakika an yi rashin dattijon arziki a masarautar Kano. Allah ya kyauta namu zuwan."

Kara karanta wannan

Sarki Sanusi II ya yi babban rashi, Galadiman Kano, Abbas Sanusi ya rasu

Imam Hakeem Ahmad:

"Ubangiji Allah ya gafarta masa ya sa aljannace makomarsa."

Musa Gambo Ibrahim:

"Ubangiji ya gafarta masa zunubansa."

Usman Bashir:

"Allah ya jikansa da rahma. Baban su Alhaji Abdullahi Abbas kenan da Baba Awaisu"

Mashkur Sani:

"Allahu Akbar, Abbas dan sarkin Kano, Abbas. Ubangiji ya ba ka fiddausi."

Muhammad Idris:

"Allah ya jikansa, ya kyautata makwancinsa, ya bashi Aljannah."

Zahrau Ali Bala:

"Allah ya sa bakin wahalarsa kenan, dattijon kirki an yi ibada."

Muhammad BetoBalle Aliyu:

"Allah ya jikan mai girma Galadiman Kano, Alh Abbas Sunusi Bayero.
"Sakon ta'aziya daga Muhammadu Aliyu Balle, shugaban kungiyar Mbinnden Janngen Adlam Pulaar daga jihar Sokoto.
"Allah Ubangiji ya jikansa, ya gafarta masa, Allah ya sa mutuwa hutu ce a gareshi."

Sarki Sanusi II ya yi sababbin nade-nade

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Muhammadu Sanusi II ya amince da nadin sarauta ga wasu gidaje da suka taba rike mukaman sarauta a baya.

Kara karanta wannan

Ana zargin matashi da kisa a tawagar Sanusi II, ƴan sanda sun gargadi al'ummar Kano

An zabi Abba Yusuf daga gidan Galadiman Kano a matsayin Dan Makwayon Kano, inda aka yi masa nadin a ranar 18 ga Oktoba, 2024.

Tun daga shekarar 1965 babu wani daga zuriyarsu da ya rike sarauta, sai bayan dawowar Muhammadu Sanusi II.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.