Gwamnonin Arewa Sun Haɗa Kai kan Kisan Hausawa a Edo, Sun Shawarci Al'umma
- Gwamnonin Arewa sun yi Allah-wadai da kisan matafiya a Edo, suna cewa wannan abin takaici ne da ya sabawa hakkin dan Adam
- Gwamna Inuwa Yahaya ya ce dole ne a binciki lamarin tare da hukunta masu laifi, domin hana irin haka faruwa a gaba
- Ya jaddada cewa kowane dan Najeriya na da ‘yancin tafiya ba tare da fargabar farmaki, barazana ko muzgunawa ba
- Ya bukaci gwamnati da jami’an tsaro su dauki matakin gaggawa don kare lafiyar matafiya da hana sake aukuwar irin wannan lamarin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Gombe - Gwamnonin jihohin Arewa sun yi magana kan kisan wulakanci da aka yi wa ƴan Arewa a jihar Edo.
Gwamnonin sun yi Allah-wadai da kisan matafiya daga Arewacin Najeriya a garin Udune Efandion da ke Uromi a jihar Edo.

Asali: Twitter
Rabiu Kwankwaso ya yi magana kan kisan Hausawa
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan yada labaran gwamna Inuwa Yahaya, Ismaila Uba Misilli ya wallafa a shafin Facebook a yau Juma'a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A bangarensa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi magana kan harin da aka kai wa ƴan Arewa a jihar Edo.
Kwankwaso ya yi Allah wadai da abin da ya faru inda ya bukaci jami'an tsaro su yi duk mai yiwuwa domin tabbatar da hukunta waɗanda suka aikata laifin.
Kisan Hausawa: Gwamnonin Arewa sun yi Allah-wadai
Sanarwar ta ce shugaban gwamnonin Arewa, Inuwa Yahaya, ya ce wannan hari ya saba wa hakkin dan Adam kuma ba za a yarda da shi ba.
Ya ce gwamnonin sun mika ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu da duk masu alhinin wannan mummunan al’amari.
Sanarwar ta ce:
“Mu na cikin damuwa matuka kan asarar rayuka da kuma yadda aka kai harin.
“Dole ne a gano wadanda suka aikata wannan aika-aika, a kama su, kuma a gurfanar da su gaban kuliya ba tare da bata lokaci ba."

Asali: UGC
Matakin da gwamnonin Arewa suke bukata
Sanarwar ta ce wannan danyen aiki yana barazana ga doka da oda, don haka dole ne hukumomi su gudanar da bincike mai zurfi don hukunta masu laifi.
Gwamna Yahaya ya ce dole ne kowane dan Najeriya ya sami ‘yancin tafiya cikin kwanciyar hankali ba tare da tsoro ko barazana ba.
Ya bukaci gwamnati da jami’an tsaro su dauki matakin gaggawa don hana sake faruwar irin wannan mummunan lamari.
Har ila yau, ya kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu yayin da ake cikin wannan hali na rashin tabbas.
Gwamnan Edo ya magantu kan kisan Hausawa
Mun ba ku labarin cewa Gwamna Monday Okpebholo ya yi Allah-wadai da kisan matafiya ƴan Arewa a garin Uromi da ke ƙaramar hukumar Esan a jihar Edo.
Gwamna Okpebholo ya ba da umarnin gudanar da bincike domin hukunta duk mai hannu a aikata wannan ɗanyen aiki.
Wannan na zuwa ne bayan wasu matasa sun ƙone Hausawa da ke hanyar dawowa gida domin shagalin ƙaramar sallah bisa zargin cewa masu garkuwa ne.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng