Bayan Ganawar Aminu da Wike, Ana Fargabar Kotu na Iya Hana Sanusi II Hawan Sallah

Bayan Ganawar Aminu da Wike, Ana Fargabar Kotu na Iya Hana Sanusi II Hawan Sallah

  • Kwararren lauya kuma mai kare hakkin dan Adam, Chidi Odinkalu, ya bayyana damuwarsa kan yadda kotu za ta yi katsaandan a hawan sallah a Kano
  • Fitaccen lauyan ya ce an samu bayanan sirri a kan hukuncin da kotun daukaka kara ke shirin zartarwa, wanda zai goyi bayan Sarki Aminu Ado Bayero
  • Ya bayyana haka ne bayan gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya umarci sarakunan jihar, karkashin Sarki Muhammadu Sanusi II su shirya hawa
  • Fargabar Odinkalu na zuwa kwanaki kadan bayan an ga Alhaji Aminu Ado Bayero ya na tattauna wa da Ministan Abuja, Nyesom Wike a garin Kalaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar KanoKwararren lauya kuma mai kare hakkin dan Adam, Chidi Odinkalu, ya bayyana damuwarsa kan hukuncin da Kotun Daukaka Kara ke shirin yanke wa kan masarautar Kano.

Kara karanta wannan

Ruguntsumi a Kano yayin da Aminu Ado ya kalubalanci Sanusi II kan hawan sallah

Farfesa Odinkalu ya ce bayanan da suka iso gare shi dangane da wannan hukunci na iya yin tasiri mai girma a fannin siyasa da shari’a a jihar Kano.

Hawan sallah
Ana fargaba kan yunkurin hana Sarki Muhammadu Sanusi hawan sallah Hoto: Abba Kabir Yusuf/Masarautar Kano
Asali: Facebook

A shafinsa na X, Odinkalu ya bayyana cewa wasu majiyoyi masu tushe daga bangaren shari’a sun sanar da shi an shirya bayar da umarnin dakatar da hawan Sarki Muhammadu Sanusi II a ranar Talata mai zuwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana fargabar hukuncin kotu kan masarautar Kano

Fitaccen lauyan ya ce wannan hukunci zai sahale wa Sarki Aminu Ado Bayero gudanar da hawan Sallah karama, bayan an hana Sarki Sanusi II.

Chidi Odinkalu ya nuna matukar damuwa kan abin da wannan mataki zai haifar, ya na gargadi cewa ya na iya jefa jihar cikin rudani.

Masarauta
Sarki Aminu a lokacin da ya ke gana wa da Wike Hoto: @HrhBayero
Asali: Twitter

A cewarsa, za a jingina hukuncin ne da umarnin kotu na a kwanakin baya da ya dakatar da hukuncin da ta yanke kan nadn Sarki Muhammadu Sanusi.

Kara karanta wannan

'Wani gwamnan Najeriya zai mutu kafin 2027': Malami ya hango makomar Atiku, Tinubu

Su wanene masu hukunci kan masarautar Kano?

Odinkalu ya ce daya daga cikin alkalan da za su yanke hukuncin mai dakin guda daga cikin masu ruwa da tsaki a shari'ar dambarwar masarautar Kano ce.

Ya yi zargin cewa wannan sabon yunkuri wani nau’in zai iya haddasa tashin hankali a Kano, ganin yadda gwamnati ta umarci sarakunan jihar guda hudu su shirya hawan sallah.

Fitaccen lauyan ya bukaci jama’a da su kasance cikin shiri da lura, yana mai cewa karin bayani zai biyo baya nan gaba kadan.

Kano: Sarki Aminu ya kalubalanci hawan sallah

A baya, mun ruwaito cewa yayin da rikicin masarautar Kano ke ci gaba, al’ummar jihar sun shiga damuwa bayan da sarakuna biyu ke shirin gudanar da hawan Sallah karama.

Bayan da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ayyana cewa Sarakuna su yi hawan Sallah, sai Aminu Ado Bayero da aka tsige ya fitar da sanarwa cewa zai gudanar da nasa hawan a Kano.

A baya-bayan nan ba a yi hawan Sallah ba saboda tsoron barkewar rikici tsakanin mabiyan Sanusi II da Aminu Ado Bayero, wanda ya sa shirin hawa a yanzu ya jefa jama’a a cikin fargaba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng