'Ba Alfarma ba ce': Ana Zargin Pantami na Shirin Neman Mulki, Ya Yi Wa Shugabanni Nasiha

'Ba Alfarma ba ce': Ana Zargin Pantami na Shirin Neman Mulki, Ya Yi Wa Shugabanni Nasiha

  • Isa Ali Pantami ya gargadi shugabanni su tabbata sun yi adalci ga al'ummar da suke mulka, tun daga kansiloli har zuwa shugaban kasa
  • Malamin ya bukaci masu rike da iko su tausayawa jama'a saboda matsin rayuwa, yana mai cewa taimakon al'umma ba alfarma ba ne
  • Ya ce rashin tsaro da wahalar rayuwa ba su dace ba, musamman Arewa da ke da arzikin kasar noma amma mutane na fama da yunwa
  • Sheikh Pantami ya soki raba abinci ga talakawa, ya na mai cewa ya kamata a koyar da su dogaro da kai maimakon zaman bara

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami ya yi nasiha ga shugabanni musamman na siyasa a Najeriya.

Farfesa Isa Pantami ya ja kunnen yan siyasa da shugabanni kan tabbatar da adalci ga wadanda suke mulka a Najeriya.

Kara karanta wannan

Rundunar ƴan sanda ta yi magana kan shirin hawan sarakuna 2 a Kano

Pantami ya yi wa shugabanni nasiha kan mulki
Sheikh Isa Pantami ya shawarci shugabanni kan taimakon al'umma. Hoto: Prof. Isa Ali Pantami.
Asali: Facebook

Pantami ya shawarci shugabanni kan adalci

Shehin malamin ya bayyana haka a cikin wani faifan bidiyo da shafin Karatuttukan Malaman Musulunci ya wallafa a shafin Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Farfesa Pantami ya yi nasihar tun daga kan masu mukaman kansiloli da shugabannin kananan hukumomi da gwamnoni har shugaban kasa.

Malamin ya roki masu rike mudafun iko su duba yadda za su tausayawa al'umma saboda halin kunci da ake ciki.

Sheikh Pantami ya ce:

"Ina nasiha ga waɗanda ke da iko da kuma dukiyar al'umma ke hannunsu tun daga kansiloli zuwa ciyamomi har shugaban kasa.
"Don Allah a duba yadda za a na taimakon al'umma a rayuwa kuma taimakon ba alfarma aka yi musu ba.
"Ko a kundin tsarin mulki taimakon al'umma ba alfarma ba ne hakkinsu ne da suke da a matsayin yan kasa."

Farfesa Pantami ya ce ba al'umma tsaro da kuma walwala ba alfarma ba ce bin kundin tsarin mulkin kasa ne da kuma bin abin da Kur'ani ya ce.

Kara karanta wannan

Malamin Musulunci ya gano hanya, ya jagoranci 'yan PDP da APC zuwa SDP

Ya ce:

"Ba daidai ba ne yanzu a ce a Arewa muna da kasar noma da gonaki amma ana wawan abinci ana kokuwa.
"Duk shugaban da ya tausayawa talakawa Allah ya na saukaka masa haka duk wanda ya tsananta Allah yana tsananta masa."
Sheikh Pantami ya yi nasiha mai kama hankali ga shugabanni
Sheikh Isa Ali Pantami ya shawarci shugabanni kan tausayawa al'umma. Hoto: Prof. Isa Ali Pantami.
Asali: Facebook

Sheikh Isa Pantami ya fadi illar rabon abinci da ake yi

Sheikh Pantami ya shawarci shugabanni su rika taimakawa al'umma su dogara da kansu ka da ya kasance kullum suna cikin bara.

Malamin yake cewa tsarin raba abinci da ake yi ba zai yi dogon tasiri ba, ya ce ya kamata a gina al'umma ne domin dogaro da kansu.

Ya ce amfanin raba abincin kawai na lokaci kadan ne amma ba shi da wani tasiri a rayuwar mutum ta gaba.

Pantami ya fadi hanyar dakile ta'addanci a Najeriya

Kun ji cewa tsohon Ministan sadarwa a Najeriya, Farfesa Isa Pantami ya fadi dalilin ƙaruwar ta'addanci da garkuwa da mutane musamman a Arewacin kasar.

Kara karanta wannan

Barau: An saki adadi da bayanin tantance matasan da suka nemi tallafin Barau N5m

Pantami ya bayyana yadda ya yi nasarar hada layukan miliyoyin yan Najeriya da lambar NIN lokacin da ya ke ofis domin dakile garkuwa da mutane.

Sai dai malamin ya ce komai ya lalace tun bayan barinsa ofishin da kuma sauye-sauye da aka samu a sabuwar gwamnatin Bola Tinubu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng