Plateau: Gwamna Ya Kulla Yarjejeniya da Kasar Isra'ila, Ya Soki Kungiyar Hamas

Plateau: Gwamna Ya Kulla Yarjejeniya da Kasar Isra'ila, Ya Soki Kungiyar Hamas

  • Gwamnatin Plateau ta kulla yarjejeniya da Isra'ila kan aikin noma, fasaha da kiwon lafiya domin bunkasa tattalin arziki da inganta rayuwar al’umma
  • Gwamnatin ta ce Plateau na da kamanceceniya da Isra’ila wajen yanayi da ƙasa, inda za a yi amfani da fasahar ban ruwa don inganta amfanin gona
  • A bangaren kiwon lafiya, gwamnatin jihar za ta kafa kwalejin likitanci a Jami’ar Plateau tare da gina asibitoci masu inganci da hadin gwiwar Isra’ila
  • Caleb Mutfwang ya yi Allah-wadai da sace Isra’ilawa da Hamas ta yi, ya na mai cewa Filato za ta ci gaba da karɓar shawarwari domin inganta tsaro

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Jos, Plateau - Gwamnatin jihar Plateau ta sanar da kulla yarjejeniya da kasar Isra'ila domin inganta ɓangarori da dama.

Gwamna Caleb Mutfwang ya ce yarjejeniyar ta mayar da hankali kan noma, fasaha da kiwon lafiya muhimman fannoni da ke da matukar tasiri ga ci gabanmu.

Kara karanta wannan

Fubara: Gwamnonin PDP sun nufi kotun koli kan dokar ta baci a jihar Ribas

Gwamna ya nemi taimakon kasar Isra'ila
Gwamna Caleb Mutfwang ya kulla yarjejeniya domin bunkasa tattalin arzikin Plateau. Hoto: @CalebMutfwang.
Asali: Twitter

Gwamna Mutfwang ya fadi shirin alaka da Isra'ila

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da gwamnan ya wallafa a shafinsa na X a yau Laraba 26 ga watan Maris, 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutfwang ya ce Plateau za ta yi amfani da kwarewar Isra’ila wajen kiwon dabbobi da inganta harkar kiwo da sarrafa madara.

Ya ce:

"Ina mai farin cikin sanar da yarjejeniya ta musamman tsakanin Jihar Plateau da ƙasar Isra’ila, wadda za ta mayar da hankali kan noma, fasaha da kiwon lafiya, muhimman fannoni da ke da matukar tasiri ga ci gabanmu.

Sanarwar ta ce:

"Plateau na da kamanceceniya da Isra’ila ta fuskar yanayi da ƙasa, hakan na samar da damar haɗin gwiwa.
"Mu na da burin inganta noman zamani, magance matsalar ajiya da adana amfanin gona, tare da amfani da fasahar ban ruwa ta Isra’ila domin wadatar abinci, inganta rayuwar manoma da bunkasa tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Gwamnoni 35 sun yi matsaya kan dakatar da Fubara da Tinubu ya yi

"Za mu kuma yi amfani da kwarewar Isra’ila wajen kiwon dabbobi da inganta harkar kiwo da sarrafa madara."
Gwamna ya fadi alakar da suka kulla da Isra'ila
Gwamna Caleb Mutfwang ya kulla yarjejeniya da Isra'ila domin kawo sauyi a Plateau. Hoto: Caleb Mutfwang.
Asali: Facebook

Isra'ila: Sauran bangarori da yarjejeniyar ta shafa

A fannin kiwon lafiya, Gwamna Mutfwang ya ce suna aniyar kafa sashen likitanci a Jami’ar Jihar Plateau da ke Bokkos tare da habaka damar da za su samu wajen yawon bude ido na lafiya.

Ta hanyar kwarewar Isra’ila, ya ce za su gina manyan cibiyoyin lafiya masu inganci, domin mayar da Plateau cibiyar jinya ta zamani.

Ya kara cewa:

"A bangaren tsaro, ina Allah-wadai da sace Isra’ilawa da Hamas ta yi, domin mu ma mun san raɗaɗin rashin tsaro.
"Za mu ci gaba da neman haɗin gwiwa da kasashen duniya don inganta tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al’ummarmu."

Yadda Najeriya take taimakon Falasɗinawa

Kun ji cewa ministan harkokin kasar waje, Ambasada Yusuf Tuggar, ya fadi yadda Najeriya ta taka muhimmiyar rawa wurin ceto jarirai daga Gaza.

Ya ce Najeriya ta yi nasarar kwashe jariran zuwa asibitoci a Jordan, Masar, da hadaddiyar daular larabawa domin ceto su daga luguden Isra'ila.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng