Najeriya Ta Yi Rashi: Yadda Edwin Clark da Fitattun Ƴan Siyasa 4 Suka Mutu a 2025

Najeriya Ta Yi Rashi: Yadda Edwin Clark da Fitattun Ƴan Siyasa 4 Suka Mutu a 2025

A tsakanin Janairu zuwa karshen Maris din 2025, fitattun 'yan siyasar Najeriya biyar sun bakunci lahira, ciki har da Chief Edwin Kiagbodo Clark.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Waɗannan fitattun mutane sun shafe shekaru da dama a harkokin siyasa, inda suka taka rawa wajen inganta tattalin arziki, zamantakewa da shugabanci a ƙasar nan.

Najeriya ta rasa wasu fitattun 'yan siyasa 5 daga Janairu zuwa Fabrairun 2025.
Edwin Clark da wasu fitattun 'yan siyasa 5 da suka mutu a farkon 2025. Hoto:, @Morris_Monye, @abati1990, @adewunmionanuga
Asali: Twitter

Fitattun 'yan siyasa 5 da suka mutu a 2025

Rasuwarsu ta bar babban gibi a duniyar siyasa da kuma zuciyar ‘yan Najeriya, ana ci gaba da tunawa da tarin alkairansu, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kowanne daga cikin 'yan siyasar biyar, ya bayar da gudunmuwa ta musamman a fagen mulki, daga matakin gwamnatin tarayya har zuwa ƙananan hukumomi.

Ga jerin sunayen fitattun ‘yan siyasar da suka rasu a farkon shekarar 2025:

1. Chief Edwin Kiagbodo Clark (1927–2025)

Kara karanta wannan

Yadda 'yan siyasar Najeriya ke rububin sauya jam'iyya gabanin zaben 2027

Edwin Clark ya rasu ne bayan ya yi fama da rashin lafiya
Edwin Clark, ya rasu yana da shekaru 97 a daren Litinin, 17 ga Fabrairu, 2025. Hoto: @Morris_Monye
Asali: UGC

Marigayi Chief Edwin Kiagbodo Clark, babban jigo ne a siyasar yankin Niger Delta, ya kasance mai fafutukar kare hakkin mutanen yankin sa.

Edwin Clark, wanda ya kasance shugaban ƙungiyar dattawan Neja Delta ta PANDEF, ya rasu yana da shekaru 97 a daren Litinin, 17 ga Fabrairu, 2025, kamar yadda muka ruwaito.

An haife shi a ranar 25 ga watan Mayu, 1927, a garin Kiagbodo da ke Jihar Delta. Ya fara aikinsa a matsayin malami kafin ya tsunduma cikin harkokin siyasa a shekarun 1960.

A matsayinsa na ministan labarai daga 1975 zuwa 1978, Clark ya taka muhimmiyar rawa wajen inganta sadarwa tsakanin gwamnati da ‘yan Najeriya.

Ya kasance ɗaya daga cikin fitattun jagororin da suka yi fafutukar a bai wa yankin Niger Delta kulawa ta musamman, tare da fafutukar samun karin kudaden shiga ga jihohin da ke da arzikin man fetur.

A shekarar 2015, ya sanar da janyewar sa daga siyasa, amma har zuwa rasuwarsa ya na bayar da shawarwari kan sha’anin mulki a Najeriya.

Kara karanta wannan

Ana zargin matashi da kisa a tawagar Sanusi II, ƴan sanda sun gargadi al'ummar Kano

2. Pa Ayo Adebanjo (1928–2025)

Ayo Adebanjo ya rasu bayan ya yi fama da rashin lafiya
Ayo Adebanjo ya rasu a ranar 14 ga Fabrairu, 2025, yana da shekaru 96. Hoto: @abati1990
Asali: Twitter

Marigayi Chief Ayo Adebanjo, wani fitaccen ɗan siyasa ne kuma jigo a kungiyar Afenifere, wanda ya shafe fiye da shekaru 70 ya na fafutukar adalci da dimokuradiyya a Najeriya.

An haife shi a ranar 10 ga Afrilu, 1928, a garin Isanya Ogbo da ke jihar Ogun, kuma ya fara harkokin siyasa tun ya na matashi.

A matsayinsa na mamba a jam’iyyar AG karkashin jagorancin Chief Obafemi Awolowo, ya taka rawar gani a fafutukar kafa tsarin dimokuradiyya a yankin Kudu maso Yamma.

A lokacin mulkin soja a Najeriya, Pa Adebanjo ya kasance ɗaya daga cikin manyan ‘yan adawa da suka yi fafutuka domin dawo da tsarin mulkin farar hula.

Har zuwa rasuwarsa, yana jagorantar Afenifere, wata kungiya da ke kare muradun mutanen Yarbawa, yana kuma kira ga tsarin mulkin tarayya mai bai wa kowane yanki damar cin gashin kansa.

Legit Hausa ta ruwaito cewa Ayo Adebanjo ya rasu a ranar 14 ga Fabrairu, 2025, yana da shekaru 96, bayan ya kwashe lokaci yana fama da rashin lafiya.

Kara karanta wannan

Sanatocin Arewa sun haɗa kai, sun taso da ƙarfi kan abin da aka yi wa ƴan Arewa a Edo

3. Rt. Hon. Adewunmi Onanuga (1965–2025)

Adewunmi Onanuga ta rasu ne bayan fama da rashin lafiya
Adewunmi Onanuga ta rasu a ranar 15 ga Janairu, 2025, tana da shekaru 59. Hoto: @adewunmionanuga
Asali: Twitter

Marigayiya Adewunmi Oriyomi Onanuga, wacce aka fi sani da “Ijaya”, ta kasance jagora a majalisar wakilai, ta zama mataimakiyar mai tsawatarwa ta majalisar.

An haife ta a ranar 2 ga Disamba, 1965, a birnin London, kuma ta yi karatu a Najeriya da kuma ƙasashen waje.

Tun kafin ta shiga siyasa, Onanuga ta yi aiki a sassa daban-daban na gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu, ciki har da Quaker Oats Plc a Ingila da Southgate Technologies a Najeriya.

A shekarar 2019, aka zabe ta a matsayin 'yar majalisar wakilai, ta wakilci mazabar Ikenne/Sagamu/Remo ta Arewa karkashin jam’iyyar APC.

Ta kasance mai goyon bayan kare hakkin mata da ‘yan kasa masu bukata ta musamman, tare da neman a samar da ma’aikatar kula da manyan mutane.

A shekarar 2023 aka sake zaɓenta a karo na biyu, sai aka naɗa ta a matsayin mataimakiyar bulalar majalisar, kuma ita kaɗai ce mace da ta riƙe mukamin shugabanci a majalisar.

Kara karanta wannan

Kungiyar Izalah ta yi maganar kisan ƴan Arewa a Edo, ta fadi hanyar dakile lamarin

Hon. Onanuga ta rasu a ranar 15 ga Janairu, 2025, tana da shekaru 59, bayan ta yi fama da gajeruwar rashin lafiya, kamar yadda muka ruwaito.

4. Justice Azuka (???–2025)

Justice Azuka ya rasu ne bayan watanni da yin garkuwa da shi
An gano gawar Justice Azuka a ranar 6 ga Fabrairu, 2025 bayan kimanin wata biyu da sace shi. Hoto: @betacuntri
Asali: Twitter

Marigayi Justice Azuka, ɗan majalisar dokokin jihar Anambra mai wakiltar Onitsha North 1, ya rasu ne bayan kwanaki da sace shi.

Mun ruwaito cewa an sace shi a ranar 24 ga Disamba, 2024, kuma bayan kimanin wata biyu an gano gawarsa a ranar 6 ga Fabrairu, 2025.

Mutuwarsa ta jefa al’umma cikin alhini, mutane da dama suka bukaci a inganta tsaro domin kare rayukan jami’an gwamnati da sauran ‘yan kasa.

Ya kasance mai fafutukar kare muradun mazabarsa, ya yi aiki tare da matasa da kungiyoyin ci gaba don inganta rayuwar al’umma.

Rasuwarsa ta haifar da kiraye-kirayen a kawo karshen hare-haren da ake kai wa ‘yan siyasa da sauran jami’an gwamnati a kasar nan.

5. Dr. Doyin Okupe (1952–2025)

Kara karanta wannan

Bayan kona 'yan Arewa kurmus a Edo, an kashe mutane 10 da ke zaman makoki a Filato

Doyin Okupe ya rasu bayan fama da cutar daji
Dr. Doyin Okupe ya rasu a ranar 7 ga Maris, 2025, yana da shekaru 72. Hoto: @TheoAbuAgada
Asali: UGC

Marigayi Dr. Doyin Okupe, wani likita ne wanda ya yi suna a fagen siyasa, musamman a matsayin mai ba wa shugabanni shawara kan harkokin yada labarai da al’amuran jama’a.

Legit Hausa, ta rahoto cewa, Dr. Doyin Okupe ya rasu a ranar 7 ga Maris, 2025, yana da shekaru 72, bayan fama da cutar daji.

An haife shi a ranar 22 ga Maris, 1952, a birnin Lagos, amma iyayensa 'yan asalin garin Iperu ne da ke jihar Ogun.

Ya yi karatu a jami’ar Ibadan, ya kammala digirinsa a fannin kiwon lafiya, sannan daga baya ya kafa cibiyar Royal Cross Medical a birnin Lagos.

Okupe ya rike mukamin mataimakin darakta na kamfen din Shugaba Olusegun Obasanjo a 1999, kuma daga baya aka naɗa shi a matsayin mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai.

A lokacin mulkin Shugaba Goodluck Jonathan, an sake naɗa shi a matsayin mataimakin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin hama’a.

Kara karanta wannan

Masu bautar kasa a Najeriya na cikin alheri dumu dumu, Tinubu ya fara biyan N77, 000

Ya kasance ɗaya daga cikin kusoshin yakin neman zaɓen Peter Obi a 2022 kafin daga baya ya janyewa Yusuf Datti Baba-Ahmed.

Mataimakin gwamnan jihar Delta ya mutu

A wani labarin, mun ruwaito cewa, tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Delta, Farfesa Amos Utuama, ya riga mu gidan gaskiya.

Marigayin, wanda lauya ne mai matsayi na SAN, ya rasu da safiyar Asabar, 2 ga Nuwamba, 2024, a birnin Legas.

Farfesa Utuama ya rike mukamin Mataimakin Gwamna a lokacin mulkin Emmanuel Uduaghan, suka yi shekara takwas tare karkashin jam’iyyar PDP.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng