Tankar Mai Ta Sake Fashewa a Neja, Hukumomi Sun Tashi Tsaye

Tankar Mai Ta Sake Fashewa a Neja, Hukumomi Sun Tashi Tsaye

  • A karshen makon jiya aka samu tashin gobara bayan wata tankar mai ɗauke da man fetur ta tashi a wani gidan mai da ke jihar Neja
  • Lamarin ya auku ne garin Kontagora lokacin da ke sauke fetur daga cikin tankar a yammacin ranar Lahadi, 23 ga watan Maris 2025
  • Majiyoyi sun bayyana cewa ba a samu asarar rayuka ba saboda mutanen da ke kusa da wurin sun tsere domin tsira da rayukansu
  • Kwamandan hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa (FRSC) ya bayyana namijin ƙoƙarin da jami'ansa suka yi wajen shawo kan lamarin

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Neja - Wata tankar mai ɗauke da man fetur ta kama da wuta a gidan mai na A.A Rano da ke Hannun Riga, kusa da babban asibitin Kontagora, hedkwatar ƙaramar hukumar Kontagora ta jihar Neja.

Gidan man da lamarin ya auku ya na kuma da nisan ƴan mitoci kaɗan daga ofishin rundunar ƴan sandan Najeriya da ke Kontagora.

Kara karanta wannan

Hankula sun tashi bayan bam ya fashe ana cikin azumi a Yobe

Tankar mai ta fashe a Neja
Tanka dauke da man fetur ta fashe a Neja Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Yadda tankar mai ta fashe a Neja

Jaridar Daily Trust ta ce majiyoyi sun ce lamarin ya faru ne yayin da ake sauke man fetur daga cikin tankar wajen ƙarfe 7:00 na yamma a ranar Lahadi, 23 ga watan Maris 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani ganau ya bayyana cewa gobarar ta fara ne yayin da ake sauke man, kuma sauran manyan tankunan ajiya na gidan man suna cike da mai, lamarin da ya haifar da fargabar yaɗuwar wutar.

Ya bayyana cewa ba a samu asarar rai ba, amma mutane ciki har da masu wucewa ta kusa da wurin, sun tsere domin tsira da rayukansu.

Hukumar FRSC ta shawo kan lamarin

Kwamandan hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa (FRSC) reshen jihar Neja, Kuma Tsukwam, ya tabbatar da aukuwar lamarin ga jaridar The Punch a ranar Litinin.

Ya bayyana cewa jami’an hukumar sun samu nasarar daƙile gobarar tare da hana asarar rayuka.

"Eh, mutanenmu sun samu nasarar hana wutar yaɗuwa. Lamarin ya faru ne a cikin tashar mai. Sun kewaye yankin gaba ɗaya, don haka ba a samu asarar rai ba."

Kara karanta wannan

Fubara: Gwamnonin PDP sun nufi kotun koli kan dokar ta baci a jihar Ribas

"Ba a samu asarar rai ba, amma wutar ta tashi sosai. Ina ganin rashin amfani da matakan kariya ne ya janyo hakan, amma mun yi nasarar kewaye wurin gaba ɗaya."
"Lamarin ya faru ne a cikin tashar mai, kuma an hana motoci da mutane shigowa cikin wurin. Eh, haka ne, tabbas lamarin ya faru."
"Babban damuwarmu shi ne ba a samu asarar rai ba. Dole ne su bi ƙa’idojin kiyaye lafiya, domin hakan wajibi ne."

- Kuma Tsukwam

Tankar mai ta fashe a Neja

A wani labarin kuma, kun ji cewa an samu fashewar wata tankar mai a garin Kusogbogi da ke a kan iyakar ƙananan hukumomin Lapai da Agaie a jihar Neja.

Fashewar tankar man ta ritsa da wasu mutane huɗu da ke cikin motar waɗanda ake fargabar sun riga mu gidan gaskiya.

Lamarin dai ya auku ne lokacin da tankar man take ƙoƙarin wucewa ta wata babbar hanya da ta bi ta cikin garin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel