Kudirin Majalisa: Jihohin Najeriya 5 da Ake Shirin Kara wa Yawan Kananan Hukumomi
- Majalisar wakilai ta amince da kudirorin da ke neman kirkirar sabbin kananan hukumomi a jihohi biyar, ciki har da Abia, Delta da Zamfara
- Wadannan kudirori na bukatar amincewar majalisar dokoki, majalisun jihohi, da rattaba hannun shugaban kasa kafin su zama doka a hukumance
- Majalisar ta kuma amince da wasu kudirori da suka hada da kafa jami’ar harsunan Najeriya da kayyade wa’adin sauraron shari’a a kotuna
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Kudirorin gyaran kundin tsarin mulki da ke neman kirkirar sababbin kananan hukumomi a jihohi biyar sun wuce karatu na biyu a majalisar wakilai.
Kudiri na farko, wanda Benjamin Kalu, mataimakin kakakin majalisar wakilai, da wasu ‘yan majalisa shida suka dauki nauyi, ya na neman raba karamar hukumar Bende da ke jihar Abia zuwa biyu: Bende ta Arewa da Bende ta Kudu.

Asali: Facebook
Kudirorin kirkirar sababbin kananan hukumomi
Kudiri na biyu, wanda Francis Waive, shugaban kwamitin dokoki da harkokin majalisa ya dauki nauyi, yana neman kafa sabuwar karamar hukuma Ughievwen a jihar Delta, inji rahoton The Cable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kudiri na uku, wanda Paul Nnamchi, Chimaobi Atu, da Nnolim Nnaji suka dauki nauyi tare, yana neman kirkirar karin kananan hukumomi a jihar Enugu.
Kudiri na hudu, wanda Ikeagwuonu Ugochinyere ya dauki nauyi, yana bukatar kirkirar karamar hukumar Ideato ta Yamma daga karamar hukumar Ideato da ake da ita a yanzu a jihar Imo.
A jihar Zamfara, wani kudiri da Bello Shinkafi ya dauki nauyi ya nemi kirkirar karamar hukumar Moriki daga Zurmi da ake da ita a yau.
Wadannan kudirori, na bukatar samun amincewar majalisar wakilai da sanatoci, da amincewar kashi biyu cikin uku na majalisun jihohi kafin a tura su ga shugaban kasa don amincewa.
Wasu muhimman kudirori da aka amince da su

Kara karanta wannan
Jami'an tsaro sun cafke mataimakin shugaban ƙasa, sabon yaƙi na shirin ɓarkewa a Sudan
A ranar Laraba, majalisar ta amince da kudirin da ke neman tabbatar da yankunan cigaban birane 37 na jihar Legas a matsayin sahihan kananan hukumomi.
Haka nan, an amince da wasu kudirori da suka hada da na kayyade wa’adin sauraron shari’o’in farar hula da na laifuffuka a kotuna, da bayar da damar shigar da majalisar dokoki ta kasa cikin shirin rattaba hannu kan yarjeniyoyi.
Majalisar ta kuma amince da kudirin da ke neman sanya Hukumar kula da ayyukan majalisar tarayya da hukumar ta majalisar dokokin jihohi a matsayin hukumomi masu ‘yancin kansu.
An nemi gudanar da kidayar jama'a a shekaru 10

Asali: Facebook
Haka kuma, The Nation ta rahoto majalisar ta amince da kudirin da ke neman kafa jami’ar harsunan Najeriya a Aba, jihar Abia, domin bunkasa koyar da harsunan gida.
Wani kudiri da aka amince da shi ya bukaci a rika gudanar da ƙidayar yawan jama’a a duk bayan shekaru goma a Najeriya.
Wadannan kudirori, wanda Kalu da wasu ‘yan majalisa suka dauki nauyi, an gabatar da su a karatu na biyu ta hannun jagoran majalisa, Hon. Julius Ihonvbere.
Za a iya kara yawan kananan hukumomin Legas
Tun da fari, mun ruwaito cewa, majalisar wakilai ta amince da kudirin dokar da ke neman karin kananan hukumomin Lagos daga 20 zuwa 57.
Kudirin, wanda wasu ‘yan majalisa 22 suka dauki nauyi, na daga cikin kudirori 42 da suka samu amincewa a ranar Laraba.
Idan aka amince da kudirin gaba daya, yawan kananan hukumomin Najeriya zai karu daga 774 zuwa 811, inda Lagos za ta zama jiha mafi yawan kananan hukumomi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng