Yunkurin Raba Sanata Natasha da Kujerarta: An Ji abin da INEC Za Ta Yi a Kwana 90
- A makon da ya gabata, mazauna yankin Kogi ta Tsakiya sun gabatar da bukatar yi wa Natasha Akpoti Uduaghan kiranye daga majalisar dattawa
- Idan fiye da rabin masu kada kuri’a sun amince da bukatar, INEC za ta gudanar da kuri’ar raba gardama cikin kwanaki 90 domin tantance makomarta
- Bukatar kiranyen ta samo asali ne daga dakatar da Natasha daga majalisa bisa zargin “munanan halaye” bayan sabani da Shugaban Majalisar Dattawa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Ana sa ran Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da aka dakatar, wacce ke wakiltar yankin Sanatan Kogi ta Tsakiya, za ta san matsayinta a cikin kwanaki 90.
A makon da ya gabata, wasu mazauna yankin da take wakilta suka gabatar da takardar bukatar yi mata kiranye daga zauren majalisar dattawa ga hukumar INEC.

Asali: Facebook
Lokacin da INEC za ta kada kuri'ar raba gardama
A halin yanzu, INEC na cikin matakin tantance sahihancin sa hannun wadanda suke neman yi wa Sanata Natasha kiranye, inji rahoton Punch a ranar Litinin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Domin aiwatar da bukatar kiranyen, dole ne fiye da rabin masu rajistar kada kuri’a a yankin Kogi ta Tsakiya su sanya hannu kan bukatar.
Idan wannan sharadi ya cika, hukumar za ta gudanar da kuri’ar raba gardama cikin kwanaki 90 daga ranar da aka karɓi takardar neman yi mata kiranye.
Sababbin ka’idojin INEC na 2024 kan yi wa ‘yan majalisa kiranye sun nuna cewa, hukumar za ta fitar da sanarwa dangane da lokaci, rana, da wurin da za a gudanar da kuri’ar raba gardama idan sharadin kiranyen ya cika.
Abin da zai sa a yi wa dan majalisa kiranye
Sai dai idan adadin masu rajistar kada kuri’a da ake bukata ba su cika ba, nan ma hukumar za ta fitar da sanarwa tana bayyana hakan.
INEC ta bayyana cewa:
“Hukumar za ta gudanar da kuri’ar raba gardama idan ta tabbatar da cewa fiye da rabin masu rajistar kada kuri’a a mazabar sun goyi bayan yi wa dan majalisa kiranye. Wannan za a yi shi a kasa da kwanaki 90 daga ranar da aka karɓi bukatar.
“Za mu fitar da sanarwa ta musamman da za ta bayyana rana, lokaci, da wurin da za a gudanar da kuri’ar raba gardama.
“Idan kuma bayan tantancewa an samu cewa masu goyon bayan bukatar basu kai fiye da rabin masu rajista ba, nan ma hukumar za ta fitar da sanarwa domin yin bayani.”
Natasha na fuskantar kiranye daga majalisa

Asali: Facebook
Bukatar yi wa Sanata Natasha kiranye ta samo asali ne daga cece-kuce da ya biyo bayan dakatar da ita daga majalisar dattawa a ranar 6 ga Maris.
An ce an dakatar da Sanata Natasha ne bisa zargin “munanan halaye” bayan sabani da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio.

Kara karanta wannan
Ana zargin matashi da kisa a tawagar Sanusi II, ƴan sanda sun gargadi al'ummar Kano
Takardar neman yi mata kiranye, wacce ke dauke da dalili na “rashin gamsuwa” da wakilcinta, ta zarge ta da rashin da’a, amfani da ofis ba bisa ka’ida ba, da kuma yaudarar jama’a.
An gabatar da takardar bukatar tare da jakunkuna shida cike da takardu masu dauke da sa hannun fiye da rabin masu kada kuri’a 474,554 da ke Kogi ta Tsakiya.
An tattara wadannan sa hannun ne daga rumfunan zabe 902 da ke fadin kananan hukumomi biyar: Adavi, Ajaokuta, Ogori/Magongo, Okehi, da Okene.
INEC ta aika sako ga Sanata Natasha
A wani labarin, mun ruwaito cewa, INEC ta sanar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan cewa ta fara tantance sa hannun masu neman yi mata kiranye daga majalisa.
Hukumar INEC ta ce ta kuma karɓi cikakkun bayanan masu ƙorafin waɗanda ba su cika takardun da suka shigar a baya da kyau ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng