Dalilin Da Ya Sanya Emeka Ihedioha Ya Janye Daga Takarar Gwamnan Jihar Imo, Wata Kungiya

Dalilin Da Ya Sanya Emeka Ihedioha Ya Janye Daga Takarar Gwamnan Jihar Imo, Wata Kungiya

  • Wata ƙungiya a jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta bayyana dalilin da ya sanya Emeka Ihedioha, ya janye daga takarar gwamnan jihar Imo
  • Ƙungiyar tace shugabancin jam'iyyar PDP na ƙasa bai yiwa Ihedioha adalci ba inda ya fifita abokin takarar sa
  • Ƙungiyar ta bayyana cewa kuskure ne babba sakataren jam'iyyar na ƙasa yayi takara a zaɓen alhali bai yi murabus daga muƙamin sa ba

Jihar Imo- Wata ƙungiya mai suna Peoples Democratic Party (PDP) Action, tayi bayanin dalilin da ya sanya Emeka Ihedioha, ya janye daga takarar zaɓen fidda gwanin jam'iyyar PDP na gwamnan jihar Imo. Rahoton The Cable

A ranar Talata ne dai, Emeka Ihedioha a wata wasiƙa da ya aikewa shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa, ya bayyana cewa ya janye daga takarar bayan jam'iyyar ta nemi da ta marawa ɗan takarar gwamna ɗaya baya. Rahoton Punch

Kara karanta wannan

"Na Sama Da Mu Sun Karbi Tuhumar", 'Yan Sanda Sun Bayyana Halin Da Ake Ciki Game Da Shari'ar Ado Doguwa

Emeka
Dalilin Da Ya Sanya Emeka Ihedioha Ya Janye Daga Takarar Gwamnan Jihar Imo, Wata Kungiya Hoto: The Cable
Asali: UGC

A wata sanarwa da aka fitar ranar Laraba, shugaban ƙungigar Rufus Omeire, yayi zargin cewa Ihedioha ya janye ne saboda babu gaskiya a cikin zaɓen fidda gwanin.

Ya bayyana cewa sakataren jam'iyyar PDP na ƙasa, Sanata Samuel Anyanwu, wanda yake takara a zaɓen fidda gwanin ya ƙi yin murabus daga muƙamin sa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Omeire ya bayyana cewa bai dace ba Anyanwu ya sanya ido akan zaɓen wanda yake takara a cikin sa ba.

“Da farko dai, Ihedioha, wanda ya kasance jajirtaccen mamban jam'iyyar PDP ne tun shekarar 1999, shugabannin jam'iyyar ba suyi masa adalci ba," A cewar sanarwar
"Sakataren jam'iyyar na ƙasa, Sanata Samuel Anyanwu, ya nuna aniyar sa ta yin takara a zaɓen fidda gwanin tun da yana da ƴancin hakan a matsayin sa na ɗan asalin jihar Imo."
"Sai dai a matsayin sa na sakatare mai ci a jam'iyyar abinda yakamata shine kada ya sanya ido akan zaben fidda gwanin wanda yake takara a ciki."

Kara karanta wannan

An Tafka Magudi: Dan Takarar Gwamnan PDP Yaki Yarda Da Kaddara, Zai Kalubalanci Sakamakon Zabe a Kotu

Ƙungiyar ta bayyana cewa kundin tsarin mulkin jam'iyyar yayi tanadin cewa duk mai riƙe da wani ofis a shugabancin jam'iyyar na ƙasa da yake yin takara yayi murabus daga muƙamin sa.

Rufus yayi iƙirarin cewa jam'iyyar PDP a ƙarƙashin shugabancin Iyorchia Ayu ta ƙi bin doka inda ta fifita Anyanwu.

APC Na Binciken Yan Majalisa Kan Zargin Yiwa Jam’iyya Zagon Kasa

A wani labarin na daban kuma, jam'iyyar APC a jihar Gombe ta kafa kwamiti domin bincikar wasu manyan jiga-jiganta a jihar.

Jam'iyyar tana yi musu zargin cin dundunniyar ta a lokacin zaɓe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel