Rigimar Sarauta: Kalu Ya Hadu da Aminu Bayero a Taro, Ya Ƙi Kiransa da 'Sarkin Kano'
- Mataimakin kakakin majalisar wakilai, Benjamin Kalu, ya kauracewa ambaton Aminu Ado Bayero da "Sarkin Kano" a taron jami’ar Calabar
- Masana sun fassara hakan a matsayin wata alama da ke nuna tasirin rikicin masarautar Kano da kuma siyasar Najeriya baki daya
- Dr. Riyaudden Maitama ya ce lamarin ya na da nasaba da siyasa, inda ‘yan siyasa ke kokarin amfani da rikicin wajen cika burinsu na zabe
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Calabar - Rikicin sarautar Kano ya dauki sabon salo a ranar Juma’a, 21 ga Maris, yayin da mataimakin kakakin majalisar wakilai, Benjamin Kalu, ya hadu da Aminu Ado Bayero a Calabar.
A taron cika shekaru 50 da kafuwar jami'ar Calabar, Benjamin Kalu ya kauracewa kiran Alhaji Aminu Bayero da 'Sarkin Kano', lamarin da wani masani ya kira da "tasirin rikicin shiya."

Asali: Facebook
Benjamin Kalu ya ki kiran Aminu da 'Sarkin Kano'
Rahoton TVC News ya nuna cewa mataimakin kakakin majalisar yana daga cikin manyan baki da suka halarci bikin cika shekaru 50 da kuma yaye dalibai karo na 37 na hami’ar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A yayin da yake girmama fitattun baki, kamar shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, sai aka ji Benjamin Kalu ya kira sunan Alhaji Aminu Ado Bayero, ba tare da sanya masa sunan 'Sarkin Kano' ba.
Iyakar ta dai ya nuna basaraken shi ne mai kula da jami'ar da ke jihar Kuros Riba.
Wannan lamari, an ce ya ja hankalin mutane, kasancewar ana ci gaba da kai ruwa rana kan sahihin sarkin Kano tsakanin Aminu Bayero da Muhammadu Sanusi II.
Masu sharhi kan lamuran siyasa sun fassara matakin mataimakin kakakin majalisar a matsayin wata alama da ke da tasiri kan rikicin masarautar da kuma siyasar kasa baki daya.
Tsokacin masana kan haduwar Kalu da Aminu Ado
Da yake tsokaci ga jaridar Legit.ng, wani masanin siyasa, Dr. Riyaudden Zubairu Maitama daga sashen kimiyyar siyasa na jami’ar Bayero, Kano, ya bayyana cewa lamarin na da nasaba da manyan rikicin siyasa da ke faruwa a kasar.
Dr. Maitama ya ce rikicin sarautar Kano ya samo asali ne daga siyasa, inda ‘yan siyasa ke son amfani da tasirin gwamnatin tarayya a matsayin makami na cimma muradun su, musamman a zaben 2027.
“Akwai bayani a kundin tsarin mulki da ke fayyace cewa gwamna da majalisar dokokin jiha su ne ke da ikon tantance wanda zai zama sarki da kuma yadda za a nada shi.
"Amma abin da ya faru a Calabar ba wani abu ne mai tasiri sosai wajen yanke hukunci kan wanda zai ci gajiyar wannan takaddama ba.
- Dr. Maitama.
Ra'ayin masana kan matsayin Aminu ga tarayya
Masanin siyasar, ya kara da cewa:
“Abin da Kalu ya yi a Calabar ba ya wakiltar matsayin shugaban kasa ko gwamnatin Najeriya. Watakila ra’ayin mataimakin kakakin majalisar ne kawai, wanda ba lallai ba ne ya shafi yanke hukunci kan wanda zai zama sarki ko a’a.”
Sai dai Dr. Maitama ya jaddada cewa:
“A fuskar siyasa, wannan matakin na Kalu na da nauyi. Duk da cewa Aminu Ado Bayero na samun tagomashi daga gwamnatin tarayya, amma hakan ba shi ne ke ba da tabbaci cewa gwamnatin na goyon bayansa a matsayin Sarkin Kano ba."
Gidan talabijin na TVC, ya fitar da cikaken bidiyon abubuwan da suka faru a taron, har zuwa lokacin jawabin Benjamin Kalu.
Kalli bidiyon a nan kasa:
An tura shari'ar masarautar Kano zuwa Kotun Koli
A wani labarin, mun ruwaito cewa, kotun daukaka kara, ta tabbatar da cewa an mika shari'ar masarautar Kano zuwa ga Kotun Koli bisa ga bukatar gwamnatin Kano.
Gwamnatin jihar Kano ta mika takardar karar zuwa Kotun Koli, tana mai nuna cewa akwai kuskure a hukuncin da Mai shari'a Okon Abang na kotun daukaka kara ya yanke.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng