Ana Shirin Sallah: An Kara Kudin Litar Man Fetur a Najeriya
- Farashin litar man fetur ya tashi daga N890 zuwa N900 a manyan wuraren dillalai mai masu zaman kansu a kasar nan
- Rahotanni sun nuna cewa karin farashin ya samo asali ne daga hauhawar farashin danyen mai a kasuwar duniya
- Masana sun ce dakatar da tsarin sayar da danyen mai a Naira a Najeriya na iya kara dagula lamarin fetur a kasar nan
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Manyan dilolin man fetur masu zaman kansu sun kara kudin litar mai zuwa N900, daga N890 da ake sayarwa a makon da ya gabata.
Hakan na zuwa ne yayin da aka fara samun tangarda kan cinikin danyen mai da Naira tsakanin matatar Dangote da kamfanin NNPCL.

Kara karanta wannan
Bayan kona 'yan Arewa kurmus a Edo, an kashe mutane 10 da ke zaman makoki a Filato

Asali: Getty Images
Binciken da Vanguard ta gudanar ya nuna cewa kamfanonin Rainoil, Prudent, A.Y.M Shafa da Mainland sun kara kudin litar mai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Karin na da nasaba da tashin farashin danyen mai a kasuwar duniya, wanda ya haura daga $70 zuwa $75, lamarin da ke kara tsadar sarrafa mai a matatun Dangote da na ketare.
Tasirin sayar da danyen mai da Naira
Binciken da aka gudanar ya tabbatar da cewa matatar Dangote, mai karfin tace gangar mai 650,000 a rana, ba ta sayar da mai ga masu motocin dakon mai a karshen mako ba.
A cewar wani rahoto, lamarin ya shafi wasu kamfanonin man fetur kamar MRS da Ardova, wadanda ke kokarin samun isassun kayayyakin man fetur ta jiragen ruwa daga ketare.
A cewar rahoton:
"Tuni masu dakon mai sun kara farashin lita zuwa N900, yayin da gidajen mai masu zaman kansu ke sayar da shi tsakanin N930 zuwa N950 a wasu yankuna."
Bayanin kungiyar MEMAN kan tsadar mai
A halin yanzu, kungiyar Major Energies Association of Nigeria (MEMAN) ta bayyana cewa farashin shigo da man fetur ya karu da N88 a cikin sati guda.
MEMAN ta shaida hakan a cikin rahoton ta na yau da kullum a ranar Laraba, 26 ga Maris, 2025, inda ta ce farashin ya tashi daga N797 zuwa N885 a wannan mako.
A cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar, ta bayyana cewa:
"Yayin da kasuwar man fetur ke kokarin sauyawa, za a ci karo da matsaloli da kuma adawa daga wadanda suka saba da tsare-tsaren da gwamnati ke aiwatarwa.
"Amma idan aka samar da ingantaccen tsarin kula da harkar mai, hadin gwiwar masana’antu, da kuma shugabanci na gari, Najeriya za ta iya cin moriyar wannan sauyi."

Asali: Facebook
Za a daina samun karin farashin fetur?
MEMAN ta ce idan aka samu tsarin kasuwanci mai inganci, komai ya daidaita za a jawo masu zuba jari, rage asara wanda hakan zai saukaka lamura.
Sai dai har yanzu, rashin aiwatar da tsarin cinikin danyen mai da Naira yadda ya kamata yana barazana ga tashin farashin man fetur, hakan zai iya kara haddasa karin farashi a nan gaba.
Dangote ya daina sayar da mai da Naira
A wani rahoton, kun ji cewa matatar Dangote ta yanke matsayar daina sayar da man fetur a Najeriya da Naira.
Rahotanni sun tabbatar da cewa matatar Dangote ta dauki matakin ne bayan dakatar da cikinin danyen mai da Naira tsakaninta da gwamnatin Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng