Gwamna Abba Ya Kaɗu bayan Rashin Fitaccen Jarumi da Masana'antar Kannywood Ta Yi

Gwamna Abba Ya Kaɗu bayan Rashin Fitaccen Jarumi da Masana'antar Kannywood Ta Yi

  • Abba Kabir Yusuf, ya nuna alhinin rasuwar fitaccen jarumin Kannywood, Abdullahi Shuaibu Karkuzu, wanda ya rasu ya na da shekara 94
  • Mai magana da yawun gwamna, Sanusi Bature, ya ce Karkuzu ya bar babban gibi a masana’antar, kasancewarsa gwarzo mai horar da matasa
  • Gwamna ya ce marigayin ya kasance jarumi mai iya sauyawa daga barkwanci zuwa wani rawar da ya ke yi da kwarewa
  • Ya yi addu’a ga Allah ya gafarta masa, ya ba shi hutun dawwama, tare da bai wa iyalai da masana’anta hakurin rashinsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya nuna alhinin rasuwar fitaccen jarumin Kannywood.

Gwamnan ya tura sakon ta'azziya ga iyalan marigayi Abdullahi Shuaibu, da aka fi sani da Baba Karkuzu.

Kara karanta wannan

Gwamnonin Arewa sun haɗa kai kan kisan Hausawa a Edo, sun shawarci al'umma

Gwamna Abba ya yi alhinin mutuwar jarumin Kannywood
Abba Kabir ya tura sakon ta'azziya ga iyalan marigayi Baba Karkuzu da ya rasu. Hoto: Abba Kabir Yusuf.
Asali: Facebook

Abba Kabir ya yi rashin hadiminsa na musamman

Wannan na kunshe a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamna, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne bayan miƙa sakon ta'azziya da Gwamna Abba Kabir ya yi na rashin hadiminsa na musamman a asibitin Kano.

Gwamna Abba Kabir ya shiga jimami ne bayan sanar da rasuwar Abdullahi Tanka Galadanci, babban mai taimaka masa kan Rediyo.

Mai magana da yawun gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya bayyana cewa Galadanci ya rasu bayan gajeruwar rashin lafiya a asibiti.

Gwamnan Kano ya bayyana marigayin a matsayin ginshiki a gwamnatinsa, ya na mai addu’ar Allah ya gafarta masa, ya kuma ba iyalansa hakuri.

Gwamna ya tura sakon ta'azziya ga iyalan Karkuzu
Abba Kabir ya bayyana rashin jarumin Kannywood, Karkuzu a matsayin wanda zai yi wahalar cikewa. Hoto: Sanusi Bature Dawakin-Tofa.
Asali: Facebook

Abba ya jajanta bayan rasuwar Baba Karkuzu

Sanarwar ta ce marigayin ya rasu ya na da shekaru 94 bayan jinya mai tsawo da ya yi fama da ita.

Kara karanta wannan

An shiga jimami a Kano: Babban mai taimaka wa Gwamna Abba ya rasu ana azumi

Gwamna Yusuf ya ce rasuwar Karkuzu babban rashi ne ga masana’antar fim da kuma daukacin al'umma baki daya.

Ya ce marigayin ya sadaukar da kansa ga sana’arsa tare da horar da matasa da ke tashe a masana’antar.

Abba Kabir ya fadi gudunmawar Karkuzu a fim

Sanarwar ta ce:

"Marigayin ya bar babban gibi da zai yi wahala a cike, domin ya nuna kwarewa ta musamman a tsawon lokaci a aikinsa.
"Iyawarsa ta sauya daga barkwanci zuwa rawar da ta fi tasiri da kwarewa wanda abin alfahari ne."

A madadin gwamnati da al’ummar Jihar Kano, Gwamna Yusuf ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, Kannywood, da dukkan masana’antar fim.

Daga karshe, gwamna Abba Kabir ya yi addu’a Allah ya gafarta masa, ya ba sanya shi a gidan aljannar Firdausi madaukakiya.

Allah ya karbi rayuwar 'dan Kannywood, Karkuzu

Kun ji cewa shahararren ɗan wasan kwaikwayo, Abdullahi Shuaibu wanda aka fi sani da Baba Karkuzu, ya rasu a ranar Talata, 25 ga Maris, 2025 da muke ciki.

Majiyoyi sun nuna cewa za an yi jana'izar marigayin a ranar Laraba, 26 ga Maris da safe a gidansa da ke layin Haruna Hadeja a garin Jos, Jihar Filato da ke Arewacin Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng