COVID-19: NAFDAC ta tabbatar da ingancin shinkafar da muka rabawa jihohi - FG

COVID-19: NAFDAC ta tabbatar da ingancin shinkafar da muka rabawa jihohi - FG

Gwamnatin tarayya a ranar Alhamis ta karyata ikirarin da ake yi na cewa ta raba wa jihohin Kudu maso Yamma shinkafar da kwari suka lalata inda ta ce an tabbatar da ingancin kayan abincin.

The Punch ta ruwaito cewa Ministan walwala da jin kai, Sadiya Umar-Farouq, ta ce hukumar kula da ingancin abinci da magunguna na kasa, NAFDAC, ta amince da ingancin shinkafar da aka raba a matsayin tallafi.

Umar Faruq wacce ta yi wannan bayanin yayin jawabi a kan COVID-19 a Abuja ta kuma karyata ikirarin da ake yi na cewa maaikatar ta ta karkatar da kaduden N-Power don sayan kayan tallafin COVID-19 .

A ranar Jumaa ne gwamnatin jihar Oyo ta nuna alamar cewa akwai yiwuwar ta mayar da buhunnan shinkafa 1,800 da gwamnatin tarayya ta bawa jihar a matsayin tallafi a kan cewa kwari sun lalata shinkafar.

COVID-19: NAFDAC ta tabbatar da ingancin shinkafar da muka rabawa jihohi - FG

COVID-19: NAFDAC ta tabbatar da ingancin shinkafar da muka rabawa jihohi - FG
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Covid-19: Yara biyu sun mutu a dandazon jama'a yayin siyayyar azumin Ramadan

Kazalika, akwai jita jitar cewa wasu jihohin a Kudu maso Yamma suna shirin mayar da shinkafar da gwamnatin tarayya ta basu a matsayin tallafi na Coronavirus.

Da ta ke mayar da martani game da wannan a ranar Litinin, Umar-Farouq ta ce, "A kan batun shinkafa da muka rabar a jihohi.

"Hukumar kwastam ta bamu shinkafar sannan NAFDAC ta tabbatar da ingancin sa sannan muka fara raba wa jihohi.

"Iya sanin mu, an tabbatar da cewa mutane za su iya cin shinkafar ba tare da matsala ba. Mun samu matsala a jihar Oyo da aka sanar da mu safiyar yau."

Ta kara da cewa, "kwanaki biyu ko uku da suka gabata, mun ga labarai cewa dukkan shinkafar da muka kai yankin Kudu maso Yammacin kasar nan sun lalace.

"Kuma wai Legas ta zubar da nata a rafi sannan sauran jihohi sun mayar da nasu. Ina son in tabbatar muku wanna labaran bogi ne. Duk karya ne."

Ministan ta ce ta yi magana da Gwamnan Ekiti, Kayode Fayemi a ranar Litinin kuma ya tabbatar mata cewa shinkafar za a iya amfani da shi ba tare da matsala ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel