Hukuncin Rama Sallar Idi da yadda ake Yin Ta a Gida idan an Makara

Hukuncin Rama Sallar Idi da yadda ake Yin Ta a Gida idan an Makara

  • Hankulan al'ummar Musulmi ya fara karkata kan sallar Idi yayin da ake daf da kammala azumin watan Ramadan
  • Malamai sun bayyana cewa wanda ya makara bai riski sallar ba ana son ya rama, amma ba tare da ya yi huduba ba
  • Biyo bayan hukuncin rama sallar, masana fikihu sun yi sabani kan halaccin yin ta a gida ga wanda ya kasa zuwa filin ibada

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Sallar Idi ibada ce da Musulmai ke gudanarwa bayan kammala azumin Ramadan ko lokacin sallar lahiya.

Wani lokaci wasu kan makara ko su rasa damar halarta, hakan na haifar da tambayoyi kan yadda za su yi da sallar.

Dr Ahmad
Wanda ya rasa sallar Idi zai iya ramawa. Hoto: Sheikh Dr Ahmad BUK
Asali: Facebook

Domin samar da mafita, marigayi Sheikh Dr Ahmad Ibrahim Muhammad Bamba ya taba amsa tambayar a wani bidiyo da aka wallafa a shafin X.

Kara karanta wannan

Sheikh Pantami ya jero hanyoyi 3 da za a kama waɗanda suka kashe yan Arewa a Edo

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malamai sun yi bayani kan yadda wanda bai samu halartar Sallar Idi ba zai iya rama ta ko kuma idan ana iya yin ta a gida.

Hukuncin wanda ya makara sallar idi

Marigayi Sheikh Ahmad Bamba ya ce ya halasta wanda ya rasa sallar Idi ya rama kamar yadda malamai suka tabbatar.

"Imam Malik ya ce idan wanda ya makara ya yi sallar Idi a gida ko a masallaci babu laifi."

- Dr Ahmad Bamba

Sheikh Ahmad Bamba ya ya yi bayanin ne a cikin wani karatun Muwadda Malik da ya gabatar a lokacin rayuwarsa.

Marigayi Sheikh Bamba ya kara da cewa a fahimtar Imam Malik babu laifi idan mutum bai rama sallar ba.

Haka zalika ya kara da cewa mutum zai rama sallar ne da yin kabbara guda bakwai a farko kafin karatun sura sai ya yi kabbara biyar a raka'a ta biyu.

Kara karanta wannan

Jerin kura kurai 5 da musulmi ke yi a ranar ƙaramar sallah da yadda za a kauce masu

Karin bayanin da malamai suka yi

Sheikh Salih Al-Munajjid ya wallafa a shafinsa cewa Idan mutum ya zo masallacin Idi amma ya tarar ana huduba, ya wajaba ya saurari hudubar Imam kafin ya rama sallarsa.

A cewar malamai kamar Imam Malik, Shafi’i da Ahmad, ya na da kyau wanda bai samu sallar ba ya rama ta, amma ba tare da huduba ba.

An rawaito daga Anas bin Malik cewa idan bai samu Sallar Idi da liman ba, ya kan tara iyalinsa da bayi sannan su yi salla raka'a biyu tare da yin kabbarori.

Shin ana iya yin sallar Idi a gida?

Sheikh Al-Munajjid ya ce malamai sun yi sabani kan ko ana iya yin Sallar Idi a gida idan mutum bai samu halarta a filin Idi ba.

A fatawar Imam Shafi’i da wasu malamai, mutum na iya yin Sallar Idi a gida shi kadai ko a cikin jam’i.

Kara karanta wannan

Yadda Musulmi zai yi bikin sallah da Idi cikin nishadi a tsarin Musulunci

Imam Malik ya ce yin hakan ya na da kyau, amma ana iya yin ta a jam’i ko kuma mutum ya yi shi kadai.

Yadda ake yin sallar Idi a gida

Masana fikihu sun bayyana cewa idan mutum yana so ya rama Sallar Idi a gida, to zai yi raka'a biyu kamar yadda ake yi a filin Idi.

A kan fara kabbarori guda bakwai a raka’a ta farko, sannan a karanta Fatiha da sura, sai a yi raka’a ta biyu da kabbarori biyar kafin a ci gaba da sallah kamar yadda aka saba.

Sai dai malamai sun ce ba a yin huduba bayan sallar idan mutum ya yi ta a gida ko kuma a lokacin ramuwa.

Sallar Idi
Yadda musulmai suka yi Idi a bara. Hoto: Getty Image
Asali: Getty Images

An bukaci fara duba watan sallah a Saudiyya

A wani rahoton, kun ji cewa kasar Saudiyya ta fitar da sanarwa kan fara duba watan Shawwal yayin da ake kokarin kammala azumi.

Hukumomi a kasar sun bukaci dukkan wanda ya ga wata da idonsa ko da na'ura da ya gaggauta sanar da kotu mafi kusa da shi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng