"Ta Kai Ƙorafi LPDC," Natasha Ta Sake Kinkimo Rigima, Ta Zargi Sanata da 'Rashin Ɗa'a'
- Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da aka dakatar ta kai ƙorafin shugaban kwamitin ladabtarwa na Majalisar Dattawa gaban LPDC
- Natasha ya fallasa yadda kotun Amurka ta kwace masa lasisi saboda rashin gaskiya, damfara da rashin biyayya da ɗa'a ga hukumomi
- Ta ce sake nuna rashin ɗa'arsa yayin da ya yi kunnen uwar shegu da umarnin kotu da ya hana ɗaukar mataki kanta a Majalisa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Yayin da ake zargin mutanen mazaɓar Kogi ta Tsakiya na ƙoƙarin mata kiranye, Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta taso shugaban kwamitin ladabtarwa na Majalisar Dattawa.
Sanata Natasha ta shigar da ƙorafin shugaban kwamitin, Sanata Nedamwem Imasuen (LP, Edo ta Kudu) gaban kwamitin ladabtar da lauyoyi watau LPDC.

Source: Facebook
Jaridar Leadership ta tattaro cewa dakatacciyar sanatar ta buƙaci kwamitin LPDC ya tsige Sanata Imasuen daga matsayin lauya a Najeriya.

Kara karanta wannan
Natasha: Fada ya barke a majalisa, an yi kaca kaca tsakanin sanata da tsohuwar minista
Imasuen shi ne ya jagoranci Kwamitin ladabtarwa, wanda ya ba da shawarar hukunta Natasha bisa abin da aka bayyana a matsayin rashin ɗa'a a yayin zaman majalisa.
Natasha ta zargi Imasuen da rashin ɗa'a
A cikin ƙorafin da ta shigar, Natasha ta yi ikirarin cewa Kotun Ƙoli ta New York a Amurka, ranar 10 ga Mayu, 2010, ta tuhumi Imasuen tare da yanke masa hukuncin ƙwace lasisin aikin lauyansa.
Kotun ta masa wannan hukunci ne bisa zargin "damfara, karkatar da kuɗaɗen abokan ciniki da rashin amsa gayyyatar hukumomin ladabtarwa."
Don tabbatar da zargin na ta, Natasha ta gabatar da kwafin hukuncin 2010 mai taken "Batun Imasuen" daga Justia New York Case Law ga LPDC.
Ta kuma yi alkawarin gabatar da ƙarin hujjoji daga takardun hukuma na korarsa daga aikin lauya yayin sauraron ƙarar, rahoton Vanguard.
Yadda aka soke lasisin Imasuen a Amurka
A cewar Natasha, an soke lasisin Imasuen na aikin lauya a Amurka ne biyo bayan ƙorafin da wata abokiyar cinikinsa mai suna Daphne Slyfield, ta shigar, inda ta ce ta ɓiya kudin aiki amma ya yaudare ta.

Kara karanta wannan
Rikicin Ribas: Atiku Abubakar ya fusata, ya tona cin hancin da ake tafkawa a Majalisa
“Kotun ta gano cewa wanda ake tuhuma ya karya dokoki da dama na aikin lauya, abin da ya kai ga ta yanke hukunci haramta masa aikin lauya a Amurka.
“Bayan korarsa, ya dawo Najeriya, inda ya ci gaba da gabatar da kansa a matsayin lauya sannan ya shiga harkokin siyasa har ya zama Sanata mai wakiltar Edo ta Kudu."
“Koda yake an kore shi bisa rashin ɗa'a, bai bayyana wannan batu ba, ko a fannin aikin lauya ko siyasa. Haka kuma, bai bayyana hakan a cikin fom EC9 na INEC ba, wanda ke ƙunshe da bayanan sirri na masu neman mukamin siyasa,"
- In ji Natasha.

Source: Facebook
Dalilin kai wannan ƙorafi gaban LPDC
Sanata Natasha ta bayyana cewa ta miƙa wannan ƙorafi ga LPDC ne biyo bayan wasu abubuwan da suka jefa tambayoyi kan gaskiya da ɗa’ar Imasuen.
Ta yi zargin cewa Sanata Imasuen ya yi watsi da umarnin Kotun Tarayya da ke Abuja a ranar 4 ga Maris, wanda ya hana kwamitinsa ci gaba da bincike kanta.
A cewarta, duk da an sanar da shi umarnin da kotu ta bayar, ya yi kunnen uwar shegu, har ya ba da shawarar dakatar da ita na tsawon watanni shida.

Kara karanta wannan
Lauyan Natasha ya cire tsoro, ya fadi masu son ganin an kwace kujerarta a majalisa
Alkali ta tsame hannu daga shari'ar Natasha
A wani labarin, kun ji cewa alkalin babbar kotun tarayya da ka ɗorawa alhakin sauraron karar Sanata Natasha da shugaban Majalisar Dattawa ya janye kansa.
Alkalin ya dauki wannan matakin ne a zaman kotu na ranar Talata, bayan da Akpabio, ya shigar da koke yana kalubalantar adalcinsa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng