Daga Hukumar INEC: Tambayoyi 21 da amsoshinsu kan batun kiranyen 'yan majalisa
Hukumar zabe ta kasa, INEC, ta bayar da jaddawalin bayanai kan irin tambayoyin da jama'a kanso su yi wa dan majalisar su kiranye, guda 21, duba amsoshin a kasa.
1. Tambaya: Menene Kiranye?
Amsa: Kiranye shine korafin jama'a ga hukumar INEC domin a dawo musu da dan majalisar su gida domin su tura wani.
2. Wadanne matakai ake bi don yin kiranye?
Rubuta takarda ga shugaban hukumar zabe, da saka hannun akalla rabin wadanda suka yi rajista a yankin, duk da korafinsu a ciki.
3. Shin kiranye aikin hukumar zabe ne?
Sashe na (69) dana (110) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya da kuma na (116) na Sashen Dokar Zaben Kasa da aka ma kwaskwarima, ya bada damar kiranye ga dan Majalisar Tarayya da kuma dan Majalisar Jiha, ko kuma kamsila daga yankin birnin Tarayya, ya fadi cewa idan har kashi 50 bisa dari (wato 50%) daga cikin wadanda ake wakilta suka nuna rashin gamsuwa akan wanda yake wakiltar su, suna da damar yin kiranye ga dan majalisar mai wakiltarsu, su kuma tura wani bayan yaci zabe.
4. Tsawon kwanaki nawa ne hukumar zabe ke dauka kafin kiranye ya tabbata?
Dole cikin kwanaki 90 da karbar takardar korafin masu zabe, a yi duk abubuwan da ake bukata a rufe batun, ko kiranye ko barin dan majalisa.
5. Su wa za'a iya yiwa kiranye?
Dan majalisar jiha, ko na tarayya, ta dattijai ko ta wakilai, da kuma kamsila a babban birni a Abuja.
6. Waye ke da hakkin faro kiranyen?
Jama'ar yankin da wakilin ya fito, musamman in sun kai rabin masu rajistar zabe na wurin.
7. Ta yaya mutum zai gane yawan masu cikakkiyar rajista a yanki?
A ofishin hukumar ta zabe mafi kusa da ku ake iya samun kwafi na asalin yawan masu rajista daga kowacce maraya.
DUBA WANNAN: Shugaba Buhari ne zaqi lashe zaben 2019, inji Aso Rock
8. A ina ake iya samun bayanai kan rumfunan zabe?
Ko a ofishin hukumar na jiha, ko kuma a shafinsu na yanar gizo wato: http://www.inecnigeria.org/
9. Me INEC ke yi bayan an kai mata korafin kiranye?
Hukumar zata tantance cewa saka hannun sahihi ne, kuma ta tabbatar na yan yankin ne, kuma suna da rajista, sannan ta duba ko sun kai rabin jama'ar da suka yi rajista a yankin.
10. Me zai faru idan koraffin bai kai yawan rabin jama'ar yanki?
Hukumar zata gaya wa jama'ar cewa korafinsu bai kai yawan da ake tsammani ba, hakkinsu ne su hakura ko su koma su karo jama'arsu, su sake rubutowa.
11. Shin masu korafi na iya janye korafin kiranye?
Tabbas. Zasu iya yi wa takardar ta korafinsu kiranye ita ma, kafin hukumar ta gama tantance wa, muddin wadanda suka sanya hannun ne ko wakilansu da suka aiko da takardar.
12. Meye tantance wa?
Bin diddigin sa hannun, sunaye da ke kan takardar, ko na gaske ne ko na bogi, kuma suna da rajista daga yankin? Ana tantance su kafin ayi zaben raba gardama.
13. A ina ake bin diddigin?
A inda akwatunan zabe suke a yankin da korafin ya fito.
14. Suwa ake tantancewa?
Masu korafi kadai, kowa a akwatin layinsu, banda wadanda basu da korafi.
15. Menene zaben raba gardama, bayan an gama bin diddigi?
Shine zaben 'E' ko 'A'a' da ake gudanarwa wanda duk mai rajista zai iya shiga, ko yana da korafi ko kuma a'a.
16. Su wa ke shiga zaben raba gardama?
Duk masu rajista da ska fito daga mazaba/yankin da ake korafi kan wakili.
17. Ta yaya za'a gane ko zaben raba gardama (rafarandan) yayi nasara?
In 'E' ta kai rabin masu zabe, ta kuma haura da 1 tal.
18. A ina ake zaben raarandan din?
A rumbunan zaben yankin da korafi ya fito.
19. Me zai faru bayan an yi wa wakili kiranye?
Za'a kai sakamakon ga shugaban majalisar wakilin, sai shi kuma ya isar wa da korarren wakilin sakon mutanen mazabar sa, sai ya bar majalisa ya koma kauye fanko. Sai kuma a sake zabe a yankin, jama'a su aiko wanda ya kwanta musu cikin masu takara.
20. Shin korarren wakili zai iya sake tsayawa takara?
Doka bata hana korarren wakili ya sake tsayawa takara ba.
21. Shin ana iya yi wa shugaban kasa kiranye? Ko Gwamna? Ko Chiyaman na karamar hukuma?
A'a, su ba'a yi musu kiranye. Amma ana iya tsige su.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng