"Abin Ya Zo kan Zamfara": An Nemi Shugaba Tinubu Ya Sa Dokar Ta Ɓaci saboda Abubuwa 3

"Abin Ya Zo kan Zamfara": An Nemi Shugaba Tinubu Ya Sa Dokar Ta Ɓaci saboda Abubuwa 3

  • Yayin da ake ta surutu kan abin da ya faru a Ribas, ƙungiyar CDD ta bukaci Bola Tinubu ya sa dokar ta ɓaci a jihar Zamfara
  • Ƙungiyar mai rajin tabbatar da shugabanci na gari ta ce gwamnatin jihar Zamfara ta aikata laifukan da suka karya dokar kasa
  • Daga cikin laifuffukan da kungiyar ta lissafo akwai batun dakatar da ƴan Majalisar Dokokin Zamfara kan nuna ɓacin ransu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Zamfara - Wata kungiya mai rajin tabbatar da shugabanci nagari (CDD), ta bukaci Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu da ya ayyana dokar ta-baci na tsawon watanni shida a Jihar Zamfara.

Kungiyar ta bayyana wannan bukata ne yayin wani taron manema labarai da ta gudanar a birnin Abuja a ranar Litinin, 24 ga watan Maria, 2025.

Dauda Lawal.
Kungiyar CDD ta bukaci Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci na watanni 6 a jihar Zamfara Hoto: Dauda Lawal
Asali: Facebook

CDD ta bayyana damuwa kan yadda matsalolin tsaro da na tattalin arziki suka ƙara ta'azzara a jihar Zamfara da ke Arewa maso Yamma, Vanguard ta tattaro.

Kara karanta wannan

"Tinubu ya saba da tsarin jari hujja," NNPP ta haramta dokar ta ɓacin Ribas

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilan bukatar dokar ta-ɓaci a Zamfara

Shugaban kungiyar, Ibrahim Yakubu, ya bayyana cewa wasu matakai da Gwamnatin Zamfara ke dauka na barazana ga dimokuradiyya da zaman lafiya a jihar.

Daga cikin matsalolin da kungiyar ta lissafo akwai dakatar da ƴan Majalisar Dokoki, taɓarɓarewar tsaro, da haƙar ma'adanai ba bisa ƙa'ida ba.

Zamfara: CDD ta jero dalilan sa dokar ta-ɓaci

Kungiyar ta nuna damuwa kan dakatar da mambobi 10 na Majalisar Dokokin Jihar Zamfara har na tsawon watanni 13 saboda sun nuna ɓacin ransu kan taɓarɓarewar tsaro a Zamfara.

Haka nan CDD ta ce bayan haka an sake dakatar da wasu ƴan Majalisa takwas da suka nuna damuwa kan yadda ake tafiyar da mulkin Zamfara.

Dangane da batun matsalar tsaro, ƙungiyar ta yi zargin cewa matakan gwamnatin Dauda Lawal na PDP sun kara lalata harkar tsaro a jihar.

CDD ta kuma bayyana cewa ana zargin cewa ana gudanar da hakar zinare da sauran ma’adanai ba bisa doka ba, lamarin da ke barazana ga tattalin arzikin jihar.

Kara karanta wannan

Gwamnoni 35 sun yi matsaya kan dakatar da Fubara da Tinubu ya yi

Shugaba Tinubu.
CDC ta bukaci gwamnatin tarayya ta waiwayi abubuwan da ke faruwa a Zamfara Hoto: @aonanuga1956
Asali: Twitter

An bukaci Gwamnatin Tinubu ta ɗauki mataki

Kungiyar ta ce Gwamnatin Tarayya na da hakkin daukar matakan gaggawa don dawo da doka da oda a Zamfara.

A cewar Yakubu:

"Dakatar da 'yan majalisar jihar saboda sun nuna damuwa kan matsalar tsaro ya hana al'ummar Zamfara wakilci mai inganci. Wannan na nufin an rage karfin dimokuradiyya."
"Muna ganin ya kamata a sa dokar ta-baci na watanni shida domin dawo da doka da oda, da kuma tabbatar da cewa tsarin mulki yana aiki yadda ya kamata."

Kungiyar ta bukaci gwamnatin tarayya da ta dauki matakan da suka dace domin tsare albarkatun ƙasa da ke Zamfara, kare rayuka da dukiyoyin jama’a, da tabbatar da cewa tsarin mulki yana aiki yadda ya kamata.

Gwamna Alia ya yi watsi da dokar ta ɓaci

A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Hyacinth Alia ya yi fatalo da kiran wata ƙungiya, ya ce ba dalilin da zai sa a ayyama dokar ta ɓaci a jihar Benuwai.

Alia ya jaddada cewa shi ke da cikakken iko a jihar Benuwai kuma babu wata matsala da ta kai girman da za a sanya wannan doka.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel