Rikicin Sarauta: Aminu Ado Ya Yi Rangadi a Kano, Ya Duba Filin Hawan Sallah
- Rahotanni na nuna cewa Aminu Ado Bayero, ya dawo daga Cross River, inda ya halarci taron yaye dalibai da aka yi a Jami’ar Calabar
- Bayan saukarsa a filin jirgin sama, ya wuce fadar Mandawari domin duba aikin gyara da ake yi don shirye-shiryen bikin hawan sallah
- Rikicin sarautar Kano na daukar sabon salo yayin da gwamnatin Kano ta ba da dama ga Muhammadu Sanusi II ya gudanar da bikin sallah
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Rikicin sarautar Kano na cigaba da daukar hankula yayin da manyan sarakuna biyu ke cigaba da gudanar da harkokinsu a jihar.
Mai martaba Aminu Ado Bayero ya dawo daga tafiyar da ya yi zuwa Cross River, inda ya halarci taron taron yaye dalibai a Jami’ar Calabar.

Kara karanta wannan
Hawan Sallah: Sanusi II ya dau zafi, ya yi addu'o'i kan masu son tada tarzoma a Kano

Asali: Facebook
Legit ta tattaro bayanai kan dawowar Alhaji Aminu Ado Bayero ne a cikin wani sako da aka wallafa a shafinsa na X a ranar Lahadi da yamma.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayan dawowarsa, mai martaba Aminu Ado Bayero ya wuce fadar Mandawari don duba shirye-shiryen bikin sallah.
Aminu Ado ya dawo Kano daga Calabar
Bayan dawowarsa daga Jihar Cross River, Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya sauka a filin jirgin saman Kano, inda jama’a suka tarbe shi da farin ciki.
A yayin ziyararsa a Calabar, Aminu Ado Bayero ya halarci taron yaye dalibai na Jami’ar Calabar, ya samu damar ganawa da Ministan Abuja, Nyesom Wike.
Wasu sun yi mamakin ganawar Aminu Ado da Nyesom Wike a lokacin da APC a jihar Kano ta yi barazanar dokar ta-ba ci.
Duba shirye-shiryen hawan sallah a Kano
Bayan saukarsa daga jirgi, Sarkin Kano ya wuce fadar Mandawari domin duba aikin gyaran da ake yi a wurin don shirin bikin hawan sallah.
Daga nan, Aminu Ado Bayero ya zarce zuwa fadar Nassarawa, daya daga cikin mahimman wuraren sarauta a birnin Kano.
Aminu Ado Bayero yana zama a fadar Nasarawa ne tun bayan da gwamnatin Kano ta sauke shi a sarauta a shekarar 2024.

Asali: Twitter
Wani salo a rkicin sarautar Kano
A yayin da ake cigaba da fargaba kan rikicin sarautar Kano, Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, ya duba filin Sallar Idi domin shirin Sallah.
Hakan ya biyo bayan sanarwar da Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi cewa Sarkin Kano na 16, mai martaba Muhammadu Sanusi II shi ma zai gudanar da hawan sallah.
Wannan mataki ya sake kara daukar hankalin jama’a, domin yana nuna yadda rikicin sarautar Kano ke daukar sabon salo da ka iya tayar da wani ce-ce-ku-ce a jihar.
Pantami ya yi magana kan sarautar Kano
A wani rahoton, kun ji cewa Malamin addinin Musulunci a Najeriya, Sheikh Isa Ali Pantami ya yi magana kan rikicin sarautar Kano da ake fama da shi.
Isa Ali Pantami ya ce abin takaici ne yadda aka zuba ido ana ganin manyan kasa na bugawa da juna a kan sarautar Kano ba tare da daukar mataki ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng