Gaskiyar kenan: Wike Ya Fito Ya Fadi Dalilin Kwace Filin Jam'iyyar PDP a Abuja

Gaskiyar kenan: Wike Ya Fito Ya Fadi Dalilin Kwace Filin Jam'iyyar PDP a Abuja

  • Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Ezenwo Wike, ya kare kansa kan ƙwace filin jam'iyyar PDP a Abuja
  • Wike ya bayyana cewa ba a ƙwace filin na babbar jam'iyyar adawa a Najeriya ba ne saboda dalilai na sabanin siyasa
  • Ministan ya ce an ƙwace takardar mallakin filin ne saboda PDP ta ƙi biyan kuɗin harajin da ake bin ta na tsawon shekaru

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya yi magana kan soke takardar mallakar filin jam'iyyar PDP.

Nyesom Wike ya musanta iƙirarin jam’iyyar PDP cewa an soke takardar mallakar filin ne a matsayin wata maƙarƙashiya don danne ƴan adawa.

Wike ya yi magana kan kwace filin PDP
Nyesom Wike ya ce ba siyasa a cikin dalilin kwace filin PDP a Abuja Hoto: @OfficialPDPNig, @GovWike
Asali: Twitter

Wike ya bayyana hakan ne yayin wata ziyara da wasu lauyoyi ƙarƙashin jagorancin shugabansu, babban lauya Adegboyega Awomolo, suka kai masa a Abuja a ranar Juma’a, cewar rahoton jaridar The Punch.

Kara karanta wannan

"Ba yau aka fara ba," Gwamnatin Kano ta yi zazzafan martani kan kisan ƴan Arewa a Edo

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa aka ƙwace filin jam'iyyar PDP?

Wike wanda shi ma lauya ne, ya nuna mamaki kan zargin da PDP ke yi cewa an umurce shi da ya soke takardar mallakar filin jam’iyyar da ke yankin Central Area a Abuja, don muzgunawa ƴan adawa.

Ya bayyana cewa a Najeriya, ana danganta kowane irin matakin da gwamnati ke ɗauka da siyasa, addini ko ƙabilanci.

Ya bayyana cewa ana yi wa soke filayen da mamallakansu suka kasa biyan kuɗin haya na sama da shekaru 10 gurguwar fassara, ya ce wasu na ganin kamar an yi hakan ne saboda siyasa.

Wike ya jaddada cewa PDP ta shafe shekaru da dama tana mulki amma ta kasa biyan kuɗin haraji na Naira miliyan 7.6 domin filin da take gina babbar sakatariyarta a Abuja.

Wike ya zargi PDP da kin biyan haraji

Ya ƙara da cewa, duk da cewa PDP ta samu kuɗade tsakanin N13bn zuwa N20bn ta hanyar siyar da fom ɗin takara, jam’iyyar ta kasa biyan kuɗin haraji na N7.6m.

Kara karanta wannan

"Hantar Tinubu ta kaɗa": An faɗi wanda ya dace Atiku, Obi da El Rufai su marawa baya a 2027

Har ila yau, Wike ya bayyana cewa Wadata Plaza, inda PDP ke gina babbar sakatariyarta, ba a yi rijistar mallakarsa a matsayin na jam’iyyar ba, sai dai an yi rijistar filin a ƙarƙashin wani Sanata da ke zaune a Abuja.

Ya ce wanda ya yi rijistar filin ya kasa biyan kuɗin haraji na tsawon shekaru 28, amma PDP na ci gaba da iƙirarin cewa yana ƙoƙarin kwace mata sakatariya.

"Watakila sun yi wata yarjejeniya da shi amma ba su kammala ba, sai suka fara ihun cewa wai an turo Wike don ya soke filin don hana ƴan adawa yin aiki.
"Wane irin tunani ne hakan?"

- Nyesom Wike

Nyesom Ezenwo Wike
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike Hoto: @GovWike
Asali: Facebook

Wike ya ce har filin INEC an ƙwace

Ya jaddada cewa ba PDP kawai aka soke filinta ba, domin hukumomi da sauran kamfanoni kamar hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) da babban bankin Najeriya (CBN) ma an ƙwace na su.

Kara karanta wannan

Faɗan giwaye: Ɗan majalisa na neman kassara Sanata Yari domin rage masa tasiri?

Ya ce CBN na rokon a maida masa takardar mallakar filinsa, amma sai ya shaidawa bankin cewa sai ya biya kuɗin harajin da ya wajaba a kansa kafin a yi hakan.

An buƙaci a kori Wike daga PDP

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu daga cikin mambobin jam'iyyar PDP sun buƙaci a kori Nyesom.Wike daga PDP.

Ƙungiyar ƙwararru ta PDP (PDP-CP) ta buƙaci a kori ministan na birnin tarayya Abuja ne saboda goyon bayan da ya ba Bola Tinubu a zaɓen 2023.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel