Abin da 'Yan Najeriya ke Cewa bayan Tinubu Ya Cire Mele Kyari daga Shugabancin NNPCL
- Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi sauyin shugabanci a kamfanin mai na ƙasa (NNPCL) ranar Talata, 2 ga watan Maris 2025
- Mai girma Bola Tinubu ya sauya Mele Kyari daga shugabancin NNPCL tare da maye gurbinsa da Injiniya Bashir Bayo Ajulari
- Ƴan Najeriya sun bayyana mabanbantan ra'ayoyi kan wannan sauyin shugabancin da shugaba Bola Tinubu ya yi
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sauke Mele Kolo Kyari daga shugabancin kamfanin mai na ƙasa (NNPCL).
Shugaba Tinubu ya kuma sauya kwamitin gudanarwa na kamfanin NNPCL a cikin sauye-sauyen da ya ya amince da su.

Source: Twitter
Bola Tinubu ya yi sauye-sauye a NNPCL
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga ya fitar a shafinsa na Facebook.
Shugaba Bola Tinubu ya kuma maye gurbin Mele Kyari da Injiniya Bayo Ajulari a matsayin sabon shugaban kamfanin NNPCL.
Mai girma Tinubu ya kuma naɗa Ahmadu Musa Kida wanda ya fito daga jihar Borno a matsayin sabon shugaban kwamitin NNPCL.
Ƴan Najeriya sun yi martani kan sauke Mele Kyari
Ƴan Najeriya sun yi martani kan sauyin shugabancin da Shugaba Tinubu ya yi a kamfanin NNPCL.
Waɗanda suka yi magana kan sauyin shugabancin da aka samu a NNPCL sun bayyana mabambanta ra'ayoyi.
Ga wasu daga ciki a nan ƙasa:
Olaudah Equiano:
"Ta tabbata ana maida ƙasar nan ta Yarabawa. Muna taya ka murna shugaban ƙasa."
Kakanfo:
"Wani Bashir Ojulari daga Arewa kuma. Me yasa Shugaba Tinubu ke maida Najeriya ta zama ta Arewa?"
Oladipo E.I:
"Yaushe za a kama Mele Kyari kamar yadda aka kama Emefiele, wanda ake tsare da shi?"
Prosper Kalabar:
"Tuni dama ya kamata a kori Mele Kyari."

Kara karanta wannan
Tinubu ya fadi dalilin da ya sa ya ki daukar shawara, ya nada mai sukarsa minista
Nda Aaron:
"Mele Kyari ya na nan tun zamanin Buhari daga Arewa, don haka ba adalci ba ne sake naɗa wani ɗan Arewa a matsayin shugaban NNPCL. Ɗan Kudu ya dace a naɗa."
Akinnefisi Olamide:
"Wannan abu ne da ya kamata a yi tuntuni, amma dai Kyari ya yi ƙoƙari a mulkinsa wajen farfaɗo da matatun mai."
Haywhy Lenzo:
"Daga ƙarshe, Mele Kyari ya tafi da ƙananun uzurorin da ya daɗe yana badawa tsawon shekaru. Muna taya murna ga sababbin waɗanda aka naɗa."

Source: Facebook
Benjamin Usende:
"Mu na taya murna! Muƙamin da aka ba Arewa Ta Tsakiya ma Bayerabe aka ba daga jihar Kwara kenan. Me yasa ba a ba wasu ƙabilu don daidaita lamarin ba? Wannan ba daidai ba ne."
Mallam Na Bakin Kogi:
"Ya kasa shirya gasar Al-Qur’ani."
NNPCL ya kawo cikas a yarjejeniyarsa da Dangote
A wani labarin kuma, kun ji cewa kamfanin mai na ƙasa (NNPCL), ya ɗakatar da yarjejeniyar siyar da man fetur a Naira ga matatun cikin gida.
Kamfanin na NNPC ya dakatar da siyar da ɗanyen man fetur ga matatun cikin gida har da ta kamfanin Dangote.
Wannan matakin ana kallonsa a matsayin wani abin da zai iya sanyawa farashin man fetur ya yi tashin gwauron zabi a ƙasar nan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

