Baffan Sarki Ya Samu Babban Matsayi, An ba Shi a Sarauta Mai Daraja a Gombe

Baffan Sarki Ya Samu Babban Matsayi, An ba Shi a Sarauta Mai Daraja a Gombe

  • Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya ya naɗa Baffan sarki, Alhaji Bappah Ibrah Mohammed a matsayin sabon hakimin Gombe
  • Mataimakin gwamnan jihar Gombe, Dr. Manassah Daniel Jatau, shi ne ya jagoranci tawaga da ta ba sabon hakimin takardar naɗi
  • Alhaji Bappah Ibrahim Mohammed ya miƙa godiyarsa ga Gwamna Inuwa Yahaya bisa wannan babbar amanar da aka ɗora masa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Gombe - Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya naɗa Alhaji Bappah Ibrahim Mohammed a matsayin sabon hakimin Gombe a ƙarƙashin Majalisar Masarautar Gombe.

Wannan naɗi ya biyo bayan rasuwar tsohon Hakimin Gombe na baya, Alhaji Abdulkadir Abubakar, wanda ya rasu a watan Agustan 2023.

Muhammad Inuwa Yahaya.
Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya ya naɗa sabon Hakimin Gombe Hoto: Muhammad Inuwa Yahaya
Asali: Facebook

Alhaji Bappah Ibrahim Mohammed gogaggen shugaba ne da ke da dogon tarihi a harkokin mulki da gudanar da al’amuran masarauta, kamar yadda Daily Trust ta kawo.

Kara karanta wannan

Kaduna: Sarki ya samu shirgegen muƙamin gwamnati, Gwamna Uba Sani ya taya shi murna

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

KawunSsarki ya samu babbar sarauta

Ya kasance ɗan marigayi Sarkin Gombe, Umaru Mohammed Kwairanga, kuma baffa ga Sarkin Gombe na yanzu, Alhaji Abubakar Shehu Abubakar III.

Kafin naɗinsa, Alhaji Bappah ya shafe shekaru 23 ya na rike da sarautar Hakimin Jalo Waziri, matsayi da ya ba shi gogewa sosai wajen tafiyar da al’amuran al’umma da masarauta.

Haka kuma, ya yi ritaya daga matsayin daraktan harkokin gudanarwa da kudi a Majalisar Dokokin Jihar Gombe, inda ya bayar da gagarumar gudunmawa a fannoni da dama na ci gaba.

Gwamnatin Gombe ta ba shi takardar naɗi

A yayin mika takardar naɗin, mataimakin gwamna, Dr. Manassah Daniel Jatau, ya bukaci sabon hakimin da ya rungumi adalci, zaman lafiya, da kuma kare jama'arsa.

Ya ce gwamnati na fatan sabon Hakimin zai ci gaba da aiwatar da manufofin da za su kara haɗin kai da ci gaban masarautar Gombe, tare da tabbatar da zaman lafiya a yankin.

Kara karanta wannan

'Dan shugaban ƙasa, Seyi Tinubu ya gamu da fushin matasa, an dakawa motar tallafinsa wawa

Alhaji Bappah Ibrahim Mohammed.
Gwamna Inuwa Yahaya ya naɗa sabon hakimin Gombe Hoto: Hassan Mazadu Gombe
Asali: Facebook

Bayan karɓar takardar naɗin, Alhaji Bappah Ibrahim Mohammed ya bayyana godiyarsa ga Gwamna Inuwa Yahaya bisa wannan babbar amanar da aka ɗora masa.

Ya jaddada cewa zai yi aiki tukuru don inganta rayuwar al’ummar Gombe, tare da bayar da gudunmawa domin ci gaban masarauta da jihar gaba ɗaya.

Tawagar da suka raka mataimakin gwamna

Manyan mutanen da suka raka mataimakin gwamna zuwa wurin mika takardar naɗin sabon hakimin sun haɗa da shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin Gombe, Abubakar Inuwa Kari.

Sauran su ne kwamishinan ƙananan hukumomi, Alhaji Abdulkadir Mohammed Waziri da daraktan kula da harkoki na musamman, Alhaji Bala Sarki.

Naɗin Alhaji Bappah Ibrahim a matsayin Sabon Hakimin Gombe na da matukar muhimmanci, domin kuwa zai taimaka wajen daidaita harkokin masarauta, kyautata zamantakewa, da kuma ci gaban tattalin arziki.

Gwamnatin Gombe da al’ummar jihar na fatan sabon Hakimin zai yi aiki tukuru wajen tabbatar da zaman lafiya.

Gwamnan Gombe ya samu lambar yabo

Kara karanta wannan

Tinubu ya kadu kan rasuwar mahaifiyar Gwamna Radda, ya tura sako mai muhimmanci

A baya kuma ji cewa Malaman Tsangaya sun yaba da hidimar da Gwamna Inuwa Yahaya yake yi wajen inganta harkokin koyo da haddar Alƙur'ani a Gombe.

Malaman sun bai wa gwamnan lambar yabo ta, "Khadimul Ƙur'an," yayin da suka halarci taron buɗa baki a fadar gwamnatin Gombe.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng