Gwamna Ya Yi Magana kan Zargin Boko Haram na shirin Kwace Garuruwa a Yobe

Gwamna Ya Yi Magana kan Zargin Boko Haram na shirin Kwace Garuruwa a Yobe

  • Gwamnatin jihar Yobe ta musanta cewa Boko Haram ta na yi wa mazauna Gujiba barazana tare da ba su wa’adin ficewa daga gidajensu
  • Mai ba Gwamna Shawara Kan Tsaro, Birgediya Janar Dahiru Abdulsalam (mai ritaya), ya tabbatar da babu wannan magana ko kadan
  • Ya bayar da tabbacin an sake duba fasalin tsaro a jihar, kuma ana aiki tukuru da hadin kan jami'an tsaro wajen tabbatar da zaman lafiya
  • Gwamnati ta bukaci iyaye su sanya ido kan ‘ya’yansu tare da hana su shiga halayen da ka iya haddasa matsala ana shirin bikin sallah

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar YobeGwamnatin jihar Yobe ta karyata jita-jitar da ake yadawa cewa kungiyar Boko Haram ta bai wa wasu al’ummomi a karamar hukumar Gujba wa’adin ficewa daga gidajensu.

Kara karanta wannan

Siyasar Rivers: Shugaban riko ya sauke dukkan mutanen da Fubara ya nada

Mai Ba Gwamna Shawara Kan Tsaro, Birgediya Janar Dahiru Abdulsalam (mai ritaya), ne ya yi wannan bayani a zaman majalisar tsaron jihar da Mataimakin Gwamna, Alhaji Idi Gubana, ya jagoranta.

Mai Mala
An ƙaryata barazanar Boko Haram a Yobe Hoto: Hon Mai Mala Buni
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Janar Abdulsalam ya tabbatar wa da mazauna yankin cewa babu wannan barazana, tare da bukatar su ci gaba da harkokinsu ba tare da fargaba ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin Yobe na aiki da jami'an tsaro

Jaridar Guardian ta ruwaito cewa gwamnatin Mai Mala Buni ta na aiki kafada da kafada da jami’an tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Birgediya Janar Dahiru Abdulsalam (mai ritaya) ya ce:

"Gwamnati tare da hadin gwiwar jami’an tsaro tana ci gaba da aiki tukuru domin kare al’ummomin jihar."
"Babu wata sahihiyar bayanan leken asiri da ke nuna cewa Boko Haram ta bai wa mazauna Gujba ko wani yanki na jihar wa’adin ficewa."

Tsaro: Gwamnatin Yobe ta yi shirin Sallah

Gwamnatin Yobe ta bukaci jama’a su kwantar da hankalinsu, domin an shirya tsaf wajen tabbatar da tsaro a lokacin bukukuwan Sallah Karama.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya yi buda biki da marayu, ya ɗauki alkawarin ba su aikin yi

Gwamna
Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni Hoto: Hon. Mai Mala Buni
Asali: Twitter

Abdulsalam ya ce:

"Mun sake duba tsarin tsaro a jihar kuma mun dauki matakan da suka dace domin tabbatar da gudanar da bukukuwan Sallah cikin kwanciyar hankali."
"Muna kira ga iyaye su kula da ‘ya’yansu tare da hana su shiga halayen da ka iya haddasa masu matsala."

Haka kuma, majalisar tsaron ta yaba wa sarakunan gargajiya da shugabannin al’umma kan rawar da suke takawa wajen warware rikice-rikice da karfafa zaman lafiya a jihar.

Bam ya tashi a jihar Yobe

A baya, mun kawo labarin cewa aƙalla mutane uku sun samu raunuka bayan fashewar wani bam da aka binne a ƙaramar hukumar Gujba ta jihar Yobe.

Fashewar ta auku ne lokacin da wani matashi mai shekaru 22 ya gano alburusai da harsasai guda huɗu na bindigar AK-47 yayin da yake nemo itacen girki a daji.

Sakataren ƙungiyar ‘yan gwan-gwan a yankin, Isyaku Dahiru, ya tabbatar da an kai waɗanda suka jikkata zuwa asibitin ƙwararru na jihar Yobe don ba su kula wa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng