Ana Tsaka da Bukukuwan Karamar Sallah a Najeriya, an Kara Farashin Man Fetur
- Kamfanin MRS ya kara farashin man fetur zuwa N930 a Lagos da N960 a Arewa bayan dakatarwar sayarwa da naira daga matatar Aliko Dangote
- Sabon farashin man fetur daga MRS ya fara aiki tun 28 ga Maris 2025, inda ya karu da N70 a Kudu da N80 a Arewa
- Wasu gidajen mai kamar NIPCO a Magboro sun fara sayar da mai a sabon farashin N930, yayin da Arewa ke fuskantar mafi tsada
- Masana sun ce farashin zai iya saukowa idan matatar Dangote ta fara sayar da mai da naira, amma har yanzu 'yan Najeriya na fama da tsada
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Sakamakon dakatar da sayar da man fetur da naira daga matatar Dangote, gidan mai na MRS ya kara farashin mai a Najeriya .

Kara karanta wannan
Ana zargin matashi da kisa a tawagar Sanusi II, ƴan sanda sun gargadi al'ummar Kano
Rahotanni sun ce kamfanin MRS ya kara farashin zuwa N930 a Lagos da kuma N960 a Arewacin Najeriya.

Asali: Getty Images
Kamfanin MRS ya kara farashin fetur a Najeriya
Jaridar Punch ta ce sabon tsarin farashin ya fara aiki tun 28 ga Maris 2025 da muke ciki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Farashin ya nuna karin N70 daga N860 a Lagos da N870 a Kudu maso Yamma, da kuma karin N80 daga N880 a Arewa.
An gano cewa wasu gidajen mai sun fara sayar da mai a wannan sabon farashi, misali, a Magboro, jihar Ogun, NIPCO na sayar da mai a N930.
Sabon jadawalin farashi daga kamfanin MRS ya nuna cewa motocin tankar kamfanin za su dauko mai daga ma'ajiya a Lagos zuwa gidajen man sa a kasar.
Takardar ta nuna cewa Lagos na da mafi karancin farashi, yayin da yankunan Arewa ke fuskantar mafi tsada.
Sai dai har yanzu ba a tabbatar da ko kamfanin MRS na siyan mai daga matatar man Aliko Dangote ba.

Kara karanta wannan
Kungiyar Izalah ta yi maganar kisan ƴan Arewa a Edo, ta fadi hanyar dakile lamarin

Asali: Facebook
Yadda farashi yake a Lagos da Arewa
A Lagos, man fetur zai kasance N930 kowace lita, yayin da jihohin Kudu maso Yamma da Kwara za su biya N940 kowace lita.
A yankunan Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas, kamar Edo, Abia, Akwa Ibom, Bayelsa, Rivers, Cross River, da Enugu, farashin ya kai N960 kowace lita.
Jihohin Arewa na da bambancin farashi, a Abuja, Kaduna, Benue, Kogi, Niger, Sokoto, Kebbi, da Nasarawa, farashin shi ne N950 kowace lita.
A Zamfara, Kano, Jos, Bauchi, Taraba, Adamawa, Borno, Katsina, Jigawa, Gombe, da Yobe, farashin ya kai N960 kowace lita.
A Lagos, mafi karancin farashin FCA shi ne N905 kowace lita, yayin da jihohin Borno, Taraba, Adamawa, da Yobe ke da farashin N888 kowace lita.
Legit Hausa ta tattauna da dillalin mai
Wani dillalin mai ya magantu kan lamarin karin kuɗin mai daga kamfanin MRS.
Muhammad Hussaini a Gombe ya ce tabbas haka ne amma bai da alaka da matakin da Dangote ya dauka.
Ya ce:
"Duk ƙarin kudin mai da aka yi yana da tasiri sosai a kan cinikayya da muke yi a kasuwarmu."
Hussaini ya ce akwai bukatar samun tsari a farashin fetur domin ci gaba da inganta harkokinsu.
Kungiya ta magantu kan kara kudin mai
Kun ji cewa Kungiyar ƴan kasuwar mai watau PETROAN ta ce har yanzu matatar Ɗangote ba ta fara sayar da kayanta da Dalar Amurka ba.
Shugaban ƙungiyar, Billy Gillis-Harry ya kuma tabbatar da cewa kamfanin Ɗangote bai ƙara farashin fetur ga ƴan kasuwa ba.
Billy ya ce kuɗin da ake saye da sayarwa da kudin sufuri na cikin abubuwan da suke taka rawa wajen tashi ko saukar farashin man fetur.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng