Tinubu na cikin Aso Rock: Malamai Sun Rufe Makarantun Abuja, An Fara Yajin Aiki

Tinubu na cikin Aso Rock: Malamai Sun Rufe Makarantun Abuja, An Fara Yajin Aiki

  • Malaman firamare a Abuja sun sake tsunduma yajin aiki karo na hudu cikin watanni hudu, lamarin da ya hana ɗalibai zana jarabawa
  • Malaman sun ce shugabannin ƙananan hukumomi shida sun gaza biyan sabon albashi na N70,000, duk da alkawarin da suka ɗauka
  • Sun bukaci a cika musu hakkinsu domin su koma bakin aiki, suka nuna damuwa kan illar yajin aikin ga ci gaban ilimi a birnin tarayya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Malaman makarantun firamaren gwamnati na Abuja sun sake shiga yajin aiki karo na hudu cikin watanni hudu, lamarin da ya shafi jarabawar zango na biyu.

A baya, malaman sun tsunduma yajin aiki sau biyu a watan Disambar 2023 da kuma sau ɗaya a Fabrairun 2024 saboda matsalar albashi.

Malamai sun magantu da suka sake tsunduma yajin aiki a birnin tarayya Abuja
Malamai sun rufe makarantun firamare na birnin tarayya Abuja. Hoto: Olukayode Jaiyeola/Pius Utomi Ekpei
Asali: Getty Images

Malaman na adawa da kin biyan sabon albashi na N70,000, wanda suka ce shugabannin ƙananan hukumomi shida sun kasa aiwatarwa, inji rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Tankar mai ta sake fashewa a Neja, hukumomi sun tashi tsaye

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malamai sun tsunduma yajin aiki a Abuja

A ranar Litinin, manema labarai sun ziyarci wasu makarantu na LEA a yankunan Abuja, inda suka tarar da wasu makarantu a rufe yayin da ɗalibai ke komawa gida.

A makarantar firamare ta Pilot Science da ke Abaji, an ga wasu ɗalibai suna buga ƙwallo a cikin harabar makarantar, yayin da wasu ke komawa gidajensu.

Wasu malama da aka gani zaune a ƙarƙashin bishiyar mangwaro suna tattauna batun, sun ce shugabannin ƙananan hukumomi sun ƙi cika alkawarin da suka ɗauka.

Wani malami, Muazu Ibrahim, ya ce rashin biyan sabon albashin abin takaici ne, ya na mai cewa lamarin ya tilasta shiga yajin aiki, tare da jefa ɗalibai da iyaye a damuwa.

An rufe aji a Abuja, dalibai sun koma wasa

A makarantar Central Primary da ke Kwali, an tarar da azuzuwa a rufe, inda aka ga wasu ‘yan makaranta kalilansuna yawo a cikin harabar makarantar.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari a Abuja, sun yi awon gaba da babbar soja da wasu mutane

Wani malami, Barnabas Ayuba, ya bayyana cewa shugabannin ƙananan hukumomi na ƙara gurgunta harkar ilimi ta hanyar rashin kulawa da buƙatun malaman firamare.

Haka nan a makarantar LEA da ke Tukpechi, Kuje, an tarar babu kowa a aji sakamakon yajin aikin da malaman suka tsunduma.

A makarantar Demonstration LEA da ke Gwagwalada kuwa, wata tawagar malamai aka hango suna tattauna batun yajin aikin, yayin da wasu ɗalibai ke wasa.

Malamai sun fadi sharadin janye yajin aiki

An rufe makarantun firamare a Abuja saboda shiga yajin aikin malamai
Dalibai sun koma gidajensun da aka rufe makarantun firamare a Abuja. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Shugaban makarantar, Ibrahim Yusuf, ya nuna damuwa kan yadda jarabawar zango na biyu ke fuskantar cikas saboda rashin aiwatar da sabon albashin.

Malaman sun ce ba su da wata mafita illa ci gaba da yajin aiki har sai an aiwatar da sabon albashin don tabbatar da ingantacciyar rayuwa ga su da iyalansu.

Malaman sun roƙi shugabannin ƙananan hukumomin Abuja da su cika alkawarin da suka dauka, domin gujewa ci gaba da tabarbarewar ilimi a yankin.

Kara karanta wannan

Barau na kara barazana ga Abba a Kano, 'yan fim din Dadinkowa sun goyi bayansa

Kungiyar NUT ta shiga yajin aiki a Ebonyi

A wani labarin, mun ruwaito cewa malaman makarantun firamare a kananan hukumomi bakwai na Ebonyi sun tsunduma yajin aiki saboda kin biyan su albashi.

Kungiyar NUT ta ce yajin aikin zai ci gaba har sai shugabannin kananan hukumomi sun biya musu albashin watanni uku da ake bin su.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng