Bayan Dakatar da Gwamna Fubara, NAFDAC Ta Ƙwace Buhunan Shinkafa a Rivers

Bayan Dakatar da Gwamna Fubara, NAFDAC Ta Ƙwace Buhunan Shinkafa a Rivers

  • Hukumar NAFDAC ta kama buhuna 120 na jabun shinkafa a Fatakwal, jihar Ribas, yayin samame da aka kai tare da hadin gwiwar Big Bull
  • An gano shinkafar jabu a shaguna da ke kasuwannin Woji, Mile 3 da Mile 1, tare da wasu kayayyaki kamar shinkafar Cap, Stallion da Tomato
  • NAFDAC ta cafke wata yar kasuwa, Ogechi Okafor, da kayayyakin hada jabun shinkafa, sannan aka kai buhunan da aka kwace ofishin hukumar
  • Kwamishinan NAFDAC ya kara da cewa jabun shinkafar da ake sayarwa ba ta da inganci, kuma ana sanya mata wasu sinadarai masu cutarwa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Rivers - Hukumar NAFDAC ta cafke buhuna 120 na shinkafa da ake zargin na jabu ne a shaguna daban-daban na birnin Fatakwal, jihar Ribas.

A cewar kakakin NAFDAC na Kudu maso Kudu, Cyril Monye, an gano shinkafar ne yayin wani samame da aka kai tare da hadin gwiwar kamfanin Big Bull.

Kara karanta wannan

Ramadan 2025: Ana tafka tsananin zafin rana a Kano, masu azumi sun koma shan ORS

Hukumar NAFDAC ta yi magana da ta kama jabun shinkafa a jihar Rivers
Hukumar NAFDAC ta cafke buhunan shinkafa a wasu shagunan jihar Rivers. Hoto: @NafdacAgency
Asali: Twitter

Hukumar NAFDAC ta cafke buhunan shinkafa a Rivers

Hukumar NAFDAC, mai kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa, ta sanar da hakan ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafinta na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta rahoto kwamishinan NAFDAC na jihar Ribas, Pharm. Emmanuel Onogwu, ya gargadi jama’a da ‘yan kasuwa da su kula da jabun shinkafa da ake sayar masu.

Pharm. Emmanuel ya ce sun yi samame a shagunan da ke kasuwannin Woji, Mile 3 da Mile 1 a Fatakwal, inda aka gano jabun shinkafar Big Bull.

A wani shago a yankin YKC, an gano buhunan Big Bull na jabu da sauran kayayyaki kamar shinkafar Cap, Stallion, Tomato, Mama Pride da sauransu.

Rivers: NAFDAC ta cafke buhuna 120 na shinkafa

Sanarwar ta ce jami'an hukumar NAFDAC sun kuma kama wata yar kasuwa mai suna Ogechi Okafor, wacce ake zargi da sayar da jabun shinkafar.

Kara karanta wannan

Nasarori 3 da Nyesom Wike ya samu a cikin kwanaki 3 a siyasar jam'iyyar PDP

Daga cikin kayan da aka samu a shagonta har da injinan dinka buhu, janareta, murhu, zaren dinki da buhunan shinkafar da aka buga jabunsu.

A cewar sanarwar:

"A jimlace, an kwace buhuna fiye da 120 na jabun shinkafa daga fiye da shaguna 10, inda aka kai su ofishin NAFDAC na shiyyar domin gudanar da bincike."

NAFDAC: Yadda ake gane shinkafar jabu

NAFDAC ta fadi illolin jabun shinkafa
Hukumar NAFDAC ta cafke buhunan jabun shinkafa a jihar Rivers. Hoto: @NafdacAgency
Asali: Twitter

Pharm. Emmanuel ya shawarci jama’a da su duba wasu alamomi masu nuna bambanci tsakanin asalin shinkafar Big Bull da ta jabu.

"Muhimman abubuwan da ke raba shinkafar Big Bull da na jabunta sun hada da wani zare mai sheki da ake dinke buhun da shi.
"Sauran alamomi na gane shinkafar Big Bull ta asali sun hada da karfi da kargon buhu da kuma tambarin kamfanin, wanda ake gagara kwaikwayarsa cikin sauki."

Kwamishinan ya kara da cewa shinkafar da ake wankewa ana zubawa a buhun Big Bull ba ta da inganci, kuma ana amfani da sinadarai masu cutarwa domin sa ta ta yi kyau.

Kara karanta wannan

Fubara: Atiku, El Rufai, Obi da mutanen Buhari sun tunkari Tinubu da murya daya

Duba sanarwar a nan kasa:

Tinubu ya dakatar da gwamnan Rivers

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta ɓaci a jihar Rivers, ya na mai dogara da barazanar tsaro.

A jawabin kai tsaye da ya gabatar, Tinubu ya dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa, Farfesa Ngozi Odu, na tsawon watanni shida.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng