Bidiyo: Sarkin Kano, Sanusi II Ya Ture Umarnin 'Yan Sanda, Ya Yi Hawan Nasarawa
- Duk da hana bikin Sallah da ‘yan sanda suka yi saboda matsalolin tsaro, Sarki Muhammad Sanusi II ya gudanar da Hawan Nasarawa a Kano
- A bana, an sauya jerin gwanon Hawan Nasarawa daga hawa doki zuwa hawa motocin fada, inda sarki ya kai gaisuwa ga Gwamna Abba Yusuf
- Jama’a sun fito suna taya sarki murna, yayin da ra’ayoyin mutane suka bambanta kan yadda aka gudanar da Hawan Nasarawa duk da jan kunne
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Sarkin Kano na 16, Muhammad Sanusi II, ya gudanar da Hawan Nasarawa na shekara-shekara duk da hana bikin Sallah da ‘yan sanda suka yi saboda dalilan tsaro.
A al’ada, wannan biki yana kunshe da fitowar sarki tare da tawagarsa a kan doki cikin gagarumin jerin gwanon da ke tashi daga fadarsa zuwa gidan gwamnati domin gaishe da gwamna.

Kara karanta wannan
Hawan sallah: An taso Sanusi II da Abba Kabir a gaba kan bijirewa umarnin ƴan sanda

Asali: Facebook
Sarki Sanusi II ya fita Hawan Nasarawa a Kano
Wani bidiyo daga shafin Masarautar Kano na X, ya nuna lokacin da Sarki Sanusi II ke fitowa daga gida, yayin da ya kimtsa don Hawan Nasarawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A makale da bidiyon, an wallafa cewa:
"Hawan Nasarawa!
"Fitowar mai martaba Sarkin Kano Khalifa Dr. Muhammad Sanusi II, CON zuwa gidan gwamnatin jihar Kano don yiwa mai girma gwamna barka da Sallah."
Ana gudanar da Hawan Nasarawa a rana ta uku ga watan Shawwal, kuma yana daya daga cikin muhimman abubuwan bukukuwan Sallah a Kano.
Yadda aka gudanar da Hawan Nasarawa a 2025
Sai dai a bana, kwamishinan ‘yan sanda na Kano, CP Ibrahim Bakori, ya hana hawan Sallah bisa dalilan barazanar tsaro.
A matsayin martani, Sarki Sanusi II ya yanke shawarar gudanar da Hawan Nasarawa ta hanyar jerin gwanon motoci maimakon hawa doki kamar yadda aka saba.
Sarkin, tare da manyan fadawansa, ya bar fadar Kano a cikin gagarumin jerin motocin fada zuwa gidan gwamnati, inda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tarbe shi domin ci gaba da wannan al’ada ta tarihi.
Abin lura shi ne, bana an sauya hanyar da aka saba bi a yayin jerin gwanon Hawan Nasarawa, inji rahoton Leadership.
Duk da wadannan sauye-sauye, dandazon jama’a sun fito suna murna tare da taya sarkin da tawagarsa murna yayin da jerin motocinsa ke wucewa zuwa gidan gwamnati.
Ra'ayin mutanen Kano kan Hawan Nasarawa

Asali: Facebook
Legit Hausa ta tattaro wasu daga cikin ra'ayoyin mutane game da Hawan Nasarawa na wannan shekarar:
Sadeeq G Shuaibu:
"Ni fa a gani na, gara ma murinka yin hawa a mota ya mafi kyau wallahi."
Auwal H Muhammad:
"An gaishe ku Kanawan Dabo."
Shehilfati J Ishaq:
"Ita kan ta wannan gwamnatin ba ta damu da zaman lafiyar al'ummarta ba."

Kara karanta wannan
Ana zargin matashi da kisa a tawagar Sanusi II, ƴan sanda sun gargadi al'ummar Kano
Sa'id H. Sa'id:
"An kashe 'yan uwanmu, maimakon ku soke hawan Sallah don nuna alhininku da zaman makoki, ku bukukuwanku kawai kuke yi ba ku damu ba."
Fatin Mamta:
"Yanzu kalli Sunusi shi da Abba duk cikin bakin ciki, fuska ba annuri , Aminu Ado duk ya bi ya kidima su."
Taha Katar Mgm:
"Allah ya sakawa gwamna da alkairi ya kuma kara wa sarki lafiya da nisan kwana mai albarka."
Kalli hotunan Hawan Nasarawa da aka wallafa a shafin NNPP Kwankwasiya na Facebook a nan kasa:
Hana hawan Sallah: Sanusi II ya yi martani
A wani labarin, mun ruwaito cewa, mai martaba Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya yi tsokaci kan matakin hana hawan Sallah da ‘yan sanda suka dauka.
Sarkin ya bayyana goyon bayansa ga wannan mataki, ya na mai jaddada cewa lafiyar al’ummar Kano ta fi kowanne abu muhimmanci.
Ya bukaci jama’a da su kiyaye doka da oda tare da bai wa hukumomin tsaro cikakken hadin kai domin tabbatar da zaman lafiya a jihar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng