Ribas: Jami'in Gwamnati Ya ki yin Aiki da Soja, Ya Aikawa Shugaban Riko Murabus
- Shugaban riko na jihar Ribas, Ibok-Ete Ibas, ya naɗa Farfesa Ibibia Lucky Worika a matsayin Sakataren Gwamnatin Jihar
- Ibok-Ete Ibas ya kuma sanar da murabus ɗin Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar, George Nwaeke a wata sanarwa
- A halin yanzu, Dr Iyingi Brown za ta riƙe muƙamin Shugaban Ma’aikata na riƙo har sai an naɗa sabon shugaba a Ribas
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Rivers - Shugaban riko na jihar Ribas, Ibok-Ete Ibas (mai ritaya), ya sanar da naɗin Farfesa Ibibia Lucky Worika a matsayin sabon Sakataren Gwamnatin Jihar (SSG).
Rahotanni sun nuna cewa naɗin ya biyo bayan nazari kan ƙwarewar Farfesan da gogewarsa a fannoni daban-daban.

Asali: Facebook
The Cable ta wallafa cewa Ibas ya amince da murabus ɗin Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar, George Nwaeke, yana mai gode masa bisa gudunmawar da ya bayar a lokacinsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Legit ta ruwaito cewa Ibas ya hau karagar mulki ne bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya naɗa shi a matsayin shugaban Ribas bayan ayyana dokar ta-ɓaci a jihar.
Dalilin naɗin Farfesa Ibibia Worika
A wata sanarwa da ofishin shugaban rikon ya fitar, an bayyana cewa an zaɓi Farfesa Worika ne bisa cancanta da ƙwarewarsa a fannoni daban-daban.
Sanarwar ta bayyana cewa:
“Ya mallaki digirin digirgir a fannin Muhalli da Man Fetur daga Jami’ar Dundee da ke Birtaniya,
Kuma ya na da gagarumar ƙwarewa a harkokin mulki, ƙungiyoyin duniya da harkokin ilimi.”
Ibas ya ce naɗin Farfesa Worika ya yi daidai da manufofin sa na amfani da ƙwararru daga jihar Ribas domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Murabus ɗin Nwaeke da sabon sauyi a Rivers
Baya ga naɗin sabon SSG, Ibas ya amince da murabus ɗin George Nwaeke daga matsayin Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar Ribas.
A cewar sanarwar:
“Mai Ggrma Shugaban Riko ya gode masa bisa gudunmawar da ya bayar a ɗan gajeren lokacin da ya yi a ofis. Muna masa fatan alheri a gaba.”
A halin yanzu, an naɗa Dr Iyingi Brown, Babbar Sakatare a Ofishin Shugaban Ma’aikata, a matsayin mai riƙon muƙamin har sai an naɗa sabon shugaba.

Asali: Instagram
Ibas ya jaddada manufarsa a Rivers
Shugaban riko na jihar, Ibas, ya jaddada aniyarsa ta tabbatar da adalci da zaman lafiya a jihar Ribas.
Punch ta wallafa cewa ya ce:
“Gwamnatina za ta ci gaba da aiki don tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar Ribas. Saboda haka, ina roƙon haɗin kan al’umma domin cimma wannan buri.”
Tun bayan hawan Ibas kan mulki a matsayin shugaban riko, ana ci gaba da fuskantar sauye-sauye a gwamnatin jihar Ribas domin tabbatar da tsaro da ci gaba.
An fara neman sulhu a jihar Rivers
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnonin Kudu maso Kudu sun fara magana kan yin sulhu bayan dakatar da gwamna Simi Fubara na jihar Rivers.
Gwamnonin yankin sun bukaci amfani da hanyar sulhu domin kawo karshen rikicin da kawo zaman lafiya mai dorewa a jihar.
Asali: Legit.ng