Najeriya Ta Yi Martani ga Amurka kan Zargin Kashe Kiristoci karkashin Tinubu
- Majalisar dokokin Amurka ta bukaci Shugaba Donald Trump ya kakabawa Najeriya takunkumi kan zargin kashe Kiristoci
- Lamarin ya ba gwamnatin Najeriya mamaki, inda ta bayyana cewa babu kamshin gaskiya a zargin cewa an saka Kiristoci a gaba
- Amurka ta samu bayananta ne daga wani Bishof a Binuwai, Wilfred Anagbe, wanda kungiyoyin Musulmi ke zargi da shirga karya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Kasar America – Majalisar dokoki ta Amurka ta bayar da shawara ga Shugaba Donald Trump da ya kakabawa Najeriya takunkumi mai tsauri kan zargin kashe Kiristoci a kasar.
Wannan matakin ya biyo bayan kudurin da Kwamitin harkokin waje na Majalisar Wakilai kan Afrika ya amince da shi, bayan zaman jin bahasi da aka yi a ranar Laraba, 12 ga Maris.

Asali: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa a yayin zaman jin bahasin, Shugaban Kwamitin, Dan Majalisa Chris Smith, ya jaddada bayanan da wani Bishop Wilfred Anagbe na wata coci a Binuwai ya gabatar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An ruwaito cewa Anagbe ya zargi Fulani makiyaya da laifuffukan satar mutane, kashe-kashe da garkuwa da jama'a, lamarin da ya tunzura 'yan majalisar.
Majalisar Amurka ta tattaro rahotonta
Kwamitin ya kuma ambaci wani rahoto na 2024 da Observatory for Religious Freedom in Africa ta fitar, wanda ya nuna cewa 90% na Kiristocin da ake kashewa a duniya kowace shekara 'yan Najeriya ne.

Asali: Facebook
Rahoton ya bayyana cewa, daga watan Oktoba 2019 zuwa Satumba 2023, akalla mutum 55,910 aka kashe, yayin da wasu 21,000 suka fada hannun 'yan ta'adda da ke aiki a yankin.
Smith ya dora alhakin hakan kan tsohon gwamnatin Joe Biden saboda cire sunan Najeriya daga jerin Kasashe masu matsala, wanda aka sanya a zangon farko na Shugaba Trump.

Kara karanta wannan
Za a share hawayen ƴan Najeriya, Majalisa ta ɗauki mataki kan tsadar datar MTN da Airtel
Najeriya ta yi martani ga majalisar Amurka
A martaninsa, Mai ba Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu shawara kan harkokin sadarwa, Daniel Bwala, ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu na kokarin tabbatar da zaman lafiya da juriya tsakanin addinai.
Bwala ya jaddada cewa tun bayan hawansa mulki a ranar 29 ga Mayu, 2023, gwamnatin ba ta samu rahoton wani fitaccen abu na muzgunawa Kiristoci ba.
Yayin da ya ke karyata zargin, Bwala ya kuma kalubalanci sahihanci da mahimmancin rahoton da kwamitin Majalisar Amurka ya gabatar.
Kungiyar Musulmi ta yi wa Amurka raddi
Majalisar koli ta shari'a a Najeriya (SCSN) da kimgiyar Muslim Public Affairs Centre (MPAC) sun caccaki Bishop Anagbe bisa abin da suka kira yada karya a ketare kan zargin kashe kiristoci da gayya.
A cikin wata sanarwa daban-daban da suka fitar, Sakatare Janar na SCSN, Dr. Nafiu Baba-Ahmad da Shugaban MPAC, Disu Kamor, sun bukaci gwamnatin tarayya ta binciki tare da hukunta Bishop Anagbe.
Sakatare Janar na SCSN, Dr. Baba-Ahmad, ya ce bayanan da limamin Katolika ya gabatar a gaban Majalisar Amurka, inda ya yada kalamai masu cike da kiyayya da karya.
Ya bayyana cewa hakan abin kunya ne ga gwamnatin Najeriya, kuma abin damuwa ga Musulmi da kiristocin Najeriya masu son zaman lafiya.
Dr. Baba-Ahmad ya ce ikirarin Bishop Anagbe na cewa 2% na Fulani (Musulmi) sun karbe yankunan da Kiristoci kashi 98% suka mamaye” ba gaskiya ba ne.
Najeriya na fuskantar barazana daga Amurka
A baya, mun wallafa cewa gwamnatin Amurka na shirin dakatar da bayar da tallafi ga GAVI, wata kungiya da ke samar da rigakafi ga kasashe masu tasowa, ciki har da Najeriya.
Wannan matakin na zuwa ne a sakamakon sabon rahoton da hukumar USAID ta fitar, wanda ya nuna cewa gwamnatin Shugaba Donald Trump tana shirin rage kudaden yaki da zazzabin cizon saura.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng