Tauraruwar Man Dangote na Haska wa a Kasuwannin Kasashen Amurka da Turai

Tauraruwar Man Dangote na Haska wa a Kasuwannin Kasashen Amurka da Turai

  • Matatar man fetur ta Dangote ta samu nasara a kasuwannin duniya, inda ta tura jiragen ruwa guda shida na man jirgin sama zuwa Amurka
  • Duk da cewa Amurka tana ci gaba da kasancewa kasuwa mai muhimmanci ga matatar Dangote, ana ganin shirin fadada wa zuwa Turai
  • Masana tattalin arziki na ganin cewa shigowar matatar Dangote cikin kasuwannin duniya zai taimaka, sannan zai sauko da farashi
  • Ana samun wannan ci gaba ne bayan Najeriya ta kekashe kasa wajen kin kara wa'adin sayar wa da matatar danyen mai a farashin Naira

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Lagos - Matatar mai ta Dangote na ƙara shahara a kasuwannin duniya, ya fitar da man jirgin sama zuwa Amurka ya kai matsayi mafi girma cikin shekaru biyu a watan Maris.

Kara karanta wannan

Rundunar ƴan sanda ta yi magana kan shirin hawan sarakuna 2 a Kano

Tasirin matatar a kasuwar duniya na ƙaruwa bayan hukumomin Najeriya sun kasa cimma matsaya kan sayar da danyen mai da Naira, kamar yadda aka cimma a baya.

Matata
Kasuwar matatar Dangote ta bude a Turai Hoto: Dangote Industries
Asali: Facebook

Jaridar The Guardian ta ruwaito cewa duk da cewa Amurka na ci gaba da kasancewa muhimmiyar kasuwa ga matatar, yanzu ta na maida hankali kan kasuwannin Turai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matatar Dangote na kai kaya zuwa Amurka

Channels News ta ruwaito cewa matatar Dangote mai iya tace ganguna 650,000 a kowace rana ta riga ta tura jiragen ruwa guda shida dauke da ganguna miliyan 1.7 na man jirgin sama zuwa Amurka a wannan wata.

Yanzu haka kuma, ana sa ran wani jirgin ruwa mai suna, Hafnia Andromeda, zai isa tashar Everglades nan da ranar 29 ga Maris dauke da karin ganguna 348,000 na man jirgin sama.

Dangote
Shugaban rukunin kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote Hoto: Dangote Industries
Asali: Getty Images

Duk da ƙalubalen da matatar ke fuskanta a gida da kuma rashin tabbas a kasuwannin duniya, ana hasashen cewa za ta kasance mai samar da man jirgin sama ga Amurka a kai-a kai.

Kara karanta wannan

Nasarori 3 da Nyesom Wike ya samu a cikin kwanaki 3 a siyasar jam'iyyar PDP

Wannan ci gaba zai kasance ne a yayin da matatar Phillips 66 (PSX.N) da ke New Jersey ke shirin rufe wani sashe saboda gyara, kamar yadda fitaccen mai sharhi James Noel-Beswick, ya bayyana.

Matatar Dangote za ta habaka

Masana tattalin arziki na ganin cewa shigowar Dangote kasuwannin duniya zai kara bunkasa, kuma matatar ta riga ta kalubalanci matatun mai na Turai a fannin fitar da fetur.

Yayin da matatun mai na Turai ke fuskantar hauhawar farashin tace mai da karuwar gasa a tsakaninsu, shigowar Dangote a kasuwar na iya haifar da saukar farashi.

Matatar Dangote ta fuskanci cikas a Najeriya

A baya, kun samu labarin cewa matatar Aliko Dangote ta sanar da dakatar da sayar da kayayyakin man fetur da Naira na ɗan lokaci bayan an samu cikas a yarjejeniyarta da Najeriya.

A sanarwar da ta fitar, matatar ta bayyana cewa dalilin wannan mataki shi ne bambanci tsakanin kuɗin da ake samu da kuma kuɗin da ake amfani da shi wajen sayen danyen mai.

Matatar Dangote ta kuma bayyana cewa wannan matakin ya na daga cikin kokarinta na tabbatar da cewa kasuwannin mai na Najeriya suna samun daidaito a cikin farashin man fetur.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng