Dan uwan Sarki Sanusi ne ya zama shuganan jam'iyyar APC a jihar Kano

Dan uwan Sarki Sanusi ne ya zama shuganan jam'iyyar APC a jihar Kano

Rahotannin da muke samu daga majiyoyin mu sun tabbatar mana da cewa dan uwan Sarkin Kano, mai martaba Alhaji Sanusi Lamido Sanusi ne ya zama shugaban jam'iyya mai mulki ta All Progressives Congress, APC a jihar Kano.

Shi dai sabon shugaban jam'iyyar ta All Progressives Congress, APC Alhaji Abbas Sanusi da ne ga Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi wanda kafin yanzu kwamishinan ayyuka na musamman ne a jihar kuma na hannun damar Gwamnan jihar Dakta Abudullahi Umar Ganduje.

Dan uwan Sarki Sanusi ne ya zama shuganan jam'iyyar APC a jihar Kano
Dan uwan Sarki Sanusi ne ya zama shuganan jam'iyyar APC a jihar Kano

KU KARANTA: Daliban jami'a 2 a Najeriya sun kirkiro na'ura mai ban al'ajabi

Legit.ng ta samu cewa a zaben da aka gudanar a jiya, Sabon shugaban jam'iyyar ya samu nasarar lashe zaben ne da kuri'u 2,982 cikin masu zabe 3472 da ya kamata su jefa kuri'a.

A wani labarin kuma, Da alama dai zabukan shugabannin jam'iyyar All Progressives Congress, APC da ya gudana a mataki na mazabu, kananan hukumomi da kuma jahohin kasar nan na cigaba da kawo rarrabuwar kawuna a tsakanin 'ya'yan jam'iyyun.

Kamar dai a jahohi da dama, a jihar Taraba ba mafusanatan matasa sun farfasa tayoyin motar babbar ministan mata a gwamnatin shugaba Buhari kuma tsohuwar 'yar takarar kujerar Gwamnan jihar ta Taraba watau Sanata Ai'sha Alhassan.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel