Da duminsa: An garkame makarantun firamare a Abuja kan yajin aikin malamai

Da duminsa: An garkame makarantun firamare a Abuja kan yajin aikin malamai

  • Malaman makaratun firamaren gwamnati na karamar hukumar Bwari dake Abuja sun fada yajin aiki
  • Malaman sun shiga yajin aikin ne bayan gwamnati tayi mirsisi ta ki biyansu albashinsu na watan Yuni
  • An gano cewa dukkan daliban da suka fita makaranta a yankin a ranar Laraba sun koma gidajensu

Bwari, Abuja

Malaman makarantun firamare na gwamnati a karamar hukumar Bwari dake Abuja sun fara yajin aiki kan tsaikon da aka samu na biyansu albashin watan Yuni.

An fara yajin aikin ana sauran kwanaki biyu jarabawar zangon karatu na uku na wannan shekarar a babban birnin tarayyan, Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA: An mayar da ministan Buhari da ta yanke jiki ta fadi zuwa dakin asibiti

Da duminsa: An garkame makarantun firamare a Abuja kan yajin aikin malamai
Da duminsa: An garkame makarantun firamare a Abuja kan yajin aikin malamai. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Ku gaggauta ceto dukkan dalibai da aka sace, Buhari ga hukumomin tsaro

'Yan makaranta sun koma gida

Yaran da suka bar gida domin zuwa makarantunsu a safiyar Laraba duk sun koma gidajensu.

Wata malamar makaranta dake Kubwa da ta bukaci a boye sunanta ta sanar da Daily Trust cewa kungiyar malamai ta kasa reshen karamar hukumarsu ta bada takarda inda take sanar da cewa za ta fara yajin aikin a ranar Talata.

Wata malamar makaranta ta ce daga cikin kananan hukumomi shida na babban birnin tarayya, Bwari ne kadai ba a biya albashin malamai ba a watan Yuni.

Malamar ta kara da cewa dukkan kokarin da NUT ta dinga yi na ganin an biya su albashinsu, abun ya gagara.

Za a fara biyan albashin daga karfe 10 na safe

A lokacin da aka tuntubi mataimakin shugaban karamar hukumar Bwari, Aminu Musa, ya ce suna shiri kuma zasu saki albashin kafin karfe 10 na safiyar Laraba.

A wani labari na daban, 'yan daba wadanda aka fi sani da Area Boys a jihar Legas suna musayar wuta da jami'an tsaron hadin guiwa a Apapa dake jihar Legas a halin yanzu.

Jami'an tsaron hadin guiwar sun hada da 'yan sanda, jami'an hukumar kula da cunkoson tituna na jihar Legas da sojoji.

Ganau sun ce jami'an tsaron hadin guiwar sun isa get na farko na Tin-Can dake Mile 2 babbar hanyar Apapa domin fatattakar bata-garin da ake zargi da aikata laifuka a yankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: