Fursunoni 12 Sun Yi wa Jami'ai Dabara, Sun Tsere daga Kurkuku Salin Alin a Kogi

Fursunoni 12 Sun Yi wa Jami'ai Dabara, Sun Tsere daga Kurkuku Salin Alin a Kogi

  • A safiyar Litinin aka tabbatar da tserewar wasu fursunoni 12 da ke girbe abin da suka shuga a gidan gyaran hali da tarbiyya na Kotonkarfe, jihar Kogi
  • Kwamishinan yada labaran jihar Kogi, Mista Kingsley Fanwo, ya bayyana mamakin yadda fursunonin suka tsere ba tare da lalata komai a gidan ba
  • Ya ƙara da cewa tuni gwamnan jihar, Usman Ododo, ya bayar da umarni kan cafko wadanda suka sulale, tare da daukar matakan kare afkuwar hakan
  • Zuwa yanzu, hukumomin tsaro sun samu nasarar kama daya daga cikin fursunonin da suka tsere, yayin da ake laluben inda sauran suka shiga

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar KogiA safiyar Litinin ne fursunoni 12 suka tsere daga gidan gyaran hali da tarbiyya na tarayya da ke Kotonkarfe a jihar Kogi.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya yi buda biki da marayu, ya ɗauki alkawarin ba su aikin yi

Mista Kingsley Fanwo, wanda shi ne Kwamishinan yada labaran jihar, ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici, kuma za a dauki mataki.

Ododo
Fursunoni sun tsere daga kurkukun Kogi Hoto: Alhaji Ahmed Usman Ododo
Asali: Facebook

Channels Television ta wallafa cewa Mista Fanwo ya tabbatar wa da ‘yan Najeriya, musamman mazauna Kogi cewa gwamnati tare da hukumomin tsaro za su dauki matakan hana afkuwar irin wannan a nan gaba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An cafke fursuna a jihar Kogi

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa hukumomin tsaro sun samu nasarar kama daya daga cikin fursunonin 12 da suka tsere daga inda aka ajiye su a matsayin hukunci a kan laifuka daban-daban.

Mista Fanwo ya ce:

"Maganar cewa fursunonin sun tsere ta hasumiyar gadi ba tare da sun lalata wani bangare na ginin ba na bukatar bincike mai zurfi."
"Dole ne a gudanar da cikakken bincike don gano hakikanin yadda tserewar ta faru, a kamo sauran da suka gudu, da kuma gano ko akwai masu yin kutse a cikin tsarin."

Kara karanta wannan

Nasarori 3 da Nyesom Wike ya samu a cikin kwanaki 3 a siyasar jam'iyyar PDP

Gwamnan Kogi umarni ya yi umarni kan fursunoni

Kwamishinan ya kara da cewa gwamna Usman Ododo ya umarci hukumomin tsaro da su tabbatar da cewa irin wannan matsalar ba za ta sake faruwa ba.

Ododo
Gwamnan Kogi ta ya ba da umarnin kamo fursunoni Hoto: Alhaji Ahmed Usman Ododo
Asali: UGC

Ya ce:

"Muna kira ga jama’a da su kai rahoton duk wani mutum da ba su amince da shi ba a yankunansu. Duk wanda aka kama yana boye fursuna da ya tsere zai fuskanci hukunci."
"Babu bukatar firgici. Muna tabbatar wa ‘yan ƙasa cewa tsaron rayuka da dukiyoyinsu shi mu ka ba wa fifiko. Kowa ya ci gaba da harkokinsa na yau da kullum ba tare da tsoro ba."

Fursunonin da suka sulale sun dawo hannu

A baya, kun ji yadda rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta sake kama fursunoni biyu da ake zargin sun tsere daga gidan gyaran hali na Kuje a Abuja, tare da mayar da su hannun hukuma.

Kara karanta wannan

Dokar ta baci a Ribas: Ana zargin Shugaba Tinubu da 'juyin mulki'

Fursunonin sun samu tsere wa bayan wasu ‘yan ta’adda sun yi amfani da abubuwan fashewa wajen fasa gidan gyaran halin na Kuje, wanda hakan ya jawo fursunoni da dama su ka tsere.

An bayyana cewa akalla fursunoni 800 ne suka tsere daga gidan gyaran hali na Kuje, wanda a lokacin yana dauke da fursunoni 994, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar jami’in tsaro.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng