Bayan Kona 'Yan Arewa Kurmus a Edo, An Kashe Mutane 10 da ke Zaman Makoki a Filato
- ‘Yan bindiga sun kai mummunan hari a garin Ruwi, da ke Bokkos, Jihar Filato, suka kashe mutane 10 da ke zaman makokin mutuwa
- Gwamnatin Filato ta yi Allah wadai da harin, yayin da 'yan sanda suka tura karin jami'an tsaro zuwa Bakkos don wanzar da zaman lafiya
- Kisan mutanen a Filato na zuwa a dai dai lokacin da ake jimamin kisan wasu mafarauta ƴan Arewa a jihar Edo a hanyarsu ta zuwa gida
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Filato - Akalla mutane 10 suka mutu yayin da wasu uku suka jikkata a harin da ‘yan bindiga suka kai garin Ruwi da ke karamar hukumar Bokkos, jihar Filato.
Wani mazaunin yankin da bai so a ambaci sunansa ba ya ce ‘yan bindigar sun kutsa kauyen da misalin karfe 9:30 na daren ranar Alhamis.

Kara karanta wannan
"Ba yau aka fara ba," Gwamnatin Kano ta yi zazzafan martani kan kisan ƴan Arewa a Edo

Asali: Twitter
An kashe mutane 10 a sabon harin Filato
Majiyar da ta yi magana da jaridar Daily Trust ta ce maharan sun bude wuta kan mutanen da ke gudanar da taron makomkn wani da ya rasu a garin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Mutane 10 sun mutu, wasu uku kuma sun jikkata. Lallai wannan mummunan hari ne. Muna kira ga hukumomin tsaro da su dauki matakin gaggawa,” inji majiyar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Alabo Alfred, ya tabbatar da harin ga manema labarai a ranar Juma’a, amma bai bayyana adadin wadanda suka mutu ba.
Matakan da 'yan sandan Filato suka dauka
Ya ce rundunar ta jajantawa iyalan mamatan, tare da tabbatar da cewa an tura karin jami’ai domin dawo da doka da oda a yankin.
DSP Alfred ya kara da cewa kwamishinan ‘yan sandan jihar ya kai ziyara wurin da harin ya faru domin duba halin da ake ciki.
Dangane da matakan da aka dauka, DSP Alfred ya ce:
“Kwamishinan ‘yan sanda ya aika da karin jami’ai da kayan aiki daga hedkwatar jihar zuwa Bokkos da kewaye.
"Haka kuma ya umarci kwamandan yankin Pankshin da ya koma Bokkos domin kula da dukkan ayyukan tsaro har sai an tabbatar da zaman lafiya."
Ya kara da cewa rundunar na kokarin kama wadanda suka aikata wannan ta’asa domin su fuskanci hukunci.
Gwamnatin jihar Filato ta yi Allah wadai
A gefe guda, gwamnatin jihar Filato ta yi Allah wadai da harin, ta na mai bayyana shi a matsayin “kisan gilla ga fararen hula.”
Kwamishinar yada labarai da sadarwa ta jihar, Hon. Joyce Ramnap, ta jajanta wa iyalan mamatan tare da yin kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu.
Gwamnati ta tabbatar da cewa tana daukar matakan kawo karshen irin wadannan hare-hare a jihar.
An kona 'yan Arewa kurmus a Edo
A wani labarin, mun ruwaito cewa gungun fusatattun mutane a jihar Edo, sun tare wasu 'yan Arewa 16 da ke hanyar zuwa gida bikin Sallah, sun kone su kurmus.
An ce mazauna garin Udune Efandion, yankin Uromi a jihar Edo ne suka yi wannan aika-aika, saboda suna zargin matafiyan da zama masu garkuwa da mutane.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng