Ana tsakiyar Rikicin Rivers, Obasanjo, Atiku da Kusoshin Najeriya Sun Dura Abuja
- Tsohon shugaba, Olusegun Obasanjo, ya jagoranci taron taya murnar cika shekaru 60 na tsohon gwamnan jihar Imo, Emeka Ihedioha, a Abuja
- Manyan bakin da suka halarci taron akwai Emeka Anyaoku, Atiku Abubakar, Peter Obi, Aminu Tambuwal, Aminu Bello Masari da sauransu
- Bishop Matthew Kukah na cocin Katolika ya gabatar da jawabi na musamman mai taken “Shin Dimokuraɗiyya na kara tabarbarewa a Afirka?”
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya jagoranci taron taya murnar cika shekaru 60 na tsohon gwamnan jihar Imo, Emeka Ihedioha, a Abuja.
An gudanar da taron a dakin taro na Ladi Kwali da ke otel din kasa da kasa na Abuja, inda manyan baki suka hallara domin taya Emeka murnar zagayowar ranar haihuwarsa.

Asali: Twitter
Atiku, Obasanjo, Tambuwal, Obi sun dura Abuja
Bishop Matthew Kukah na cocin Katolikar Sokoto ne ya gabatar da jawabi na musamman mai taken “Shin dimokuraɗiyya na tabarbarewa ne a Afirka?," inji rahoton Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Cikin manyan baki da suka halarta akwai tsohon sakataren kungiyar Commonwealth, Emeka Anyaoku, da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar.
Sauran sun hada da tsohon dan takarar shugaban kasa, Peter Obi, tsohon gwamnan Sokoto, Aminu Tambuwal, da tsohon gwamnan Katsina, Aminu Masari.
Atiku ya fadi alakarsa da tsohon gwamnan Imo
Atiku ya jinjinawa Ihedioha, yana mai cewa ya kasance mutum mai aminci da gaskiya duk da cewa a wasu lokuta, sukan tsinci kansu a jam’iyyu daban-daban.
A cewar Atiku:
"Akwai babbar dangantaka tsakanina da Emeka, kuma har gobe ina kallonsa a matsayin mutum mai amana, wanda ya kasance mai jajircewa kan abin da ya sanya a gaba.
"A wasu lokutan, mukan tsinci kawunanmu a bangarori daban-daban na siyasa, amma duk da wannan bambancin, alakarmu na nan daram, kuma zan shaidi Emeka a kowane lokaci."

Kara karanta wannan
Gudaji Kazaure: Babban jigo a APC ya gana da Atiku, ya fadi shirin kifar da Tinubu
Atiku ya magantu kan goman karshe na Ramadan
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya kara da cewa ya kusan kin halartar taron saboda azumin Ramadan, amma Ihedioha ya dage sai ya halarta.
Atiku Abubakar ya ci gaba da cewa:
"A lokacin da ya sanar da ni wannan taron, har na fara korafi, na fada masa cewa, 'Emeka, yanzu fa watan azumin Ramadan ne.
"Yanzu muna cikin kwana 10 na karshen Ramadan. A kwanaki 10 na karshen Ramadan, ba mu barci da daddare, muna barci ne kawai da rana.
"Amma ya ce mun, 'haba oga na, ka yi kokari ka halarta.' Sai na ce masa, 'Shi kenan, zan halarta.' Yanzu ga shi Allah ya kawo mun wannan waje."
Za a kammala bikin da liyafar cin abinci da za a gudanar da yammacin ranar Litinin.
Tsohon hadimin Atiku ta fuskar kafofin sada zumunta, Paul Ibe, ya tabbatar da halartar uban gidan nasa a wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X.
Duba sanarwar a nan kasa:
Obasanjo, Atiku da manyan Najeriya sun dura Abuja
A wani labarin, mun ruwaito cewa, manyan shugabannin Najeriya, ciki har da Atiku Abubakar da Olusegun Obasanjo, sun halarci kaddamar da littafin tarihin rayuwar Ibrahim Babangida.
Obasanjo zai jagoranci taron, yayin da Shugaba Bola Tinubu zai kasance babban bako na musamman tare da manyan jiga-jigan siyasa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng