Iyalan Hausawan da aka Kashe a Edo Sun Yi Magana cikin ban Tausayi
- Iyalan mutane 16 da aka kashe a Uromi, Edo, sun bukaci hukuma ta tabbatar da adalci kan lamarin
- Shugaban al’ummar Torankawa ya ce wannan bala’i ne da ba za a taba mantawa da shi ba saboda girmansa
- Mutanen da aka kashen sun bar 'ya'ya, mata da yara kanana da a yanzu haka ba a san wane hali za su shiga ba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Iyalan mutane 16 ‘yan Arewa da wasu mutanen Edo suka kashe a garin Uromi sun bukaci hukuma ta tabbatar da adalci kan lamarin.
Mutanen sun taso ne daga Fatakwal, Jihar Ribas, zuwa Kano domin yin bikin Sallah kafin wasu ‘yan banga suka tare su tare da hallaka su bisa zargin su da laifin garkuwa da mutane.

Asali: Getty Images
A wata tattaunawa da suka yi da jaridar Daily Trust, iyalan sun bayyana yadda ‘yan uwansu suka kira su kafin a hallaka su, tare da bayyana yadda har yanzu al’ummar su ke cikin zaman makoki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Ya kirani yana neman addu’a kafin a kashe su”
Muhammadu Sunusi Torankawa, dan uwan shugaban 'yan farautar da aka kashe, Ibrahim Isa, ya bayyana yadda suka yi waya kafin a kai musu farmaki.
"Ya kirani cikin tashin hankali yana cewa muna cikin hatsari, ku yi mana addu'a. Ya ce an sare shi da adda a kafaɗa kusa da wuyansa, amma bai mutu ba saboda kariya da ya ke da ita.
"Ya buya yana kallon yadda ake jan mutanensa daya bayan daya ana kona su da ransu. Ya riga ya fid da rai cewa zai mutu, amma Allah ya kiyaye shi aka kai shi asibiti,"
- Muhammadu Sunusi Torankawa
Ibrahim Isa ne kadai ya tsira daga harin a kauyen Torankawa kuma yanzu haka yana kwance a asibiti a Edo, yana fama da raunuka.
“Na rasa dana, dan uwana da ɗan yayata”
Wata matar da ke cikin alhinin wannan bala’i, Sadiya Sa’adu, ta ce ta rasa dan ta, Haruna Hamidan, da kuma wasu ‘yan uwa guda biyu a harin.
Sadiya Sa’adu ta bukaci mahukunta su tabbatar da adalci domin kada rayukan ‘ya’yanta su tafi a banza.
"Ba 'yan ta'adda ba ne, sun fita ne domin neman halal. Ya kamata a hukunta wadanda suka aikata wannan mummunan aiki,"
- Sadiya Sa’adu

Asali: Facebook
"Ya bar gida yana fatan kammala ginin sa"
Zahura, matar daya daga cikin wadanda aka kashe, Haruna Hamidan, ta ce mijinta ya kira ta sa’o’i biyu kafin a kashe su yana fada mata cewa suna kan hanya zuwa gida.

Kara karanta wannan
Hafsan tsaro ya tsoma baki kan kisan ƴan Arewa a Edo, ya fadi shirinsu kan lamarin
"Ya bar ni da ‘ya’ya hudu da kuma gida da bai kammala ba, burinsa kenan. Amma kaddara ta riga fata,"
In ji Zahura cikin kuka
“Umma, ku yi mana addu’a”
Aisha Harisu, mahaifiyar wani matashi mai shekara 21 da aka kashe, Abdullahi Harisu, ta ce maganar karshe da dan ta ya yi mata a waya ita ce:
"Umma, ku yi mana addu’a."
Khadija, matar sa da suka yi aure watanni hudu da suka wuce, ta kasa magana saboda radadin alhini, mahaifin sa ya ce dansa ya fita da izinin sa domin yin farautar da suke yi a duk shekara.
“Ba za mu taba mantawa da shi ba”
Yakubu Alhaji Abdu Torankawa, wakilin dagacin garin Torankawa, ya bayyana cewa wannan bala’i ne da ba za a taba mantawa da shi ba.
Abdu Torankawa ya ce:

Kara karanta wannan
Bidiyon yadda aka yi jana'iza, aka birne ’yan Arewa 16 a Edo cikin hawaye da tausayi
"Mun yarda da kaddara, amma wannan abu abin takaici ne.
Wadanda aka kashe dukkansu matasa ne, sun fito da izinin masarautar Kano kuma suna da duk wasu takardu na izini,"
Ya bukaci gwamnati ta gaggauta daukar mataki don tabbatar da adalci ga wadanda suka rasa rayukansu da kuma iyalansu da ke cikin halin bakin ciki.
Abba zai tura tawaga daga Kano zuwa Edo
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Kano ta shirya domin tura wakilai jihar Edo saboda bincike kan mutanen da aka kashe a Uromi.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce za su tabbatar an yi adalci wa iyalan mamatan tare da kokarin ganin an biya iyalansu diyya.
Asali: Legit.ng